← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 67

Sashe 40

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu suka bar parlour ba sai da akayi kiran sallah magrib yasa suka wuce masallaci, su kuma matan suka wuce part din Mom basu suka dawo ba sai bayan isha'i jawad ya wuce part din su sadiq ya shige gida, parlour ba kowa bedroom din fatuha ya wuce a hankali ya bud'e kofar kwance ya hango ta saman bed ta dunqule waje daya rife kofar yayi tare da qarasa shigowa, gaban bed din yayi kneeldown a hankali ya kai hannu yana shafa gashin kanta cike da begenta da tausayinta, a hankali ta ware idanuwan ta kan sadiq, kuka ta saka masa mai cike da shagwaba da yarinta, "shhh..! kukan ya Isa haka mana uhm" har lokacin sadiq na sakin tattausan murmushinsa yana shafa gashin kanta kamo hannusa fatu tayi tana qoqarin kai masa marata inda ke mata ciwo sauri kauda hannusa sadiq yayi tare da wayancewa dan ya lura har yanzu fatuha yarinyace shiyasa take haka a hankali ta furta, "mai kyau"
"na'am Sister" cikin wata kasalaliyar murya fatu ta ce, "Zai daina ciwo"
"eh mana gobe da kin tashi zaki ji kin warke kin ji sis" to ta ce masa tare da riqe hannusa tana wasa da su kamar an tsunkunesa ya tashi ya fita fatuha ta bishi da kallo.

Kitchen ya shige ya d'auko mata fresh milk mai sanyi ya dawo bedroom, har yanzu tana yadda ya bar ta tana bin sadiq da ido bata fresh milk din yayi ta kafa kai ta shaye sannan ya mata peck a lunatic tare da yi mata good night ya fice.

Kun san kwanan fatuha 4 tana period tayi wanka Mom ta gwada mata duk yadda ake.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi inda yanzu duk gidan ba wanda bai san shaquwar fatuha da sadiq ba, Mom ko in ban da dadi ba abinda take ji dan gani take fatuha alheri ce a rayuwar su, sannan sadiq ya sheda mata zai kai fatuha school kuma tayi na'am da zancan.

Harhad'a kayan ta dana jidda take a trolley saboda yau zasu je wudil, bakin fatu har kunne bayan ta gama had'a kayan tsaf a trolley ta wuce part din sadiq zaune a parlour ta samesa harara ya aika mata tare da kauda kai, dan 6ata fuska fatuha tayi tare da matsawa kusa da sadiq har yana jin saukar numfashinta mai fitar da sayayan kamshi ta ce, "mai kyau.! qara kauda kai yayi langwabe kai fatu tayi cikin siririyar muryarta ta ce, "yi hakuri idan nama laifi" ta miqe zata fita ruqo ta yayi tare da cewa, "shine dan zaki tafi gida shine ko ki leqo da safe? Lumshe ido fatu tayi ta ware su kan sadiq cike da kulawa ta ce, "yi hakuri, ka hada kayan naka?
"nope..!
"to na hada ma"
eh yace a taqaice d'akin ta shige ta hada masa nashi kayan cikin trolley ta fito da su dama shima ya shirya saboda tsabar zumudi ko break fatu ta kasayi haka Mom ta mata shatara na arziki har bakin mota ta rako su, acewarsu kwana biyu zasuyi su dawo saboda ankusa komawa school da sun dawo fatuha zata fara zuwa.

Sannan sadiq ya ja mota suka bar harabar gidan angel sai murna take tare da zuba masu surutu har bacci ya kwashe.

Ko 2 hours basuyi ba suka Isa wudil tunda suka iso fatuha ke bin kauyan da kallo, rayuwar ta da fatsima ta dawo mata sabuwa dai-dai kofar gidan su fatuha sadiq yayi parking har yanzu gidan nan yadda yake sai dai dan tsufa da ya fara sai yar kofar da akasa 6ale murfin mota fatu tayi cikin sauri ta shige gidan.

Inna na zaune saman kujera tayani gulma tana tankad'e, fatuha ta shigo da gudu tana cewa, "Inna..! Inna.! ta fada jikin ta cike zakuwa dagowa da ita inna tayi a dan tsorace washe baki tayi ganin fatuha binta inna tayi da ido dan dai fatuha na diyar ta da tace ba diyar ta bace, saboda girma da haske da ta qara bakin inna bud'e sallamar sadiq ce ta katse mata tunani ta ce, "kinga inna na bar mai kyau waje shida jidda" fita tayi tare da ba sadiq hakuri ta ruqo jidda suka shigo har qasa sadiq ya gaishe da inna, fatuha tayi ma inna bayani aiko inna hannu biyu-biyu ta amshe su dan ta yaba da hankalin sadiq jidda na gani inna ta samu kaka ta maqalewa inna, ta saki jikinta.
Da gudu fatuha ta fita daga gidan sadiq ya fita da ido bata zame ko ina ba sai gidan su fatsima, tana shiga ta shiga kwalla mata kira ba fatsima ba har Gwaggo a rude suka fito saboda jin muryar da suka dad'e suna kewa, da gudu fatsima ta fada cikin fatuha tare da sakin kukan farin ciki, murna wajan fatsima da fatu ba'a magana d'akin ta ja fatuha sai dai yanzu fatsima duk tayi sanyi nan take taba fatuha labari ranar daurin auranta mijin ya rasu, fatuha sai da ta tausaya mata sannan suka koma gida a tare lokacin inna har ta bama Sadiq masauki tare da kayan motsa baki jidda kuma na maqale da ita.

Kun san a tare suka wani da fatsima inda sadiq ke ta fushi fatuha ta barshi shi d'aya, basu suka rabu da fatsima ba sai gab da magrib lokacin Baffa ya dawo shima cike da farin cikin, inda ya dinga jan sadiq a jiki suna taba hira sama-sama, inna ta cika gabansa dafura da nono da tuwan dawa miyar kuka tasha manshanu, sosai sadiq ya saki jiki yaci abincin.

Misalin karfe 8:30pm bayan sun dawo daga masallaci sadiq ya wuce masaukinsa, bayan fatuha ta gama sa kayan bacci ta shirya jidda itama cikin nata sannan ta hada ma sadiq coffee kamar yadda ta saba a gida ta ja hannu angel suka wuce masaukinsa, da sallama ta d'aga labilan d'akin suka shigo, amsawa yayi a taqaice ta aje masa coffee ya amsa tare da aika mata harara wasa hannuwanta biyu tasa a kunne alamar bada hakuri tana rausaya kai d'an murmushi sadiq ya saki yana binta da kallo.
hira sukayi sama-sama inda angel ke ta zuba qiriniya har bacci ya kwashe ta, daukar ta fatuha tayi tana qoqarin fita sadiq ya mike ya masu peck tare da shafa kan angel dake kwance saman kafadar fatu, suka wuce d'akin fatuha.

*Washe gari*

Tunda safe fatuha ta tashi ta share tsakar gida tas, ta hura icce ta dora koko tare da dumama tuwan jiya, ta juye a kwanan samira tana qoqarin fitowa daga kitchen inna ta fito d'aga uwar d'aka washe da baki tana bin tsakar gida da kallo tana zancan zuci, alallai fatuha anyi hankali.! har qasa ta gaida inna ta amsa cikin fara'a sannan ta shige qurya ta fido jidda ta wanke ta tas ta shirya ta cikin jean n t-shirts masu kyau, sannan itama ta shige kewaye tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da sket na lace red mai kyau sai yar hoda data murza da lipstick ba qaramin kyau tayi ba sannan ta dau kwanonin da tasama sadiq abinci ta nufi d'akin inna da ke surfa gero ta ce "Aiko dazu da sasafe tare suka fita da Baffan ki gona" murmushi fatuha ta saki ta ce, "shine baffa bai je dani ba ko? ta zun6oro baki tare da shigewa ciki ta aje masa abincin tana fitowa ta ci qaro da fatsima, washe da baki ta tarbeta kusan a tare su kayi kallaci sannan suka fita yawo ganin gari, duk inda fatuha ta wuce sai antanka da irin kyanda tayi da nutsuwar da ta qara haka aka rinqa layin zuwa ganin fatu ta zama balarabiya, haka ta dinga baje tsaraba tana rabawa fatsima ko tasha tsaraba kamar ba gobe.

Kwana su biyu a kauye inda yan kauye ke cewa fatuha ta zo da larabawa, itama ta zama balarabiya sun sha yawo da sadiq har rafi sai da ta kai shi, da gona mai gari inda suke satar mangwaro a da, sosai ya ji dad'in kauyan ba dan kad'an ba.

Fatuha ce riqe da trolley tana rusa kuka ita bata komawa, sai da inna tayi da gaske sannan ta shige mota sadiq yasa trolleys a boot tare da yima Baffa shatara na arziqi, duk yadda Baffa yaqi amsa haka sadiq ya matsa masa ya amsa, haka Baffa ya dinga samasa albarka fatsima har da yar kwallata sannan suka dau hanyar kano cike da kewa.

********** ********** ******

Akwana atashi ba wuya wajan sallah fatuha dai ta fara zuwa makaranta inda aka sata jss1 sosai take maida hankali kuma tana gane karatun gashi Alhamdulillah Allah ya zuba mata qoqari na ban mamaki, dan har tafi masu qoqarin ajin a yanzu a tare suke zuwa da jidda a yanzu jidda na primary 2 kusan duk makarantar su d'aya da su Hanan da Basma hakan ya qarasa suka shaqu duk inda kaga Hanan to zakaga Fatuha ko Basma sosai suke maida hankali akan karatunsu.

Kamar yadda aka saba tashin su misalin karfe 3:30pm driven yayi parking suka bale murfi motar suka fito a tare, sanye fatuha take da uniform din ta riga mai dagon hannu milk sai sket dark green dai-dai gwiwa sai dan qaramin hijab milk, jidda kuma biri da wando ne sai milk riga a ciki green a sama kallo d'aya zaka masu kasan sun gaji likis tun a parlour jidda ta fara wurgi da jakarta fatu ta ce, "oh no why this angel bari dai grandma ta fito ta zane ki.! sama nayi da ido ina tunanin wake wurgo wannan turancin kamar a mafarki ashe fatuha ce ohni salma😧, daukar bag din jidda tayi tana zun6oro baki ta kai bedroom dinta,
Chapter 40 · 0% Book details