← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya gama ne moddibo yay gyaran murya irin nasu na dattijawa ya kalli matashin yace "yaro yau dai gashi ka warke cikin ikon Allah bayan doguwar jinyar ɗakasha a tareda mu yau gashi har kana shirin tafiya, sedai kuma har yau bamu San Ainihin kokai waye ba, se nake ganin a yanda mukai sabo dakai ya kamata musan koda kaɗan ne daga tarihin Rayuwarka ko babu komai m ƙulla zumunci.

Sabida wata rana bamu San a inda zamu sake haduwa da juna ba!

Sosai kalaman moddibo suka taɓashi dan harga Allah yanajin tsohon a Ransa, tabbas gaskiya ya fada
Ya kamata ya gaya musu ko shi É—in wanene.

Murmushi yayi sannan yace " sunana Muzaffar Abdulwahab Abdullah the C.e.o of zafar Enterprises .....!

Sushmah 💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :12-13_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️"Ni ɗane ga Abdulwahab Abdullah, mu uku kawai Mahaifinmu ya haifa kaf cikinsu nine babba se Fadilah Sannan zainab, ni kaɗaine Namiji kuma wanda ke jan ragamar kamfanoninsa dake nan gida Nigeria harma dana ƙasashen waje. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ƙara da cewa

"mahaifina Haifaffan Garin kano ne a unguwar Hotoro Su biyu ne kaɗai a gurin iyayensu dashida ƙanwarsa Asma'u muna kiranta da Mama.

Mahaifinsu Shahararren ɗan kasuwa ne sosai, wanda ya kasance kaf garin na kano ana matiƙar jidashi a ɓangaren shaharar kasuwanci, ya Rasu yabar duniya a lokacin da Mahaifina yake dabda kammala karatunsa na Scondry school inda Asma'u kuma take dabda shiga sas 2, bayan Rasuwar kakana ba jimawa Itama mahaifiyarsu ta bishi sakamakon Ciwon zuciya, bayan Rasuwar Hajiya da kimanin shekara 2 Mahaifina ya fara tasowa sosai a ɓangaren Kasuwanci sabida yanda Allah ya sanyawa dukiyar Albarka, cikin ƙanƙanin lokaci Sunansa ya zarta na Mahaifinsa a fanin shahara a duniya, bayan Asma'u tayi Aure ne ta buƙaci da A raba musu gado

Sosai Mahaifina ya nuna mata rashin dacewar hakan amma sam taƙi fahimta dole yasa ya amince da abinda tazo dashi ɗin kuma ya yakai maganar kotun Musulunci dake Kano aka raba musu gadon, bayan an Raba musu gado dashida Ƙanwarsa Asma'u Itama ta fara business da kuɗaɗenta sedai bata ɗauki lokaci me tsaho ba jarin nata ya karye, shiko Mahaifina tamkar ana ƙara ɗagashi haka dukiyar ta dinga haɓaka sedai sam hakan besa ya canzawa ƙanwar tasa ba yana matiƙar sonta sosai sabida shikaɗaine ya Rage mata a Rayuwa don haka dole ne ya kyautata mata.

Koda Muzaffar yazo nan a zancensa seya kalli moddibo yace "baba wannan shine tarihina a taƙaice.

Zuru Moddibo yayi masa yana kallonsa cikeda Rashin Fahimta yace "har yanzu yaro baka sanar dani abinda nake son ji a tareda kai ba, kana so ka gaya min cewar dama ba Sunan ka muhammad Ali ba kamar yanda ka gayamin a baya ba?

"Meyasa ka zaɓi hanyar yaudarata bayan nida zuciya ɗaya na zauna dakai?

Jikin Muzaffar ba ƙaramin sanyi yayi ba sannan yace "don Allah ka gafarce ni Baba karkaga laifin pls, ni mutum ne me mu'amala da mutane kala-kala a hakan kuma wanda ake farautar Rayuwarsa ta ɓangarori da dama, shin laifi ne don nayi ƙaryadon na kare kai na?

"a'a yaro sam ba laifi kayi ba indai har ta fuskar tsaron lfyar ka ne, amma ta wata fuskar tabbas ka cutar da yarda ta a gareka. "aa don Allah baba karkace haka wllh bada nufi nayi ba amma tabbas nasan nan gaba zaka Fahimceni akan manufata na ɓoye maka Asalina! Modibbo yay Ajiyar zuciya yace "Shikenan na karɓi Uzirinka sannan innai maka fatan Alkhairi a Rayuwark ta gaba, sedai kafin ka tafi zan baka wata babbar gudun mawa wadda nake da tabbacin cewar zata taimakeka da izinin Allah koda ko wani irin yanayi zaka shiga. Moddibo ya faɗi hakan a lokacin dayake miƙawa Muzaffar wani jiƙo dake cikin ƙaramin ƙoƙo ya shanye.

Seda ya shanye tass sannan ya kalleshi yace "Baba wannan maganin na menene ? Moddibo ya kalleshi yace "maganin tsarin jiki ne dana gajeshi a gurin mahaifina wanda ya gargaɗeni kan cewar kar in badashi ga kowa se wanda naji zuciyata ta Amince dashi sannan zan iya badashi, har A raina nakejin cewar na yarda dakai shiyasa ma harna baka wannan dafa'in namu na gado wanda nakeda tabbacin cewar zakaga amfaninsa a gaba koda kuwa banan kusa bane, nidai nasihata a gareka shine ka riƙe Gaskiya da kuma amana karka taɓa bari zuciyarka ta ruɗeka ka cutar da wanda yayarda dakai komai rintsi.

Sosai jikinsa yay sanyi da kalaman Moddibo dan haka ba tareda zato ko tsammani ba yay jashi jikinsa ya Rungumeshi yanajin wani iri a zuciyarsa wanda ke kamada yanayi na kewa.

Zare jikinsa yayai daga na muzaffar sannan ya ɗau Boron Maganinsa yayi waje abinsa ba tareda yace dashi ƙala ba, shima muzaffar ɗin fita yayi waje seda ya ɗauki lokaci me tsayi sannan ya koma cikin gidan a ciki suka haɗu da Rabe tana ƙoƙarin shiga ɗakin Moddibo, bin bayanta yayi shima

Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi tunda ta zauna take kallon sa tun be lura ba har ya ya fahimci irin kallon da take masa, amma seya share sabda yasan indai ya kalleta dena kallon sa zatayi, shi kuma haka kawai yaji baya so ta dena kallon nasa, haka kawai yaji yana son hakan har cikin Randa.

Ta jima tana aikin kallon sa sannan ya dago idanunsun ya sarƙe cikin na juna kashe mata ido,
Da sauri tayi ƙasa da idanunta sbda wani irin kwarjini dataga yayi mata bugu da qarima ga kashe mata idon dayayi.
Abine ya bashi dariya sosai sannan yace" o'o yau na kama Fulani Girl tana satar kallona da alama she wants to say something oya say it. Ya faÉ—a yana wani kallonta

Kasa É—agowa tayi haka kawai setaji tanajin kunyarsa dukda irin damuwar dake Ranta akan tafiyarsa, kamar me koyon magana haka ta fuÉ—e baki tace "meyasa zaka tafi bayan mun saba dakai?

Ɗan jim yayi yana kallon gefanta kaɗan sannan yace "sabida inaso naje namu gidan nima naga iyayena I'm sure of that Suna nan suna nemana wata ƙilama har abinci basa ci. Faɗa fuskarsa na sauyawa

"Nasan suma zasu shiga damuwa duk a rashin ganinka da basayi, na tabbata muma irin damuwar zamu shiga a sanadin sabon da mukayi dakai. Rabe ta faÉ—i hakan hawaye na taruwa a manyan fararan idanunta

Kasa ce mata komai yayi hakan yasa ta kalleshi tace "meyasa ka ɓoye mana gaskiyar sunan ka?

Kallonta yayi yace "sabida lokacinda ya kamata ku sani beyi ba shiyasa.

Kallonsa kawai takeyi a ranta tana mamakin halinsa, yanzun nan ze sake dakai har kuyi hira amma lokaci guda seya gimtse kamar bashi ba, taɓe baki tayi tace "inaso nasan sunan naka da bakaso a sani?

A taƙaice yace "Muzaffar Abdulwahab Abdullah.

Kallonsa tayi tareda wara manyan idanunta tace "gaskiya sunanka yanada tsayi sosai zan iya kiranka da Zafar?

Kallonta kawai yake harta kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi yace "As you wish

Bata sake cewa komai ba tayi shiru wanda hakan ya bashi tabbaci akan cewar bata cikin yanayi me daÉ—i

Jikinsa a mace ya kalleta yace"wllh bana so ki dinga sa damuwa a ranki gameda tafiya ta nace miki idan na tafi zan dawo wani lokacin bazan daÉ—e ba kodan sabida ke.
Ya ƙare maganar tare da nuna ta da hannunsa

Sosai maganarsa tayi mata daɗi har hakan yasa ta saki murmushin daya ƙara baiyana kyawunta sannan tace "na yarda dakai yaya zafar! Nasan bazaka manta dani ba kuma nima bazan manta dakai ba zafar komai yawan shekarun daza'ayi nan gaba.

Da sauri ya kalleta a ransa yana mamakikn yarinyar, wayonta da maganganunta ya zarta shekarunta da ace zata samu wayewa a tareda ita tabbas da anyi cikakkiyar Æ´ar baiwa a nan wajen iya tsara magana cikin hikima.

A nitse ta kalleshi tace Hamma zafar idan ka tafi zanyi kewarka sosai bazan gaji da gayamaka cewar na saba dakai ba koda zan maimaita shekarun haihuwata ne ina faÉ—a maka, ni kaina bansan dalilin daya sa nake jin zafin tafiyarka a raina ba zafar!

Sosai yake kallon ta tunda ta fara magana sannan yace"ni kaina Ina jinki a raina Rabi'atu! Ta yanda har nake jin bana so na tafi na barki a nan! Har ga Allah naji jini na ya hadu dake, bama Iya nanan abin ya tsayaba kinada gurbi a zuciyata kamar yanda Zainab take da muƙami a cikim Raina!

Kamar daga sama yaji ta jefo masa tambaya tace "wacece Zainab?

Murmushin gefan baki yayi yace "she's my younger sister, inasonta Sosai sabida tana iya haƙura da komai don tabbatuwar farin cikina, shiyasa nakeji da ida Except Fadilah.

Taɓe baki tayi sannan ta kauda kanta don harga Allah ba gane maganarsa take sosai ba, abu ɗaya kawai ta gane shine ƙanwarsa ce.

Murmushi kawai yayi sannan yacigaba da cewa "duk duniyar nan Bayan Abie da Momy tareda sauran ƙannena babu wanda ya samu kusanci dani se ke! Dan haka kina da matsayi na musamman a zuciyar Muzaffar Abdulwahab Abdullah.

Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake faɗa mata , ta Daɗe tana juya abin a ranta daga ƙarshe data kasa gane manufarsa seta jefa masa tambayar datasa har seda ya ɗago ya kalleta tace "Hamma zafar dama ana Iya bawa mutum matsayi a zuciya?

Da sauri ya ɗauke kansa daga barin kallonta sannan yace " a'a ba'ayi kawai dai na faɗa ne nima. suna cikin maganar Laure ta bankade ƙofar ɗakin tace "to tsinanniya fito nan kiyi min aiki
Kin shige ɗaki da garjejen namijin da a tsaye yafi ubanki ƙirar ƙarfi da tsayi kuna lalata, in banda masifa da jaraba irinta yaran zamani inake ina wannan gabjejen ƙato wanda ko babbar macen kirki ma setaci baƙar wuya a hannunsa Amma dan rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba !
Shegiya me bin maza karuwan wofi.

sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai dukda bada hausa tayi maganar ba ya fahimci komai, amma seya danne zuciyar sa yay kamar be gane abinda take faÉ—a É—in ba.
Chapter 8 · 0% Book details