← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 67

Sashe 57

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

                   A dai-dai affcent center motocin suka faka lokacin har wasu sun halara tun daga bakin hall din kana jiyo irin sautin dake tashi, wajen ya hadu ba karya, kallo  daya  zaka masa  kasan  naira  tayi kuka wasu kujeru ne na  alfarma  a hall d'in wanda ko  ba'a  fada ba  zaka  gane  hall  din  na  d'an wane  da  wance  ne, jerawa yan'matan amaran sukayi masu ashobe, haka suma  abokan  angwayan suka  jera  reras masha Allah shigar ta su yayi kyau, amaran suka shiga tsakiya da angwayan Sadiq sai bin fatuha yake da kallo bugun zuciyarsa na daduwa, ta masa  wani  irin kyau ita kanta fatuha ta qasan ido take kallon sadiq tana jin wani irin kishinsa dan ba  qaramin kyau ya mata ba.
                      A natse suka shigo hall din, wajen ya gwarare da shewa da ihu, tuni aka canza salan kida da sauti majeed hannusa na maqale dana fatuha yadda ya shige mata kamar zai maida ta ciki, sadiq ya cika taf dan har ya fara jin kirjinsa na masa zafi duk  sanyi AC dake ratsa hall baya ji sai zafi  da  yake ji zufa na  karyo masa, kidin da  aka saki  sai  ya  qara  dagula  masa lusafi ya  fara  hanging jiri riqe hannu Basma yayi dan ba yadda zaiyi dan baya so ya bata ma qansa rai, ko bai so Basma  so  na aure ba yana sonta a matsayin ta na kanwar sa, sosai ya  damke  hannuta yana  sauke numfashi a hankali dake  neman kwace masa, ko da suka shiga gurin zama suka yi aka fara gudanar da shakali, can na hango su Aunty Rahenat anata kai kawo anzu shagali😜 ashe abin ba ita kadai ba ce har da yan Real Hausa fulani writers, can na hango Fulani da Aunty Rahama Nalele suna rabawa mutane kayan motsa baki, nima dai ba'a barni a baya ba dan na shiga a dama dani shoki kawai ake kwasowa.

          A hankali  majeed ya matso daf da kunan fatuha ya ce, "My love yanzu fa gobe kamar yanzu kin zama tawa ko? yana magana yana wasa da yan yatsunta Sadiq dake gefe yana kallon su bakin ciki na qara qumesa, dafe kirjinsa yayi domin yafara yi masa nauyi, zufa sai  karyo masa take tamkar wanda ke  bakin wuta a hankali ya miqe ya saci jiki ya bar guri tunda ya fito daga hall din jiri ke di barshi yana  had'a hanya yana  sauke  wani  irin numfashi mai  baraza na  da  rayuwarsa, ko gabansa baya gani dakyar ya iya isa inda akayi parking motarsa  ya daura hannusa kenan ya ji an riqe hannunsa, waigowa yayi su kayi 4 eye's da Dr yakub girgiza kai Dr yakub yayi ya ce, sa...!! bai furta abinda yayi niya ba ida sadiq ya fado jikisa sumame, rudewa Dr yakub yayi ya  cewa, sadiq..! captain..!  ka ga sadiq tashi ka  ji kalle ni ka  bud'e ido karka mana haka, ka  gani  ko abinda  zurfin  cikin ka  zai  ja  mana karka barni aboki na ka  ji  captain.! kuka yakub yake  sosai  ya  rude  ya  rasa  abunyi daukar sadiq yayi cak yasa a mota ya bar harabar gurin da gudu..

           Duk  wannan bidirin da ake  ba  wanda  yasan halin  da  sadiq ke  ciki  sai  Dr yakub, MC ne  ya  fara cewa, "amarya da ango  su  fito  su  yanka cake ango ya ba  amaryarsa itama ta basa" saukowa sukayi a hankali  suka  tsaya majeed ya yanka cake d'in yaba fatuha a baki itama  ta  basa hall din ya dau ihu, sadiq aka kira da Basma amma ba ango ba alama haka MC ya dinga kira ango ganin abin kunyar dake shirin faruwa yasa Khaleed hawa a matsayin ango yaba Basma cake a matsayin sadiq tuni hall ya dau tafi, Basma iyakar cika ta cika bata taba jin bacin rai ba irin na yau, yaune ta tabbatar da sadiq bai sonta kuma ba zai taba sonta ba tunda har ya iya wulaqantata gaban bainar jama'a, idanuwan ta taf da qwalla, tana tausayawa kantada irin rayuwar da zatayi a gidan Sadiq, haka akayi taro kusan duk abinda ango zaiyi ma amarya Khaleed ne yayi ma Basma.

                Ko da fatuha ta juya bata ga sadiq ba tuni idanuwan ta suka kawo ruwa, dama shi take gani tana jin sanyi a ranta.

            Ko da Dr yakub yaja mota basu zame ko ina ba sai asibitinsa, suna shiga aka turo gadon daukar marasa lafiya  sadiq da yanzu idanuwansa sun fara budewa saboda  oxygen d'in dake  manne  a  hancinsa haka yake ganin asibitin na juya masa numfashinsa na sama-sama, Dr yakub kuwa  kuka  yake  sosai, emergency aka wuce da shi doctorsa sun dade a kansa Dr yakub ma kasa shiga  yayi sai zarya da yake a bakin kofar kusan 1 hour suka dauka sannan aka fito da sadiq manne da oxygen a hancinsa daki aka bashi tare da sa masa life sport machine sai qarin jini da ake masa, a hankali Dr yakub ya qaraso gaban gadon yayi kneeldown, hawaye ne ke masa zarya  a hankali ya kai hannusa ya shafa sumar kan Sadiq ya ce, "Friend why me yasa kake bama kanka punishment haka? why sadiq.! ya ida zancan hawaye masu zafi na gangaro masa wayara ce dake  ringing ciki aljihu ya curo tare da kallon suna dake maqale a screen din majeed, kashe wayar yayi gabaki daya tare da jawo wayar sadiq ya kashe sannan ya dau kayan sadiq da aka cire masa yaba daya daga cikin ma'aikatan  asubitin su wanke.

          Bayan ankamala dinner kowa ya dau hanyar zuwa masaukinsa majeed sai kiran layin sadiq yake, baya shiga dana Dr yakub, yana mamakin  abun ya  faru yau ya  rasa  mai  ke  damun  sadiq hakura  yayi da kiran tare da maida wayar aljihu.

                  Bangaran Basma ko kuka take sosai tare da taqaicin amincewa da auran sadiq, Khaleed sai bata hakuri yake tare da ganin rashin kyautawar sadiq ya rasa dalilin da zai mata irin wannan cin fuskar bayan tana qanwarsa kuma matar da zai aura, shi a ganinsa duk wanda ya samu Basma a matsayin mata ya mure, ya rasa me yasa sadiq ke nuna rashin ko in kulla a kanta, kuma  majeed  na  gani  ko  ba  komai  yasan  dole  zai  ji  haushin sadiq da wannan tunanin suka qaraso gida ko Godiya bata masa ba ta shige gida da sauri tare da tsananta kukanta.

      Motar su fatuha na fakawa majeed ya fara jero mata kalaman soyayya tare da jan ta  jikinsa, ganin zai wuce gona da iri yasa fatuha sakin kuka,  lallashin ta majeed ya shiga dan  kukan fatu na  d'aga masa  hankali yayi mata peck, ko saurara shi ba tayi ba ta bale murfin motar ta fita da sauri.

        Bangaran sadiq ko bashi ya tashi ba sai wajan 2:00am na dare  a hankali yake ware sexy eye's ball's dinsa da wani irin ishin ruwa ya tashi, Dr yakub da ko rintsawa baiyi ba ya miqe da sauri ya qaraso wajan shi cikin cool voice sadiq ya ce, "Ruwa..! da sauri Dr yakub ya bude fridge ya dauko rubar ruwa ya bashi ko da ya sha ruwan miqewa yayi yana qoqarin cire jini da ake qara masa riqe hannusa Dr yakub yayi ya ce, "Captain me kake shirin aikatawa? ya fada bakin shi na rawa kallonsa Sadiq yayi ya ce, "so nake na tafi gida bana so majeed ya gane bani da lafiya, na  san  yanzu  haka  Basma name fushi  dani, na  ruguza  mata  farin cikinta  saboda  rashin  hakuri  na" ya ida zancan yana cire qarin jinin wasu hawaye ne masu zafi suka zubu ma Dr yakub ya ce, "Sadiq wai me yasa kake so ka raya rayuwar wani ka bata taka? why sadiq? Dr yakub ya fada yana jijiga sadiq kuka sadiq ya saki tare da cewa "ka  dai kiran  majeed da  wani  d'an uwa nane kuma  na  jini, bazan ta6a bari majeed ya mutu saboda bakin ciki na ba, nafi son farin cikin majeed a kan na kowa a duniya, bani da d'an uwa sama da majeed, kasan  ko  ya  majeed  ya  ke  waje na  yana  so na yana  son  farin  cikina, tunda  da  nake  da  majeed  bai  ta6a nuna  min  abinda  yake  so  ba  kamar fatu  ba, ina  iya  ce ma  kan  fatu majeed  ya  san  me  so saboda haka ban taba bari saboda ni ya rasa rayuwarsa..! sadiq ya ida zancan yana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare a hankali ya ida cire kayan asibiti dake  jikinsa yasa kayansa wayarsa ya dauka tare da kunna ta Dr yakub mutuwar tsaye yayi yana bin sadiq da kallo cikin  bacin  rai ya  ce, "kai  taka  rayuwar yaya  za'ayi  da  ita, kai  taka  zuciyar  ayi  yaya  da  ita? Sadiq  ka  fahimce  ni  kafi majeed  buqatar  fatu, kafi  majeed  son  ta, ka  duba  halin  da  kake  jefa  kanka, ka  falasa  abinda  ke  ranka  tun  kafin  gobe  fatu  ta zama  malakin majeed..! tabbas yanzu yasan me sadiq yake nufi so yake ya rasa rayuwarsa ya zamar masa dole ya kawo karshan abunan ko saurarashi sadiq bai yi ba saima car key daya dauka tare da fita yana ingisawa.....

Vote
Comment

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                         91_92
Chapter 57 · 0% Book details