Sashe 56
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haka fatuha ta shiga hada ma sadiq kayansa yana kallkn ta saida ta gama hada kayan tsaf tabi daki'n da kallo, kuka ya kubuce mata saboda tunowa da rayuwa da sukayi a baya shikenan yanzu rayuwar ta zama tarihi kuka take sosai, har da durkushe shikenan son da takewa sadiq ya sha ruwa, dagota sadiq yayi ya jawota jikinsa yana lallashi a hankali ta fara magana, "Mai kyau me yasa mutum baya samun abinda ya ke so a lokaci da yake so? ta fada tana qara rushewa da kuka a hankali sadiq ya lallu6o lips din ta ya fara mata hot kiss wanda shi kanshi bai san yana hakan ba, har suka zube kasan carpet bai kyale ta ba har sai da ta tsaigaita kukan, tana sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya sake ta yana maida numfashi, hada face nasu yayi guri guda yana magana can qasan makoshi mai kama da rad'a ya ce "Fatuha please ki dai kuka, dama shi rayuwa bai zama dole mu samu duk abin da muke so ba, muyi hakuri jarabawa ce daga Allah, insha Allah zai bamu sakamako mai kyau, dan haka muyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu, kuma ki daina kukan haka saboda yana tadamin da hankali a duk sanda naji.! d'aga kai tayi tare da kauda kanta dan gabaki daya kunya ta lullu6e ta, tashi tayi ta fita da sauri daga bedroom din, ko da ta fita jingina tayi da kofar tana maida numfashi a hankali ta daura hannuta saman lips din ta, ji tayi kamar an yaye mata bakin cikin dake damun ta sannan ta fito da gudu d'aga part din haka shima bangaran sadiq haka yaji.
Bayan kowa ya gama hada kayan shi su ola suka wuce da su boot gabaki d'aya, jikinta fatuha susuku yayi, haka sukayi mota 5 fatuha ta dade tana kallon gidan sannan suka bar harabar gidan suka harbawa kan titi,
***
Bayan sun Isa family house dangi har sun fara cika, take jikin fatuha yayi sanyi dan tasan tabbas ta rabu da sadiq har abada, haka shima bangaran sadiq hakan yake ji a ransa.
Bayan sun dan huta kowa ya aje kayan shi inda ake ajewa, aka kira mai lale ta fara yima amaran lale kafin ka ce me qawayan amaran sun fara halara, Zara da Nana har sun zo sai rawar kai suke zubawa, sallamar da akayi ne yasa fatuha juyowa cikin fara'a, waza ta gani inba fatsima ba, da gudu ta ruga ta rungumeta cike da murna haka itama tuni dakin ya dau shewa duk da fatuha ba jin dad'i take ba, amma ganin fatsima ba qaramin dadi ya mata ba, hakan yasa ta fara walwala.
Bangaran Basma ma haka qawayan ta duk sun hadu yan gayu masu ji da kan su, sai shewa suke suna taya Basma murnar samun handsome kamar captain sadiq, sai pictures suke kamar ba gobe kowa ce ka duba face nata kasan cikin farin ciki take.
Angwayan ma friends nasu da suke qasashan waje har sun fara sauka, haka part din nasu ya cika taf da bakin gida dana ketare, duk wannan abun da ake sadiq na gefe ya zuba masu na mujiya kamar ba abinda ke damonsa, sun san halin miskilancin sa shiyasa ba kowa ya damu da hakan ba sai Dr yakub dake ta faman lura da shi dan yasan sarai ciwo ne ke cin sa kowani lokaci zai iya faduwa...
fan's kuyi hakuri da wannan page din ba yawa, saboda ina school shiyasa, abubuwan sunyin yawa ga shirye-shiryan fara exam amma insha Allah gobe zan maku page mai yawa idan na samu dama
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=yn=H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
89_90
Shirye-shirye suke sosai kasancewar yau ake kamu, da misalin karfe 4:00pm kowace ka gani shiryawa take cikin ashobe, Fatuha da ke zaune cikin toilet tana sana'ar kuka knocking din kofar da akayi ne ya sata miqewa tana share hawayanta, Hanan dake bakin kofar ta ce, "Fatuha ki fito me make up ta zo har an gama ma Basma ke kadai ake jira" to tace tare da yin sauri ta watsa ruwa ta fito.
Ko da ta fito shaharariyar me make up fandi ta zo fatuha kawai take zaman jira, tana daure da towel ta fito ta zauna tana shafe jikinta da mai, Aunty bilki ce ta shigo da kayan da zasu sa washe da baki ta aje kayan ta ce, "a'a fatuha dama ba'a gama make up din ba" daga kai fatuha tayi Aunty bilki ta cigaba da cewa, "ya kamata kuyi sauri ku shirya kar ku 6ata lokaci saboda da kun dawo zaku dinner" to tace sannan Aunty bilki tasa kai fa fice, a hankali fandi ta fara tsantsara mata make up kafin ka ce me fatuha ta fito wasu peak materials tasa gown mai stone's masha Allah tasha kyau har ta gaji, kanta na daure da head silver, ita kanta me make up ta yaba da irin kyan da fatuha tayi, su fatsima ne suka shigo sanye da ashoben su ash atamfa mai ratsin peak suma sun sha head kun san a tare suka fito da Basma kusan kaya colours daya suka sa har yan mata amaryar anko daya su kayi, motoci ne masu numfashi da tsada suka faka amaran suka shige ba a zame ko ina ba sai meenah event hadadan hall na party iyakar haduwa hall din ya hadu, kuma ya qayatar kasancewar kamun na mata zala ne shiyasa ba ango ko daya sai yan'mata da iyaye, yan asharale ne suka fara buga ganga tuni hall ya dau sauti amaran zama su kayi ma zaunin su aka fara gudanar da shagulgula, su fatsina da Nana da Zara fili suka shiga suna ta kwaso shoki haka suma qawayan Basma biki yayi biki sai dai muce Alhamdulillah .
Fatuha ko duk wannan bidirin da ake zuciyar ta naga muradin ranta, ji take kamar ta rushe da kuka kallon kowa take da ke farin ciki da walwala angel ta hango itama ba laifi ta saki jikin ta tana warwasawa.
Anci ansha inda aka raba turaru kan wuta da atamfofi masu tsada sosai, aka raba kaya kamar ba'a so, sai kunsan yamma liqis taro ya watse suka dawo gida.
Ko da suka dawo wanka amaran suka qara tare da dauro alwala suka gabarta da sallah magrib da isha, sannan amaran aka fara shirya su cikin wani wanka ni kai na har mamaki nake irin shirin da akayi ma bikin, lace suka sa blue mai ratsin dark blue mai shegen tsada ga make up da aka qara zuba masu sai kamshi suke, yan matan amaraya ko pink lace suka sa mai ratsin white kowa ce tasha make up, fatuha ko saboda tsabar kyau kasa gane ta kake, dan ba qaramin kyau tayi ba kuma ga annuri da ya sauko mata na amarci, Basma ma ba'a barta a baya ba tayi kyau b sosai.
Shiryawa angwayan suke cikin getzner shada blue tasha aiki da dark blue zare malin-malin, duk wannan shirin da sadiq keyi jinsa yayi suku-suku dan kwata-kwata baya tare da walwalarsa links yasa ma hannun rigarsa sannan ya daura agogo a tsintsiyar hannusa hublot ya zura takalminsa black mesarath tuni ya fito yana sheqi da wani irin kyau, sajan fuskarsa ya kwanta luf-luf ya daura hula wadda ta dace da kayan gashin kansa ya leqo ta gefe-gefan hular feshe jikinsa yayi da turare masu kamshi da sanyi dadi kusan shigar su iri d'aya da majeed shima ba'a barshi baya ba dan yasha kyau har ya gaji, sai murmushi yake saki fararan haqoransa na bayana, aboka nan angwayan ma ba'a bar su a baya ba dan suma sunsha kyau ko wana su sai sheqi yake, Khaleed sai rawar kai yake zuba wa haka shima Dr yakub ba'a bar shi a baya gayu su kayi na sosai abun ka da bikin manya.
Cikin natsuwa suka fito suka shige motocin su Benz black, haka motocin masu zafi suka harba kan titi dan dauko amaran kasancewar a hotel suka shirya, ko da suka iso amaran sun shirya tsaf motoci aka fara shiga kowace amarya ta shige motar angonta,
Da murmushi majeed ya dubi fatuha da wani irin kallo mai cike da so da kauna, ba qaramin kyau ta masa ba ga wani fitinan kamshinta daya mamaye hancinsa mai kashe jiki, a hankali daura hannusa saman na fatu yana kallon lalan dake hannuta ja da baki yayi wani irin kyau ya ce, "My love lalan nan yayi kyau, bama shi kadai ba harda ke din ma" smile tayi wanda iya karshi la66anta ta janye hannuta daga cikin na majeed ta qara manewa karshan kofar tana tuna abin sonta.
Da kallo Sadiq yabi Basma ba laifi ta masa kyau, yau ce rana ta farko daya fara ganin kyanta ayanawa yayi a ransa, tunda ya ga Basma haka to ya fatuha zata kasance? wani irin kishi ne ya lullu6esa da qunar zuciya juyowar da yayi ne su kayi ido hudu da Basma smile ya sakar mata da kauda kai.