← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 57

Sashe 27

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye Abincin tayi tareda matsowa gareta tace "Baba lfy kuwa nagani haka duk kin fita haiyacinki?

Hawayen da suka samu zarafin zubo mata Baba ta goge sannan ta kalli maryam tace "wai nikam meyake shirin faruwa a gidannan ne tsawon shekaru ina cikinsa bantaɓa cin karoda abinda ya ɗagamin hankali kamar wannan ba, wllh maryamu inajiyewa kaina tsoron abinda zeje yazo a cikin wannan iyalin danake kallo tamkar nawa!!

Yanzu Hajiya Saratu take sanar dani cewar wai kotu zata tafi da sassafen nan haka kawai sena samu kaina da rashin kwanciyar hankali duk a dalilin jin hakan.

Sakin baki maryam tayi tana kallon baba harta gama magana sannan tace "Baba karkice min bakuda labari akan abinda ya faru bayan zuwan ƙaramin megida ƙasar india? To idan kuwa har Hajiya bata sanar daku ba tabbas kirkinta da kuma sanin yakamatanta ya wuce duk yanda ake zatonsa.

idan har zan iya tinawa daidai Baba yau shekarata Talatin ina tareda Hajiya Aisha inai mata aiki tun tana ƙasar nan har Allah ya ɗagata daga nan muka koma India tare ban taba samunta da wani hali na rashin kirki ba kokuma kyautatawa ba komai ƙanƙantarsa, haka kuma duk wanda Allah ya haɗata zama dashi tanayin iya ƙoƙarin wajen kyautata masa koda kuwa maƙiyinta ne shi, Amma abin mamaki se gashi an kama Hajiya Aisha dumu2 da zubawa ƙaramin megida guba a cikin abincinsa da kuma abin shansa, ni kaina na girgiza a lokacin da abin ya faru harnake ganin kamar sharri akayi mata badan ina gurin abin ya faru ba wllh zance ɗora mata kawai akayi Baba.

Amma se gashi ta faɗa da bakinta cewar itace ta zuba masa guba don kawai ta kawo ƙarshen nunfashinsa wannan shine maƙasudin baiyanar mugun halinta a gaban kowa, nafi zargin cewar don kawai bata samu haihuwa da Alhaji bane shiyasa ta gammaci data kashe musu ɗa donta huce haushin wannan zafin. Maryam ta faɗa hawaye na zubo mata

Shiru Baba tayi tana kallonta haka kawai setaji sam zuciyarta ta kasa yarda da wannan laifin da ake zargin Hajiya Aisha dashi, wllh ko a gaban uban waye zata iya shedar ta kan cewar bazata taɓa iya aikata wannan gagarumin laifin ba koda kuwa ga dabba ne ba mutum ba, a hakan kuma wai muzaffar gaskiya itakam tana tantama akai koma menene zata zauna da Alhaji tasan se sanar da ita gaskiyar lamarin kuma tasan ze saurareta tunda uwa ya ɗauketa ba ƴar aikin gidansa ba.

Murmushi Baba Hajara tayi tana kallon maryam tace " wllh maryam kin ban mamaki da har kika bari zuciyarki ta iya faɗawa cikin zargin matar data shekara Talatin tana tallafawa Rayuwarki ta ɓangarori da dama batareda ta nuna gajiyawarta ba koda so ɗaya, nayi mamaki sosai da kika iya yarda da wannan zargin a lokacin da aka baiyanashi kunnuwanki sukajishi tabbas kinji kunya maryamu. Baba ta faɗi hakan tana bin maryam da wani irin kallo wanda yasa taji ta muzanta.

Wani irin sanyi jikin maryamu yayi sabida kalaman da baba ta faɗa to amma ya zatayi dole ne ta faɗi abinda idanunta suka gane mata a wannan rana, don Hajiya Aisha ta taimka mata a rayuwa hakan baya nufin zata iya zuba idanu ta kalleta a yayinda tayi yunƙurin kashe ɗan mijin kishiyarta Hajiya Saratu.

a haka hirar tasu ta tashi jikin kowa babu ƙwari, suna nan zaune Fadilah ta shigo ɗakin kunnenta ɗauke da waya ta kalli Baba tace "mom tace ki dafawa Muzaffar farfesun kifi da kuma abinci meɗan ruwa2, and then zaki iya haɗa masa da wani abin meɗan daɗi haka. Ta faɗa tana kallon Baban tana wani yatsin fuska

Murmushi Baba tayi sannan ta miƙe tace "zama be kamani ba miji nacan ciki babu komai bari inje na sama masa abu meɗan galmi-galmi ya samu ya tauna. Ta faɗa tana miƙewa da salati ɗauke a bakinta tayi kicin tahau hidimar girkawa muzaffar abinda zeci.

Bata wani ɗauki lokaci ba ta kallama komai se baza ƙamshi farfesun kifin yakeyi tamkar ba tsohuwace ta girkashi ba, sosai baba ta ƙware a fagen dafa abinci shiyasa tai fice a cikin gidan musamman a gurin Muzaffar indai ba ita ta girka abinci ba to wllh lami ne a gurinsa shiyasa yake sonta sosai.

Da yammaci wajen ƙarfe 5pm Muzaffar dake tafiya a duke sabida yanayin condition ɗin dayake ciki ya isa katafaren garden ɗinsu wanda aka ƙawata da duk wani abu na jin daɗin Rayuwa da ɗebe keywa ya zauna akan ɗaya daga cikin fararan kujerun da akayiwa ado da jajayen duwatsu masu matiƙar sheƙi da ɗaukar ido dake maƙotaka da katafaren swimming ɗin dake gurin, gefe kuma wasu fulawoyi ne masu fitarda wani irin nau'in ƙamshi wanda yafi kamada na musamman gamida sanya nutsuwar zuciya.

Miƙe dogayen ƙafafuwansa yayi kan kujerar tareda ɗora zara2 dogayen yatsunsa a saman ƙirjinsa tareda lumshe tsumammun idanunsa yay shiru yana nazari akan jarrabawar data sameshi a ƴan kwanakin nan, kokaɗan bayaso a sanadinsa Abie ya rabu da matar daya daɗe yana tareda ita morethen 35years don kawai tayi yunƙurin kasheshi, komadai menene a shekarun baya ta wahalta masa a lokacin dayake yaro da ƙarfin jikinta dakuma bakin aljihunta dole tunda ta aikata hakan tanada wani ɓoyyayan dalilinta dayasa ta aikata hakan. Wani siririn tsaki yaja a lokacin daya tuna maganar kotun dazasu sake shiga sati me zuwa wanda daga shine Hajiya Aisha zata fuskanci hukunci, gyara zaman kansa yayi bisa lallausan hannun kujerar dayake kai a haka daddaɗan yanayin dake gurin ya fara tasiri a jikin kowace gaɓa ta jikinsa lokaci guda hakan ya zama tamkar wata ilhama ne dake jan zuciyarsa zuwaga Fulani girl ɗinsa,

lumshe manyan idanunsa yayi tareda buɗesu lokaci guda akan korayen tsirran da suka ƙawata gurin ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda hakan yasa dimples ɗinsa both side suka lotsa a tare. A hankali can ƙasan maƙoshinsa yace "i miss you babe I miss everything about you my poor babe . Ya faɗa yana gyara zaman hannayensa dake zube saman ƙirjinsa.

wata danƙareriyar jeep ce ƙirar ford ta sulalo cikin harabar gidan Maroon colour wadda taji uban tinted da gani kasan duk wanda ya kasance mamallakin wannan mota to la shakka hannunsa ya cuɗi gadon bayansa, a nutse motar tai parking sannan ta ɓalle murfin motar ta sanyo ƙafarta waje wadda ke cikin wani haɗaɗɗen takalmi baƙi wuluk me bala'in tsini dashi se walwali yake sabida stones ɗin da akai masa ado dasu masu matiƙar haske da ɗaukar idanu,

Hajar ce the IG doughter ta sakko cikin wata shainaɗaniyar shiga ta ban mamaki tamkar wadda zata zaɓen sarauniyar kyau komai na jikinta baƙi ne hakanne ya bawa hasken fatarta damar baiyana a sarari, sosai doguwar rigar me fasalin fitet gown ta amshi jikinta tareda matse ta sosai tayanda duk wata halitta ta jikinta ta baiyana, a yangance take tafiya tana zuba yauƙi tana ƙoƙarin shiga falon gidan sukaci karoda Baba Hajara wadda ke ɗauke da babban flet a hannunta ta shiryawa ɗan gaban goshin nata Abinci zata kai masa, da fara'ar da bata kai zuciya ba Hajar tace "let me help you Old woman. Ba musu ta miƙa mata farantin tana kallonta bakinta a sake, murmushi ta sakin mata tace "yana ina na kai masa don nasan wannan abincin da ganinsa na mijin Hajar ne ko tsohuwa?

gyaÉ—a mata kai tayi tareda nuna mata hanyar garden batareda tayi magana ba don ita har ga Allah lamarin yarinyar nan yana masifar bata tsoro, "wannan wani irin lalacewar zamani ne ni Hajara?

Ko a jikin hajar sam bata damu da irin kallon da Tsohuwar kebinta dashi ba tai hanyar inda ta nuna mata tana wani juya mazaunai a haka ta isa garden ɗin ta sameshi idanunsa a lumshe, Ajiye flet ɗin tayi sannan ta sunkuya dabda fuskarsa tana wani bin fuskarsa da kallo kamar zata cinyeshi ɗanye, saukar numfashinta da nata ne suka haifar da sarƙewar numfashi a tsakaninsu take shauƙinso ya fara fuzgar Hajar ta fara ƙoƙarin kaiwa jajayen laɓɓansa farmaki hakan yasashi buɗe idanu da sauri ya saukesu bisa beauty face ɗinta.

jada baya tayi da sauri sabida wani bala'in kwarjini dayayi mata, kallon tsaf yayi mata kimanin 5second sannan ya miƙe yabar mata gurin yana riƙe da cikinsa, gabaɗaya ji yake dama ya kwasawa ƴar banza mari kozata fita daga sabgarsa wannan wani irin bala'i ne haka ?

shidai kam Allah ya jarabce shi da jarababbiyar yarinya wadda idan har beyi da gaske ba tsaf zata iya jefashi a masifa watarana.

Fashewa da kuka Hajar tayi a gurin sabida takaicin abinda yayi mata amma sabida naci irin nata haka ta miƙe tabi bayansa still tana kukan...

*_GYAMBU TARABA STATE_*

Tunda wannan mummunan al'amari ya faru da inna laure gabaɗaya duniya ta juya mata baya duk tabi ta rame ta koɗe kamar ba ita ba, yawan masifar nan ma duk ta dena kullum bata da aiki se kuka yau kimanin wata guda kenan da faruwar lamarin amma sam ta kasa mantawa da komai, duk sanda ta tuna ji take tamkar a lokacin abin ke faruwa da ita haƙika Fyaɗe babbar masiface me zaman kanta kuma duk wadda akayiwa shi an gama kashe mata rayuwa na har Abada!!!!

yauma kamar kullum Moddibo dake tsaye jikin ƙofar ɗakinta ya ɗaga labulan buhun yana kallonta kukan takeyi duk yanda yaso ya shareta kasaw yayi dole tasa ya shiga ɗakin ya zauna daga gefan katifar ciyarwar dake ɗakin ya dubeta ya dinga bata baki harya samu tayi shiru, sosai ya dinga zuba mata nasiha a kan yarda da ƙaddara da kuma haƙuri babu abinda take se kuka tareda nadamar bijirewa umarninsa datayi a baya, tabbas da bata biyewa son zuciyarta ba wata ƙila da yanzu ta tsira da sauran mutuncinta. Shidai moddibo miƙewa kawai yayi yabar mata ɗakin don tunda abin ya faru yaji gabaɗaya Laure ta gama sire masa, bayajin ze iya zaman Aure da ita kokaɗan sedai ze mata alfarma guda ɗaya ya cigaba da zama da ita batareda wani abu ya gifta a tsakaninsu ba, idan ta amince da hakan to shikenan zeci gabada zama da ita a haka tunda duk wanda ya rufa Asirin ƴar wani To Allah xe rufa nasa ..... Badan haka ba wllh da tabbas ya gama zama da Laure har Abadah

*_ABUJA_*
Chapter 27 · 0% Book details