← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 57

Sashe 6

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana taba jikinta yace " subahanallah!!
Rabe meya sameki be jira cewarta ba ya kinkimeta yayi Ɗakinsa da ita banda hawaye babu abinda ke fita a idonta a haka ya Ƙaraso Ƙakin da ita,
Da sallama ya shigo ÆŠakin sannan ya kwantar da Ita.

tunda suka shigo Ɗakin gaban Sa ya faɗi ganin wadda moddibo ya kwantar Daga ɗan nesa dashi, a rude yake tambayar moddibo abinda ya sameta har yana Ƙoƙarin tashi daga inda ya ke kwance,
Sosai moddibo ke kallonsa girmama sanin yakamata irin na matashi, cikeda tsantsar so da Ƙauna Moddibo yace "yaro ka kwantar da hankalin ka ba wani Abu bane zazzabi ne kawai Kuma zata samu sauƙi da izinin Allah. Ya faɗi hakan yana kallonsa

Har ga Allah moddibo yaji Matashin ya Ƙara kwanta masa a rai musamman dayaga ya nuna kulawar sa a kan tilon 'yarsa guda daya!

Wai shin wanene wannan matashin ne kuma mene cikaken sunansa?

Sannan kuma meyasa yake fargabar komawa ga iyayensa ?

Menene hujjarsa na ƙin gayawa modɗibo sunansa a lokacin daya tambayeshi Ya gaya masa wani sunan na daban?

Comment
And
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

_Page : 8-9_

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️Murmushi moddibo yay masa sannan ya juwaya ya ɗakko ƙatuwar Boron sa (jaka) dayake sa magani a ciki ya ɗaukko wani farin magani ya jiƙashi a wani madaidaicin kwanon sha, seda ya ɗan ɗauki lokaci sannan ya ɗgota ya fara ƙoƙarin bata,

Ba tayi masa gaddama ba ta karɓa tasha sabda bata ƙin magani kokaɗan.

Duk abinda suke idon sa yana Kansu se kallon su yake a ransa yana mamakin yanda moddibo yake Iya gane ko wani ƙullin maganin dake cikin jakar, shi'a tsarinsa sam be yarda da maganin Gargajiya ba sena Asbiti a cewarsa wai a maganin Gargajiya baya maganin cuta sedai ma ya ƙarawa mutum wata cutar. Amma se gashi a yau maganin Gargajiya yayi masa ranah fiyeda zatonsa.

shiyasa a rayuwa kada ka raina baiwar da Allah yayiwa wani ko wata komai ƙanƙantarta idan ba haka ba watara seka samu kanka da a ƙarƙashin Abinda kake Rainawar kuma yayi maka Rana.

A hankali seyaji abin yana birgeshi sosai lallai ilimin sanin itace shima abune me zaman kansa bawai kowa ne yake da wannan baiwarba, domin kuwa shima abune me zaman kansa. Bata jima da shan maganin ba bacci ya ɗauketa ta banda zufa ba abinda takeyi wanda hakan ya bawa moddibo tabbacin cewar zazzaɓin ya sauka.

Matashin ya kalli moddibo cike da damuwa yace "ya Kamata kayi wani Abu kagafa se gumi take kodai zamu kaita asibiti ne??

Kallon tsaf modibbo yayi mai da mamaki kwance akan fuskarsa sannan yace "hmmm a wannan ƙungurmin Dajin kake tinanin Samun Asibiti?

Batare da tunanin komaiba yace "ae mana aiko ba'a
Nan ba ina zaton idan muka fita da ita zuwa cikin gari zamu sami Asibitin dazamu kaita. Ƙura masa idanu moddibo yayi harya kai ƙarshen maganarsa take yanayinsa ya canza yace "yaro ka gani nan tunda na tashi da iyayena a nan muke Rayuwa bamu taɓa tunanin muyi nisa da nan ba tunda muka dawo nan muka yada zango damu da jama'armu, Asalin mu 'yan jihar Adamawa ne Haifafun NUMAN ne mu ba Asalin cikin garin Adamawa ba a cikin Daji muke Rayuwa tareda Dabbobin mu, dolece tasa mukabar Mahaifarmu muka dawo nan Sabida wata Masifa data Afka mana.

Modibbo sauƙe ajiyar zuciya yacigaba da cewa " mu uku kacal iyayenmu suka Haifa, mu biyu ne maza se kuma Ƙaramar kanwar mu BADDO wadda a halin yanzu bansan inda take ba Shin tana Raye ne kokuma ta Mutu Allah shikaɗai ne masani!!! Ya faɗa Hawaye na Sakko masa.

Wani irin kuka ne ya taso masa wanda ya daɗe beyi irin sa ba a wannan lokacin, koda Wasa Matashin beyi yinƙurin ya dakatar dashi ba sabida ya samu Zuciyarsa tayi Sanyi

Seda yayi me isarsa sannan ya daidaita nutsuwarsa ya cigaba da cewa " tun daga Ranar da muka nemi ƙanwata Baddo Muka rasa iyayen mu suka shiga tashin hankali mara misaltuwa, bayan wanda muka samu kanmu a ciki kafin ɓatanta, wannan dalilin ne yasa muka tattara ƙwanmu da ƙwar-kwatan mu mukabar NUMAN muka dawo nan da zama sakamakon ƴan fashin da suka sa mu a gaba ba dare ba Rana, babban takaicin ma shine ba Iya fashin da suke mana bane matsalar har yaran mu mata ƙanana suke yiwa Fyɗe a gaban idanun mu ba tareda imani ko tausayi ba.

wannan Shine dalilin dayasa muka bar jaharmu ta asali muka Dawo wannan dajin, dikkan mu dakake gani duk ƴan uwan juna ne, shiyasa muke zaune lfy lau a nan ɗin batareda mun leƙa cikin gari ba ko hanyar titi bama bi Tunda ɗan Uwana Zakariya ya gamuda Haɗarin mota a sanadin tsallaka titi, a lokacin da muka ɗakkoshi ya Rasa jini sosai shiyasa muka yanke shawarar mukaishi Asibitin, mashin ɗin malm Iro muka hau mu uku muka nufi Babban Asibitin Gwamnati dake cikin garin gyambu Amma sam sukaƙi taimaka mana, munaji muna gani a gaban idon mu Zakariya ya Rasa Rayuwarsa munyi kuka har muka gode Allah sannan muka sake ɗakko gawar muka dawo da ita gida, tundaga lokacin zuwa Asbiti ya gama ficemin a rai wllh ko sunansa ma banason sabida mutanan mu na wannan lokacin a cike suke taf da son zuciya gamida Rashin tausayin talaka.

"sosai jikin matashin yayi da labarin Moddibo wanda yay matiƙar taɓa masa zuciya sannan yace "A zaman danai dakai na fahimci cewar kai mutum ne na musamman wanda yakeda shahararriyar baiwar da kaikanka bakasan iyakarta ba, da ace Hukumar lfy zasu samu labarinka tabbas dasun Amfana dakai ta ɓangare da dama musamman abinda ya shafi sani akan itacen gargajiya

"Hmmm kaidai ai sha'ani kawai yaro amma lamarin mutanan dake cikin wannan duniyar sesu,
Wata rana da yamma bana mantawa wasu mutane suka shigo mana Nan da sunan Su jami'an hukumar lafiya ne, kuma sunzo ne don su kafana mana Sansaninsu a nan sbda muma mu samu cigaba.

"batareda tunanin komai ba muka karbe su hannu biyu Ashe abinda bamu sani ba shine cutarmu sukazo suyi, Dayawa a cikin mu kasuwanci shanu mukeyi wanda ya zame mana tamkar Sana'ar Gado seda suka bari kowa ya dawo daga kasuwancin sa yaxo da kuɗaɗe masu yawa sannan suka far make mu cikin Dare suka ƙwace komai sannan suka kashe na kashewa,
Tun daga lokacin bamu ƙara yarda da kowani mahaluki ba, hatta baƙi ma muka dena karbarsu koda kuwa daga ina suke.

"shiyasa tunda naju ka ambaci sunan Asibiti kaga yanayina ya canza yaro sabida ko sunan Asibitin banason ji wllh, yanzu zancen danake maka wllh da mutanan Rugar nan zasu samu labarin zuwanka tabbas da se sun koreka kokuma ma su kashe ka.

A firgice Matashin ya zaro manyan idanunsa yana kallonsa jin kalmarsa ta ƙarshe wato kisa sannan yace "to Baba meyasa lokacin da abin ya faru Baku nemi tai makon jami'an tsaro ba ???

Moddibo ya kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace " yaro da fari minyi ƙoƙarin gwada yin hakan amma daga baya se muka gane itama hukumar se a hankali.

Matashin yayi shiru a zuciyarsa yace "Ashe Dama a kwai mutane masu fiskantar irin wannan rayuwa?? Be taɓa zaton a kwai irinsu moddibo dake Rayuwa a cikin wannan halin me cikeda ƙunci ba,
Tabbas Allah ne ya Ƙaddara zuwansa wannan gurin dan ya Ƙara Imani a kan rayuwar duniya,
Haƙiƙa baka sanin Allah yayi maka Wata ni'ima a Rayuwarka har seka ga Wanda be kaika ba sannan kake sanin Allah yayi maka Gagarumar Ni'ima,
Haka kawai seya samu kansa da jin tausayin su tareda ƙudurtawa kansa cewar insha Allah seya temakesu da wani jinjinan Abu daze Amfanesu da izinin Allah.

Tunda garin Allah ya waye Laure ta fice daga Gidan sabda bata da wani buri yanzu a rayuwata daya wuce Rayuwar Rabe bata inganta ba kamar ta Sauram Sa'o'inta, tafiso tayi Rayuwa a ƙasƙance ta ƙare a tantal baɗeɗe, shiyasa ta ɗorawa zuciyarta tsanar yarinyar tun batakai haka ba, duk wani buri na laure a yanzu be wuce taga ta samu haihuwa da Moddibo ba ta hakane kawai zata iya mallake dukiyar sa.

Tabdi kujifa masu karatu!
Dama ance yanzu ba'a maƙiyin nesa , ya Allah ka shiga tsakanin mu da maƙiyan mu na sarari Dana boye🤲
********

*ZAFAR ENTERPRISES* shararren Companyn dayay fice a ɓangaren kasuwanci a cikin ƙasashen Duniya guda 12 , waƴanda suka haɗa da America, Germany, Cairo,London da sauran ƙasashen duniya wanda yake mallaki ga babban Ɗan kasuwar nan Alhaji Abdulwahab Abdullah, dandazon ƴan Jaridan na hanga a Harabar Babban Companyn nasu dake Garin abuja banyi ƙasa a gwiwa ba na kutsa ta cikinsu yaja tunga na tsaya don in samu damar ɗakkowa masu karatu Rahoto.

Wani farin Mutumi ne ya fito wanda baze wuce shekaru Sittin ba a duniya (60years) Sanye cikin wata dakakkiyar Suite Baƙa wuluk da ita se ɗaukar idanu takeyi, tafiya kawai yakeyi Fuskarsa a tamke babu Annuri, inda bodyguards ɗinsa majiya ƙarfi kimanin Mutum biyar suke take masa baya harya ƙaraso ga ƴan jaridar, nan da nan Sukayi masa caa tamkar ƙudajen da sukai arba da Buhun Sikari abinka da babban mutum kuma me wahalar gani

Kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tashin hankalin dayake ciki duk a sanadin Ɓatan tilon ɗansa tsahon wata Uku babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan yaron, cikeda Damuwa Dattijon ya sauke glass ɗin dake idanunsa ya fuskanci, wani irin takaici ne ya ƙara samun muhalli a zuciyarsa sabida besan abinda ƴan jaridar nan suke nema dashi ba, wannan wace irin masiface ??

A halin dayake ciki a yanzu bayajin zasu iya samun koda kalma ɗaya daga gareshi, Wata matashiyar yarinya ce ta fito daga Companyn itama sanye da Suite Royal blue riga da wando, ƙafarta sanye take cikin wani dogon takalmi me tsinin gaske ta sanya wata irin hula wadda tafi kamada ta mata ƴan ƙwalisa, inda ta rufe idanunta a cikin wani baƙin glass wanda ya mamaye rabin Fuskarta.
Chapter 6 · 0% Book details