Sashe 16
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Briefcase din sa sadiq ya d'auka fatuha na d'auke da jidda suka fito harabar gidan, haka fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da amsar briefcase din sadiq ya kai masa mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha ta aje jidda cikin mota , zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa, da sauri ya ture ta tare da taka mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da hannun shi da karfi yana kallon ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla taf saboda ita kad'ai tasan azabar da take ji, ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magana shiyasa baiji abinda take fadi ba, kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan, fatuha ko Allah ya isa ta shiga jeramasa tana kuka tare da shigewa gida a guje.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_yn_=H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*👏🏼Godiya ta musanman ga masoya na ❤ina jin dadi addu'ar ku ta fatan alheri😍 nima ina son ku ana mugun tare*🤝🏽
*Wannan shafin nakune masoya na asha karatu lafiya*❤
33_34
Parlour ta qaraso tare da share yar qwallar da ya taru a idonta, Mom na zaune saman three star tana kallo juyowa tayi cikin murmushi tare da kallan fatuha, ita ma fatuha murmushi tayi tare da fara kwashe kayan abinci da ke dining area Mom ta ce, "ah fatuha da kin bari rabi'a ta zo ta kwashe" washe baki tayi tare da cewa, "barshi kawai hajiya" Mom murmusawa tayi tare da cewa "Ni ko fatuha da kin daina ce min hajiya nan da yafi! Ki rinqa kira na da sunan da sadiq ke kira na" murmushi fatuha tayi tare da cewa, "toh.! sannan ta kwashe kayan ta kai kitchen Mom kuma ta cigaba da kallon ta tana ayana wasu abubuwa a ranta, tana fituwa direct part d'in sadiq ta wuce ta gyara part d'in sosai, tana gamawa ta shiga toilet shima toilet d'in sai daya sha wanki dan fatuha gyara tayi bana wasa ba, tana gamawa ta washe baki tare da zama saman sofa tana qarewa d'akin kallo hotan sadiq ta hango manne jikin bango tangameme shi da kausar sunyi murmushi.
A hankali ta qaraso wajan hotan tare da washe baki tana kallon hotan ta ce, "ohni ashe sangami na murmushi, ah ji yadda ya washe hakora dan Allah ai da haka yake kullun daya fi kyan gani" murmushi tayi tare da d'aura hannuta saman pic din ta ce, "uhm gaskaya kana da kyau Qur'an" chan kuma sai ta bata fuska tare da cije lips dinta dariya tayi sannan ta ce, "Kwarankwatsi zaka zo ka same ni wallahi ba kasan *wacece fatuha ba yar gidan Baffa jauro*" sannan ta bala wa pic din harara ta fita daga part din.
Tana sakowa downstairs ta shige bedroom dita wanka ta kumayi, tana fitowa ta shafe jikin ta da lotion tana shafa lotion din tana washe baki tana surutu da cewa, "Qur'an wanga mai sanyi garai ga kamshi, wallahi birni tayi" sai da ta gama shafe jikin da mai tas sannan ta sa wasu uniform din.
**
Cikin school yayi parking tare da fituwa ya budewa jidda murfin mota smile ya mata me sanyi, sannan ya ciro mata lunch box dita ya miqa mata, 6ata fuska jidda tayi tare da cewa "Daddy am going to miss u daddy" saman kanta ya shafa tare da cewa "Sorry angel soon za'a tashi aiko? sai inna dawo gida sai muje shan ice cream ko my angel" washe baki tayi tare da yi mashi peck sannan ta shige class yana kallonta har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige mota yatafi.
Bayan ta gama shirin ta tafito parlour ba kowa sai kamshi da ke tashi na girki, kitchen din ta nufa tare da sallama baba junmai ke girki sai rabi'a na gyara salat murmushi tayi tare da gaishe su washe da baki baba jummai ta amsa tare da cewa "Yar albarka kin zo taya ni aiki ne?" daga kai tayi alamar Eh, can kuma fatuha ta bata fuska tare da cewa, "baba wai ina kike kwana jiya kika barni ni kad'ai," washe baki baba jummai tayi tare da cewa, "aini fatuha banan nake kwana ba a gida na nake kwana sai da safe na zo" turo baki fatuha tayi ta ce, "gaskiya baba yau binki zanyi,"
"ah ba za'ayi haka ba ki zauna nan nima ai gidan bacci ke kai ni" baba jummai ta shiga lalla6a fatuha.
Taya su aiki tashiga yi sosai can baba jummai ta miqawa fatuha kwano ta d'ebo man da za'a soya kaji a store, wani irin murmushi tayi tare da shiga store d'in nan ta zuba a kwano tare da qule wani a leda tasa a aljihun skrit d'in ta ta fito, sannan tayi ma baba jummai sallama ta koma parlour ta cigaba da kallo tanayi tana washe baki, Mom ce ke saukowa daga stairs sanye da mayafi da car key a hannu ta kallon gefan da fatuha take tayi tare da cewa "Oh na manta, nayi da ke jiya zan kai ki gyaran kai wallahi na manta gashi yanzu fita zanyi" murmushi fatuha tayi ta ce, "ba komai gobe maje,"
"toh shikenan idan na manta ki tuna min please" toh ta ce mata tare da rakota har bakin kofa sannan ta koma parlour ta cigaba da kallo.
Tana kallo har bacci ya kwashe ta a parlour, cikin bacci taji ana sallama tashi tayi tare da ware idanuwan ta ta sauke su kan Anuty bilki, ware ido ta kuma yi tana qarewa Anuty bilki kallo dan tabbas tayi mata kama da sadiq sai dai sadiq ya fita kyau sosai qaqaro murmushi tayi bakin ta na rawa ta gaida Anuty bilki, zama tayi tare da amsawa tayi ma fatuha murmushi fatuha ta ce, "uhm hajiyar ba ta nan ta fita? murmushi Anuty bilki tayi ta ce, "ai na sani munyi waya yanzu zata dawo ba dad'ewa zatayi ba" fatuha kitchen ta shige ta fada ma baba jummai anyi baquwa lemo ta zuba mata a tray da kayan motsa baki tare da ce mata gata nan zuwa taga baquwar, Anuty bilki ko kayan jikin ta ta rage tare da haurawa upstairs dan ta watsa ruwan , fatuha na zuwa parlour taga ba baquwa sai Afra da ke bacci saman kujera baba jummai ta qwalawa kira ta fitu a rud'e ita ma Anuty bilki da shigar ta bedroom kenan ta sauko, turus baba jummai tayi a parlour tana cewa, "lafiya fatuha me ya faru" bakin fatu na rawa ta ce, "baba wallahi baquwar ce ban gani ba gashi ta bar yar ta a nan" Anuty bilki ce ta qaraso, da murmushi a fuskarta baba jummai ta ce, "ah wai Bilkisu ki ka gani kike nufin baquwa ai yar gidan ce amma tayi aure ganin gida tazo yi" murmushi fatuha tayi ta ce, "Aiyo aini ban sani ba shiyasa" itama Anuty bilki dariya tayi sannan ta haura sama tare da ba fatuha afra ta kula da ita kafin ta fito.
Misalin karfe 12:00pm jidda ta dawo school ita da Jamal, kasancewar school d'aya suke da yan'yan Anuty bilki cikin murna fatuha ta tare su , kasancewar fatuha me son yara ce, ta ja jidda da Jamal bathroom ta masu wanka suka fita tas, sannan ta sa masu kaya ta zo da su dining area suka ci abinci sannan ta dawo parlour da su suna dan ta6a hira sama-sama duk cewa kusan rabin hira duk shirme yafi yawa, can sai ga Hanan ita ma ta dawo daga school washe da baki ta qaraso ta fad'a jikin Anuty bilki take ce, "wash Mom am tied"
"sorry sweet je kiyi wanka ki canza kaya" fatuha ko washe baki tayi tana qarewa su Hanan kallo, tsakanin Hanan da fatuha kunsan sa'anin ne shiyasa tunda ta shigo fatuha ke kallon ta hakan sai yasa ta tuna da fatsima kwalla taji ta zo mata gaskiya ta san tayi kewar su inna da fatsima d'aki ta shige tayi kwanciyarta Hanan ce ta shigo ta shige toilet tayi wanka sannan ta fito d'aure da towel suna hada ido da fatuha tayi murmushi take ce, "sannu ki"
"yauwa" fatuha tace mata, nan Hanan ta fara janta da hira sama-sama, Hanan dama kawa take so gashi ta samu aiko nan hira ta barke tsakanin su idan fatuha ta fadi wani abu Hanan tayi dariya sosai har cikin ta ya kule.
Sai yamma likis su Hanan suka tafi, har bakin mota fatuha ta rako su ita da jidda, kamar kar su tafi saboda fatuha taji dadi hirarsu da Hanan.
Bayan sun tafi suka koma bedroom din jidda, taci gaba da zubama fatuha surutu can kamar an mintsili fatu ta tashi ta koma parlour kad'an-kad'an ta leqa waje.