← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 57

Sashe 19

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikeda girmamawa matashin Drivern yace "I don't know sir but let me check. Maida hankalinsa kan wayar yayi batareda ya damu da abinda ke faruwan ba yaji an ƙwanƙwasa glass ɗin motar dayake ciki, cikeda damuwa Wanda ya ƙwanƙwasa ɗin yace "im sorry sir hatsari muka samu a sanadin bige wata yarinya.

Da sauri guy É—in ya ajiye wayar ya fito cikeda tashin hankali, sanye yake ciki wata dakakkiyar suit's maroon colour dogo ne sosai ma'abocin cikar zati da kuma kwarjini, sam be kasance cikin jerin maza masu hasken fata ba amma yanada gogewar fata sosai irinta Æ´aÆ´an masu hannu da shuni.

Gabansa ne ya faÉ—i a lokacin dayayi arba da jinin dake futa ta hancinta da kuma kunnenta, a hanzarce ya tsuguna yace "pls be fast let's take her to the hospital.

Babu ɓata lokaci suka sanyata a cikin ɗaya daga cikin motociɓ batareda sunyi la'ajari da kar jinin ya ɓata musu mota ba suka kwasa da wani mahaukacin gudu suka nufi wani ƙaramin hospital dake dabda cikin wani ƙaramin ƙauye dake maƙotaka da dajin. Babban abinda ze bawa me karatu mamaki shine still her hand is on the wannan jakar da Modibo ya Rataya mata.

Tofa ana wata ga wata 🤔

thanks 4d love guys

comment
nd
share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :23

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️Cikin mintunan da bazasu gaza goma ba likitan dake on duty ya shiga bata taimakon gaggawa don gudun kar jinin dake fita ta kunnenta ya samu nasarar taɓa ƙwaƙwalwar ta, dukda cewa Asibitin basuda isassun kayan aiki sunyi bakin ƙoƙarinsu akanta kuma Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida zubar jinin cikin sauƙi.

Gabaɗaya haɓkalin matshin a tashe yake dukda cewar mutum neshi me izza Amma sam bashida kwanciyar hankali yayinda yaga na ƙasa dashi a cikin hali na buƙatar taimako, likitam na fitowa Direct gurin matashin ya nufa tareda miƙa masa hannu yace "congrats munyi nasara wajen tsaida zubar jinin sedai tana buƙatar ƙarin jini sabida tarasa jini dayawa amma yanzu hkaa mun saka mata drip da ace so samu ne ku miƙata ga babban Asbitin don gudun karta samu matsala a ƙwaƙwalwar ta, Zaro ido matashin yayi tareda dafe kansa cikeda damuwa yace "oh my God!!!!! Kallonsa ya mayar ga guards ɗinsa sannan yace " nanda zuwa wani lokaci zamu isa Abuja daga nan?

Kallonsa sukai da kulawa sannan ɗyaa daga cikinsu yace" ranka ya daɗe zamu iya ɗaukar lokaci me ɗan tsayi kafin mu isa sabida doguwar tafiyace sosai amma zamuyi iya bakin ƙoƙarinmu don ganin mun isa akan lokaci da yardan Allah. Ajiyar zuciya ya sauke meɗan nauyi sannan ya biya kuɗin Asbitin tareda bada umarnin a fito da ita asa a mota zasu wuce, ba musu suka shiga cikin Asbitin suka fito da ita tareda sanyata a bayan ɗaya daga cikin motar suka kwantar tareda gyara mata zaman drip ɗin dake saƙale a hannunta sannan sukaja motoci @360

Ba ƙaramin gudu suka dinga zubawa ba cikin ikon Allah kuwa suka shigo garin Abuja akan lokaci, wani hamshaƙin Asibitin kuɗi suka nufa da ita wanda ke cikin Asokoro inda Family Dr. Ɗinsu ke aiki me Suna Mujaheed Abdullahi, cikin ƙanƙanin lokaci suka shiga bata taimakon gaggawa abinka da masu citta a hannu sun juma suna gudanar da aikinsu a kanta sannan Dr. Mujaheed ɗin ya fito daga ɗakin wata matashiyar nurs na biye dashi a baya.

Direct inda matashin ke zaune tareda Gurds ɗinsa Dr. Mujaheed ya nufa sannan ya kalleshi yace "muje office ba musu ya miƙe yabi bayansa seda duka ɗanyi tafi kaɗan sannan suka isa office ɗin me shegen kyau sannan suka zauna, cikeda damuwa matashin yace "ya jikin nata Dr.? Murmushi Dr. Mujaheed yayi yace "ka kwantar da hankalinka Edriss insha Allah komai zeyi daidai, ka godewa Allah ma kun kawota akan lokaci. Murmushin jin daɗi Edriss Adam yayi tareda faɗin "Alhamdulillah Dr. Wllh har hankalina ya kwanta.

Magungunan da suke buƙata ya rubuta masa tareda cewa "a halin yanzu tana buƙatar jini domin kuwa ta rasa jini dayawa, mun binkita mun gani launin jininta me wuyar samu ne kuma ya kamata a ƙara mata shi da gaggawa idan ba haka ba gaskiya something can happen to her. Da sauri Edriss yace " no Dr. You can take my own because nau'in jini na ze iya yiwa kowa

Ƙura masa manyan idanunsa Dr. Mujaheed yayi a zuciyarsa yana mamakin yanda Edriss ya damu da wannan baiwar Allah, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "who is she to you Edriss?

Murmushin rainin hankali Edriss yayi yace "ba wannan ba tukun muje ka ɗau jini na. Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar ƙwayar idon Mujaheed ɗin

Basarwa yayi ya miƙe yace "bani zan ɗau jininka ba Edriss yanzu dai zan turaka inda za'a ɗauka ɗin, cikin mintunan da bazasu gaza 10 ba akayi komai aka gama se'a lokacin hankalin Edriss ya kwanta sannan ya wuce gida donya samu ya huta.

INDIA🇮🇳

dakewa Ummie tayi tana binsa da kallo tamkar wadda aka dasata a gurin, gaba ɗaya ji take komai ya tsaya mata chak har motar Asibitin ta ƙaraso ƙofar gidan still tana tsaye kan ƙafafunta, Maryam ce ta fita da hanzari tayo musu jagora zuwa cikin gidan inda muzaffar ɗin ke kwance samɓal babu alamar numfashi a taredashi, kin kimarsa sukayi suka ɗorashi bisa wani siriri gado sannan suka fito dashi Zuwa cikin motar, basu jira fitowar wani daga cikin gidan ba sukaja motar sabida ganin irin condition ɗin mara lfyn se bayan sun fita Hajiya Aisha ta zube bisa doguwar kujerar dake falon tana maida numfashi

wayar muzaffar dake kusa da System ɗin Ummie ce ta fara ƙara kasa ɗagawa ummie tayi hakanne yasa maryam ta isa ga wayar jikinta na wani irin rawa ta Amsa ba tareda ta duba sunan me kiran ba, cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali mom tace "boy are you Ok?

Wani irin fashewa Maryam tayi da kuka nan ta shiga zaiyanawa Mom halinda muzaffar ɗin ke ciki. Wani irin Zabura mom tayi ta miƙe zaune daga kwancen da take cikin yanayi na fitar haiyaci tace "ɗan nawa ne yafi guba ??????

Abie wanda ke kwance ne ya miƙe idansa nakan Mom wadda jikinta ke wani irin rawa sabida tsabar tashin hankali, fashewa tayi da kuka tana danne ƙirjinta dake mata wani irin suya ta kalli Abie bakinta na rawa tace "kagani ko? Senayi magana sekace kishi ne ke ƙoƙarin hanani zaman Lfy da Aisha to gashi nan yau ta zubawa ɗana guba a abinci kuma ya........... Girgizata yayi da wani irin Sauri sabida ganin idanunta na ƙoƙarin rufewa take mom ta dawo daidai cikin haiyacinta tareda faɗawa jikin Abie ta saki wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wata uwa datasan ma'anar haihuwa. A daran ranar Abie yayi hayar privet jet zuwa ƙasar India aiko kiran sallar farko suka himmata sukabar ƙasar.

India 🇮🇳

Hajiya Aisha da ƙyar ta iya miƙewa ta koma ɗakinta tareda zubewa a bakin gadonta zuciyarta duk a cushe, gabadaya komai ya tsaya mata tayanda takejin cewar dama hakan bata faru ba do take tayi kuka amma kuma ta kasa yin hakan, dama idan wani bala'in ya sameka hawayen ma ɗaukewa yake gabaɗaya a haka har gari ya fara haske still tana zaune batareda ta rintsa ba.

cikin ikon Allah jirginsu Abie ya sauka lfy cikin mintuna kaɗan motocin company sukazo ɗaukarsu Kasan cewar basu san Asibitin da aka kwantar da Muzaffar ɗin ba dole yasa suka ɗauki hanyar gidan Hajiya Aisha, gabaɗaya mom ta birkice tamkar wata zararriya idanunta duk sunbi sun koɗe sabida kukan data gurza, a haka motocin suka tsaya a bakin ƙofar gidan cikin jerin gwano.

kokaɗan basu jira an buɗe musu ƙofar motar ba kamar yanda suka saba mom ta ɓalle murfin motar ta diro tana huci, da wani irin sauri ta shiga gidan tana kwaɗawa Ummie kira a birkice, sautin muryarta ne yasa Hajiya Aisha tasha jinin jikinta kuma ta fito daga ɗaki jikinta a saluɓe tamkar kazar da ƙwai ya fashe ma

tana fitowa idonsu ya sarƙe cikin na juna a karon farko tun bayan shekara 35, wani irin wawan Mari mom ta ɗauke Ummie dashi har seda taga taurari tun kafin ta watsetsake ta ƙara ɗauketa da wani marin, cikin kiɗima Ummie tace "ni kika mara Saratu?

cikin fusata Mom tace "na mareki Kiyi duk abinda zakiyi, Se yau na sake tabbatar da cewar ki cikakkiyar shaiɗaniya ce Aisha kuma wllh ki kwana da sanin cewar sena hukuntaki a bisa laifinki na bawa ɗana guba wllh koda kuwa abinda na mallaka ze ƙare akan shariya dake!!!!

Abie dake tsaye yana kallonsu ji yayi duk Hajiya Aisha ta sure masa a rai a sanadin abinda ta aikatawa gudan jininsa namiji tilo tabbas baze ƙyaleta ba a wannan karon dole ne shari'a tayi aiki akanta, ya juya yana kallon jami'an tsaron dake bayansa yace "ku tafi da ita!!!

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo mata daga idanunta ba tareda tayi magana ba jami'an suka tusata Station abisa yunqurinta na kisan kai..............

Har suka fita da ita bata dena kallon Abie ba lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka wanda ita kaÉ—ai tasan ma'anar abinta.

Thanks 4d love fans❤️

comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :24_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

_____✍️Har suka fita kuka takeyi sosai jikin Abie ya sanyi dajin sautin kukanta seda dukda hakan bayajin cewar ze iya ƙyaleta bisa yunƙurinta na kashe masa ɗa.

Tsaki Mom taja tana shirin magana sega maryam ta fito, ƙura mata iɗanu mom tayi a ranta tana tunanin inda tasan wannan fuskar Katse mata tunani maryam tayi ta hanyar cewa "Sannunku da zuwa Ranki ya daɗe nice wadda mukai magana dake ta waya ta faɗi hakan tana matse ƙwallar data zubo mata da gefan zanin Atamfar dake jikinta. Ajiyar zuciya mom itama hawaye na zubo mata tace "wani Asbiti aka kaimin ɗana ?
Chapter 19 · 0% Book details