← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 67

Sashe 28

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta wanke jidda tas suka fito washe da baki jidda ta gaisheshi, amsa mata yayi tare da yi mata peck jidda ta ce, "Aunty me ya sami fuskar ki" jidda ta fada a tsorace kallon sadiq fatuha tayi shima ita yake kallo sannan ya kauda kai murmushi fatuha ta qaqaro ta ce "Bigewa fa nayi jiya, aini fushi nake dake Jidda kika tafi kika barni ni kad'ai a gida to shine fa na bige gashi ba kyanan" raurau jidda tayi da ido ta ce "Sorry Aunty ba laifina bane laifin daddy ne" ta ida zancan tana nuna daddy da hannu daddy ta ce cikin shagwaba ya ce, "yes..! a taqaice yana kallon newspaper, "daddy please kar a qara barin Aunty a gida ita kad'ai, daddy kalli face din Aunty fa?" tana fadi tana ware ido juyowa sadiq yayi ya kalli jidda tare da lumshe ido angel kin fiye surutu please ki tsaya Aunty ta shirya ki kinga mun kusa maqara, sai da fatuha ta gama shafe jidda da mai sannan suka fita kai tsaye bedroom din ta ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta sannan ta ruqo hannu ta suka fito parlour dinner area suka zauna ta shiga bama jidda abinci tana feeding din ta sadiq ya qaraso dining area riqe da briefcase din shi kujera ya ja ya zauna, plate fatuha ta janyo ta fara saving din sadiq yau anci sa'a bai hana ta ba sai da ta gama zuba masa ta tura masa gabansa sannan ta hada masa tea a cup ya amsa ya fara sha zai kai chips din baki ya kalli fatuha da ke feeding din jidda, ya ce "Ke Bakiyin break din?" kallon shi fatuha tayi ta hadiye wani yawo dan bata san me yake nufi da hakan ba murmushi sadiq yayi ya ce, "yar kauye kawai kalaci nake nufi.! washe baki fatuha tayi ta ce "Aiyo zanci to"
"fara cin yanzu" murmushi tayi tana ci tana feeding din jidda a zuciyar ta ko mamakin canji sadiq take, shiko sadiq amanar Mom yake riqewa ba wai wani abun ba, fatu ko tana cin abincin tana satar kallon sadiq.

Bayan sun gama break har filin gida fatuha ta rako su da lunch box din jidda peck jidda ta mata tare da yi mata bye bye, fatuha na tsaye har suka fita daga harabar gida ta juyo ta dawo cikin gida kayan breakfast ta kwashe ta kai kitchen, a kitchen ta hadu da rabi'a na girki murmushi tayi tare da gaisheta amsa mata tayi cikin fara'a sannan ta aje kwanikan cikin zing ta wanke su tas rabi'a sai hannata take amma taki kusan tare sukayi komai na kitchen din sannan suka jera a dining area ,washe baki rabi'a tayi ta ce, "kai amma fa fatuha na gode dan ba dan ke ba da yanzu ina ta aiki wallahi" murmushi fatuha tayi tare da cewa, "ba komai wallahi"
"bari na zo na lalla6a na wuce gida" kala tausayi fatuha tayi ta ce, "Wai har zaki tafi ne?"
"eh wallahi,"
"yanzu ni ka dai za'a bari a gida nan kamar maya? ta ida zancan tana raurau da ido, Rabi'a ta ce, "yi hakuri kin ji fatuha akwai inda zani da ba inda zani dana taya ki hira amma akwai inda zani" murmushi fatuha tayi ta ce "Ba komai" bakin kofa ta raqota sannan ta koma parlour ta zauna tare da kunna kallo kitchen ta shiga ta gyara fruit sannan ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci ya kwashe ta.

Bangaran sadiq yana sauke jidda ya wuce office, ko da ya je office yayi aiki sosai karfe 2:00pm nayi ya fito yaje school din su Jidda ya dauko ta suka dawo office tare sai zuba masa surutu take kowa na office din ji yake da jidda, daka ganta hannun wannan sai ka ganta hannun wancan sai la'asar sadiq ya amshe ta suka wuce gida.

Fatuha ko kiran sallar la'asar ne ya tashe ta, wanka tayi tare da dauro alwala tana gama sallah parlour ta dawo tana lunch cuscus ne da miyar kwai take ci tana jin dadin abincin har wani lumshe ido take, sallamar su sadiq ce ta qatse mata cin abinci washe da baki ta kalli jidda rugowa jidda tayi ta fada jikin fatuha tana dariya cike da tsantsar Darin ciki itama fatuha dariya tayi tare da gaishe da sadiq ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana sannan ya haura upstairs, fatuha ko saida ta cikawa jidda cikin ta da abinci sannan ta kai ta bedroom ta rage mata kaya sannan ta kaita toilet ta mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito suna daririku, lotion ta shafa mata sannan ta sa mata gwon brown mai kyau tare da jan hannun ta suka dawo parlour, hango sadiq sukayi yana zaune a dining area yana lunch guri fatuha ta samu ta zauna jidda ko wajan daddy ta nufa tare da haye masa cinya tana masa surutu ta ce, "daddy.!
"yes angel.!
"daddy please muje shan ice cream please" ta fadi tana lagwabe kai ja mata hanci sadiq yayi ya ce "Wannan bakin naki kullun san zaqi yake" dariya tayi mai nuni tana cikin farinciki, ture plate din gaban shi yayi tare da aje jidda qasa qafa ta shiga bubuga masa ita aladule sai sun je shan ice cream yau yace mata "Ok Angel is ok daina kukan kije Aunty ta shirya ki ko" sannan ya haura sama yana last stairs jidda ta ce, "amma har da Aunty zamu tafi dan kar dodo ya ji mata ciwo" toh yace tare da bude kofar part din shi.

Shirya jidda tayi tsaf amma ita ta rasa kayan da zatasa, duk gwon din data janyo sai ta maida jidda rugawa ta yi parlour zaune ta sami sadiq cikin shirin shi na qananan kaya yasa red riga mai ratsin black mai dogwon hannu shirt sai wando black da takalmi yasha kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf sai sheki yake sumar kansa tasha gyara jidda ta fada jikinsa ta ce, "daddy..! a dan shagwabe sadiq ya juyo alamar gajiya ya ce, "menene angel? lagwabe kai tayi ta ce, "daddy zo ka za6a ma Aunty dress ta rasa wanda zatasa" dan guntun tsaki sadiq ya ja ya ce "Angel me yasa kika fiye rigima?" um bata fuska tayi tana shirin yin kuka tana qoqarin sauka daga jikin sadiq hakan yasa sadiq tashi ba dan ya so ba bedroom din fatuha ya shiga tsaye ya ganta gaban drawer ta riqe qugu ga kaya baje a saman bed bakin kofa ya tsaya yana qarewa bayan ta kallo juyowa fatuha ta yi jin kamar ana binta da kallo ta bayanta su kayi 4 eye's da sadiq dake binda da sexy eyes ball d'insa kauda kai tayi ta cigaba da abinda take a hankali ya qaraso wata gwon ya gani kawai ya jawo ba wai da ya lura da ita ba miqa mata yayi ya ce, "kisa wannan mu tafi" sannan yasa kai ya fice cikin 5 minute fatuha ta shirya cikin red gwon mai stones sai black veil tasa tare da murza hoda ta shafa lipstick wani irin kyau fatuha tayi komai na shape din ta ya bayana duk da ba wasu shekaru gare ta ba amma ita kanta tana mamakin girman jikinta kallo daya zaka mata kasan ta hadu tayi tamkar ba yar aiki ba takalmi tasa tare da feshe jikin ta da turare masu kamshi sannan ta yafa veil din ta, a hankali ta bude handle din kofar bedroom din parlour ta fito sadiq dake zaune saman two sitar ya lumshe ido, jidda na zaune gefe shi kamshin turaren fatuha ne yasa sa ware sexy eye's ball din shi ya sauke su kanta wani irin kyau ta masa na ban mamaki sosai ya zage yana binda da idanusa ta6e baki yayi yace ashe wannan yarinyar nada kyau duk yana wannan zancan ne a zuci miqewa yayi tare da daukar car key suka fita, gaba jidda ta shiga fatuha na baya jidda sai zuba mata surutu take.

Sun sha yawo kamar me ice cream ko har sai da suka ture, fatuha ko baki har kunne dan dadi duk inda suka wuce sai an kalle su saboda sun sha kyau sun gaji munjibir park sadiq ya kai su zama yayi a resting chair yana kallon su, su fatuha wasa ko ba wanda basuyi ba, basu suka bar munjibir park ba sai yamma likis a gajiye suka dawo gida, fatuha ko dadi fal a zuciyar ta jidda ko saboda tsabar gajiya tayi bacci cikin mota.
hancin motarsa yasa cikin gida bayan mai gadi ya wangale get parking space yayi parking bala mai gadi sai washe hakkra yake daga masa hannu sadiq yayi tare da dai-daita parking din motar sannan ya kashe motar, kamar jira fatu take ta fito murfin motar gaba ta bude tana qoqarin d'aukar jidda shima sadiq ya turo kai da hannu yana qoqarin daukar jidda ji kake gwab sun qume kai "wash..! sadiq yace fatuha ma haka yadda sadiq yayi da fuska shi yaba fatuha dariya sai kace baby boy, dariya ta saki har ana ganin fararan haqoranta sosai take dariyar mai cike da birgewa, dariya da fatuha take sai ta qara mata kyau hakan yasa sadiq mutuwar tsaye yana kallon fatu yana qara ganin kyanta 6oyaye na bayana na ban mamaki, kallo da yake mata ne yasa ta tsagaita dariyar tare da daga masa gira hakan maido da sadiq saiti harara ya aika mata ya wani had'e rai ya ce, idan kin gama dariyar ki dauko ta mu shiga gida" dariyar da yake shirin zo mata ta guntse tare da daukar jidda.

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Salma mas'ud nadabo

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=,52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSFULANIWRITERSFORUM.com

                53_54
Chapter 28 · 0% Book details