← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 57

Sashe 34

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Janyota jikinsa Abie yayi tareda haɗeta da ƙirjinsa yanajin wani irin sonta da kuma tausayinsa na ratsa matsa kowani lungu da saƙo na zuciyar sa, wani irin nauyinta da kunyarta yakeji a yanzu musamman idan ya tuna irin ɗumbin halacciɓ da Aishar tayi masa a rayuwarsa, ta sadaukar da abubuwa dayawa na rayuwarta sabida shi ciki kuwa harda gudan jinin tilon ɗanta data haifa a duniya kuma duk tayi hakanne sabidashi a kasalance ya buɗe bakinsa dayayi masa wani irin mugun nauyi yace " Don girman Allah Aisha kiyafemin abinda na aikata a gareki pls karki bari zuciyarki ta samamin wani gurbi na ɓacin rai a cikinta don girman Allah!!!!!

Tureshi tayi daga jikinta tana kuka tace "gurbi dai kace ko Abdul toka sani tun ranar daka miƙani ga hukua zuciyata tayi maka tanadin wani babban masauki zallar tsanar.......... Da sauri Abie ya yunƙura cikin zafin nama ya haɗe bakinsa da nata guri ɗaya. Duk yanda Ummie taso ta ƙwace kanta abin gagararta yayi domin kuwa Abie be mata riƙon wasa ba, nan take dattijon ya shiga sarrafa matarsa cikin salo na ƙwarewa da bajinta a fagen iya soyayyah gamida tattali ya jefa uwar gidan tasa Ummie cikin duniyar gajimaren soyayyarsa ganida begensa. Ganin ze wuce gona da iri ne yasa ta shammaceshi ta fusge jikinta tayi hanyar ɗakinta, yunƙurawa yayi ya bita tana ƙoƙarin kulle ƙofar ya tura da ƙarfin tsiya ƙofar ta buɗe bayan ya shiga ne ya murzawa ƙofar key ya janyota jikinsa yana aikin rarrashi, ganin zata bashi wahala ne yasa ya shiga aikin rarrashin ta wata hanyar daban mesa zuciya ta zagwanye sabida shauƙin so gamida zallar ƙauna mara algus a cikinta, nan dai Abie ya sami nasarar sheƙe zuciyar ummie suka faɗa duniyar Ma'aurata.

Sosai Abie ya fahimci yayi kewar matar tasa tsahon lokaci wanda itama Ummien ta ɓangarenta kusan hakanne a haka dai al'amura suka wakana komai kuma ya tafi daidai kamar yanda yake fata. A haka dai Ummie ta daure ta kuma yafewa mijin nata don koda wasa bazata iya fushi ɗashi ba sam.

Ɓangaren Muzaffar kuwa kwance yake a ɓangarensa ko abinci ya kasa ci sabida tsabar fargabar dayake ciki komai bayajin daɗinsa don hkaa ma be nemi wani abinci ba sabida halinda yake ciki yafi gaban nan, wayarsa dake gefansa ce ta ɗauki ƙara harta katse be kalli inda wayar take ba, seda aka sake kira a karo na biyu sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauka tareda karawa a kunnensa batareda ya kalli screen ɗin ba, Muryar Hajar ya tsinkaya ta doki dodon kunnensa tace "Hi sweetheart. Shiru yayi sabida rashin sanin makamar abinda zece mata, kamar zata mai kuka tace" sweetheart are you there? Daƙyar ya Iya buɗe bakinsa cikeda ƙosawa da maganganunta yace "yeah WhatsApp? Lushe idanunta tayi da sauri sabida wani irin daɗi dataji tace "i just call you ne dama to ask you ko kana lfy, I feel like something is definitely wrong with you sweetheart, wllh koda fitar numfashinka ce ta sauya senaji a jikina..... Ta faɗi hakan idanunta na cikowa taf da kwallah.

Shiru yayi yana sauraron ta maganganunta nayi masa yawo a tsakiyar kansa, yau a karon farko yaji cewar hajar ta samu wani ɓangare na daban a cikin ransa dukda cewa hakan ba yana nufin yana sonta bane a'a kawai dai yaji ta bala'in burgeshi ne data fahimci irin halinda yake ciki a maganarsa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske yace "I'm fine Hajar is just a headache but Alhamdulillah I'm feeling better now. Zatayi magana kenan ya katseta ta hanyar cewa" i will call you tomorrow in the morning Insha'Allah. Ya katse wayar

Washe gari da safe kamar yanda ya mata alƙawari ya kirata suka ɗanyi magana sannan ya katse wajen 8am suka tafi Asbitin gabaɗayansu don Ayi musu gwajin ƙwayar halittar da alƙali ya bada Umarni (DNA TEST) tunda suka fita daga gidan ƙirjin muzaffar ke bugawa da ƙarfi hakama na Mom wadda tun a daren ranar bata rintsa ba sabida tashin hankali, daga ranar da Alƙali ya ɗage zaman shariyar zuwa yanzu duk Mom ta gama Ramewa ta fita haiyacinta kamar ba ita ba se dogon hanci wanda ya fito yay mata ƙwam a tsakiyar fuska. A haka suka isa cikin Babban General Hospital ɗin dake garin na Abuja don tabbatar da abinda sukazo neman.......

Thanks for d du'ah sisters Rabbi yabar zumunci👏

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page:34_*

*_WRITING BY:CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

____✍️Jiki babu ƙwari muzaffar ya sakko daga motar hakama Ummie wadda ta kasance ita kaɗaice a motar datake babu kowa ciki se drivern dake tuƙa motar, cikin sa'a kuwa idanunta dana muzaffar suka Sarƙe cikin na juna wanda tunda ya fara mallakar hankalinsa hakan bata taɓa faruwa a tsakaninsu ba, wani irin Amo da soyayyar uwar ce kwance a tsakiyar ƙwayar idanun Ummie wanda sam hakan ya gaza ɓoyuwa.

Take jikin muzaffar ya fara barazanar rawa tamkar ana kaɗa masa gangi, wani irin baƙon yanayi yakeji a cikn jikinsa me wahalar fassarawa a gareshi wanda sam ya gaza fuskantar ma'anar wannan yanayi dayake ciki ɗin, hannunsa mom ta damƙe cikin nasa hakanne ya taka mahimmiyar yawa wajen dawo dashi cikin nutsuwarsa.

A hka suka shiga cikin farfajiyar inda ake gudanar da DNA test ɗin jinin mom aka fara ɗauka sannan aka ɗauki na Ummie da kuma na muzaffar, kasancewar a kwai cigaba yanzu ba kamar da ba cikin Awa ɗaya akai komai aka gama har fitowar sakamakon duka, karɓa sukayi sannan suka fita zuwa motocinsu Ba tareda Ummie ta sake kallon indasu mom da Abie ɗin ke tsaye ba, a yanzu damuwarta ɗayace shine tasan halinda gudan jininta yake ciki wanda sam yaƙi yarda ya haɗa idanunsa da ita tun bayan fitowarsu daga lab ɗin.

Motocin suka buɗe kowa ya shiga sannan suka ɗun guma zuwa faɗar alƙali don yake hukuncin daya dace ba tareda an zalinci koɗaya daga cikinsu ba.

Bayan sun isa Inda za'a yanke hukuncin addu'a alƙali ya fara buɗewa da ita sananna ya bada umarni ga magatakardansa daya karɓo sakamakon Asibitin dake hannun security ɗin da aka haɗasu dashi don gudun ruɗani sannan ya kaimasa shi kuma ya miƙawa likitan dake zaune can daga gefan hannun daman Alƙalin donya tabbatar musu da abinda sakamakon yazo dashi, karɓa likitan yayi tareda warware takardan cikin nutsuwa Seda ya kama nazartar takardun sannan ya dubi alƙali cikeda nutsuwa yace " Sakamokon ƙwayar Halittar farko wanda ke ɗauke da sunan Aisha Muhammad Lamiɗo wanda binciken ƙwayar halitarta ya nuna cewar lallai tanada kamanceceniyar halittar jini da wasu nau'ika wanda yay daidai da ƙwayar halittar Muzaffar Abdulwahab Abdullah saɓanin yanda sakamakon Saratu Ahmadu Bello ya bayar sam babu kamanceceniyar halitta ta jini kota wani abu a tsakaninta da Muzaffar ɗin.

A zabure mom ta tashi lokaci guda kuma ta zube akan ƙafafunta ta fashe da wani irin kuka me masifar ban tausayi, daga yanda take kukan kaɗai zaka fahimci cewar tana cikin gagarumin bala'i mara misaltuwa. Sosai take wani irin kuka kamar zata shiɗe da wani irin hanzari kamar an mintsineta ta miƙe ta isa gaban Muzaffar ta zauna tana gunjin kuka tace "shikenan ya tabbata kaiɗin Ba ɗana bane Muzaffar?!! Mom ta jefo masa tambayar yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin kanta da kuma makomarta.

Toshe mata baki muzaffar yayi da sauri idanunsa a cike tab da ƙwalla shima yace "don't say that Mom. Kema mahaifiyata ce tunda kece kika raineni tun ina cikin tsuma kuma kikaci gaba da wahala dani tun daga yarinta na har zuwa girma na, duk wata wahala da uwa keji a lokacinda take rainon ɗanta kinsha dani mom haka kuma Allah shikaɗai ne masani aka lokutan dana dinga hanaki bacci sabida kukana tun ina jariri harna mallakin hankalina. A cikin jerin nauyin larurar rainon da duw wata uwa keyida ɗanta kinyi dani cikina ne kawai baki ɗauka ba tareda ciwon naƙudar haihuta, don haka wllh kema uwace a gareni mom don Allah karki sake bari bakinki ya furta cewar keɗin ba mahaifiyata bace!!!!!! Ya faɗa yana sakin wani irin marayan kuka me matiƙar taɓa zuciya.

Duk ilahirin jama'ar dake falon kuka suke na tausayin Rayukan guda biyu idan ka cire alƙali tareda muƙarrabansa, ita kanta Ummie kukan take tareda jin wani irin tausayin abokiyar zaman nata Saratu na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta.

Baba Hajara ma kukan takyi saɓanin maryamu da idanunta ke soye tanabin kowa da kallo.

Bayan lafawar komai ne alƙali ya tabbatar da hukunci cewar Muzaffar ɗan Aisha ne ba ɗan Saratu ba kamar yanda duniya ta ɗauka, a karon farko a rayiwar Fadilah taji cewar dama ace Muzaffar yayanta ne kamar yanda take kallonta a shekarun baya lallai a yau kam ta fahimci wani abou a tareda ɗan uwan nata, ba komai ta fahimta ba illa zallar ma'anarsa da kuma irin kulawar daya dinga bata don ganin ta zama mutuniyar kirki wadda zata sanya mahaifansu Alfahari kamar ƙanwarta zainab. Ta daɗe tana kokwanto akan wasu ɗabi'un nasa dayake nunawa ga duk wanda Allah ya haɗashi zama ɗashi, mutum ne shi very friendly and social Ashe duk wannan ɗabi'un nasa gado yayi daga mahaifiyarsa. Wani irin kuka ne ya kufcewa Fadilah tareda dana sanin abubuwan data dinga aikata masa don kawai taga ta daƙile tauraronsa a idon duniya

Gyaran murya Alƙali yayi tareda gyara glashin dake idanunsa ya kalli Ummie yace "a lokacin da kika kammala dafa Abincin da kika sauki Muzaffar dashi shin kin matsa daga kicin ɗin ko daidai da second ɗaya?

Da sauri Ummie ta kalleshi se kuma tayi shiru tareda kallo gefe guda alamar tanason ta samu damar tunawa cikin sauƙi, da sauri ta kalli Alƙali tace " Ban motsa naje ko ina ba seda a lokacin danagama kwashe abincin a cikin wormers nasa Maryamu ta kwashe taje ta jera kulolin akan daining ta faɗa tana kallon Maryamu wadda wani irin gumi ya fara yanko mata.......

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :35

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*
Chapter 34 · 0% Book details