← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 57

Sashe 46

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka kuwa akayi a gurguje Mamie ta gama kimtsawa ta fito, koda ta fito bata samu muzaffar da dady a falon ba , dan haka bata tsaya jiran komaiba ta nufi waje, tana fita ta hangi muzaffar a parking space yana tsaye a jikin wata Jibgegiyar Jib qirar ford, da alama fitowarta yake jira, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda milk colour ammata dinkin Jampa da wando, aikin dake jikin shaddar maroon color ne dan haka ya sanya hula maroon da ratsin milk a jiki ta kalmin qafarsa me danyasa ne shima maroon, se agogon Rolex din dake ÆŠaure a tsintsiyar hannunsa, sosai yayi Wani irin masifan kyau Kamar ba wanda ke cikin damuwa ba kayan sunyi matiqar amsar jikin sa, a hankali Ummie ta qarasa inda yake Tsaye kallo daya zakai mata kasan tana cikin damuwa mara musaltuwa, amma dik da haka damuwar bata hana futowar kyawun da Ummie n keda Shiva, S'a yanzu muzaffar ya qare mata kallo ya fahimci irin mugun kamar da suke da moddibon Banbancinsu kawai Ummie batakaishi hasken fata da kuma manyan idanu ba.

da sauri dan nata ya matso kusa da ita ya rungumeta Cikin sigan lallashi yace "don Allah Ummie ki rage damuwa indai baffa ne wllh Nasam ze fahimce ki, nasan shi yana da sauqin hali a Iya zaman danayi dashi , pls Ummie ki cire Yawan damuwar haka don Allah!

Batace komaiba se cire jikinta Datayi daga nasa , sannan tayi wani marayen murmushi me baiyana karayar zuciya da qarfin gwiwa tace "hka dai kace yaro amma ni nasan da wuya Baffa iya ya yayfemin abinda nayi masa.
Be sake cewa komaiba sbda fitowar Abie dasu Mom daya gani, a nitse suka qaraso gurin Suma jikinsu a saluɓe murmushi Ummie tayi musu tareda Faɗin " muntashi lfy ?

Momce ta amsa mata da fara'arta Hakama su Zaynab da Fadilah dake tsaye a bayan Abie,

Cikeda gimamawa muzaffar Yace "good morning mom. "morning son ka tashi lfy?

Da fara'a kwance a saman fuskarsa yace "im fine mom.

Kallon mom Abie yayi yace "Saratu zamu É—anyi wata doguwar tafiya pls zuwa anjima kisa Fadilah Takai baba Hajara Hospital lokacin ganin likitanta yayi. Cikeda damuwa mom tace "amma dai lfy dai ko Abie?

"no karki damu lfy lau wani uziri ne ya tasomin akan compayn da Aisha take leading a india to shine zamuje TARABA Akan Maganar.

"to Allah ubangiji ya tsare amma waye zeja motar?

A taqaice Abie yace "muzaffar. Da dauri Zaynab tace "Abie don Allah zan biku becouse ban taɓa ganin Yaya yayi driving me nisa kamar haka ba. Ba musu Abie ya amince mata sannan suka shiga mota mom da Fadilah na zuba musu addu'o'i

Comment
Nd
Share

Chubaɗo✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :44

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Not Edited 🙅‍♀️

___✍️Har bakin motar Mom tazo ta tsaya a daidai saitin inda muzaffar ke zaune bayansu Ummie da Abie sun shiga motar sun zauna, hannunta ta zura cikin motar tana shafa kan muzaffar zuwa wuyansa tace "Allah ya kiyaye muku hanyar son, kada ka manta da addu'a sannan kuma banda gudu mara amfani a titi. Murmushi ya sakin mara with so much love irin na ɗa da uwarsa yace "sure mom bt pls take good care of your self. Har ya fara qoqarin tada motan Se kuma ya kalli Fadilah dake tsaye tana kallonsu yace " MD ki fara shirin zuwa office daga yau sannan kuma don Allah karki manta da kai Baba Hajara Asbiti don I'm sure ta manta yau zata koma ganin Docter. Murmushi tayi irin wanda ke baiyana tsantsar farin cikin dake zuciyarta tace "thank you so much our humble br........

Sam Be jira cewarta ba ya tashi motar suka bar harabar gidan mom na ɗaga musu hannu tareda Fadilah suka kama hanyar TARABA STATE, cikin nutsuwa muzaffar ke tuka motar tamkar ba wannan hamshaƙin matashin da ƙarti ke tukawa a mota ba, lokaci-lokaci yakan ɗaga manyan idanunsa ya kalli Ummie ta mudubin dakw gaban motar gaba ɗaya duk ta zama wata iri sabida damuwa, wata siririyan ajiyan zuciya sauke a ransa yana ƙara jinjina buwaya da hikima irinta ubangiji, yanzu banda Allah waya isa yay wannan?

Ummie ta Rabu da Ahalinta tsahon kimanin shekaru 35 amma se gashi cikin ikon Allah ɓatansa ya zama sanadiyar haɗuwarta da Yayanta, tabbas komai na ubangiji yanada iyakansa shiyasa Allah ya jefo musu wannan al'amarin a matsayin zannan ƙaddararsu gabaɗaya.

******

Se wajen qarfe 10pm na dare sannan su moddibo suka iso cikin garin taraba sannan ya fara shirin kama hanyar Rugarsu kokaɗan be damuda duhun da garin yayi ba, jefa ƙafarsa kawai yakeyi tsabar sabida tsabar tanda zuciyarsa ke ke tafasa da baƙin ciki, gabaɗaya jiyake komai na dawo masa a ƙwaƙwalwarsa tamkar a lokacin abin ke faruwa, wasu zafaffan hawayene suka zubo masa yasa hannunsa ya share still be dena tafiya ba, a haka har ya iso cikin Rugar tasu tun kafin ya isa ga ƙofar gidansa jama'ar garin wasu suka dinga kallonsa kamar sun samu Tv kasancewar yanzu basa bacci da wuri sabida tsaron lfyarsu,

ko kaɗan be damu da irin kallon da suke binsa dashiba hasalima baƙin cikin dake ransa ma baze barshi harya damu da irin kallon ɗa suke masan ba, Direct ƙofar zagayayyen karan daya kewaye ɗakunansu dashi ya nufa ya shige gidan ba tareda ya iya furtawa jama'an dake biye da bayansa koda kalma guda ba, Bamanga ne yay ƙarfin juyawa da saurinsa ya nufi gidan malam Iro zuciyarsa fal farin ciki donya shaida masa cewan Amininsa moddibo fa Allah yayi masa dawowa cikin ƙoshin lfy.

Da sauri malam Iro ya miƙe tsaye lokaci guda kuma ya fara jerawa Allah kirari da sunayensa mafiya kyau, da murmushin me ɗauke da zallar farin ciki ya Raɓa ta gefan Bamanga ya fita da sauri zuwa gidan moddibo, ta cikin jama'ar dake tsaye ya raba ya kutsa kansa tsaye cikin gidan yana me ƙwallawa Moddibo kira with so much love and caring.

Tsayawa moddibo yay cak yana bin Malam Iro da Kallo batareda ya iya furta ko kalma guda ba, da sauri malam Iro ya matso gareshi ya Rungumese yana me shafa kwantaccen vaƙin gaskin kan Abokin nasa hawaye na zubo masa. Shima kansa moddibon kukan yake sabida murnan ganin abokin nasa da kuma taron jama'an dukda suka taru sabida shi. Cikin farin ciki malam iro yace "haqiqa Allah mai iko ne akan komai, haka kuma babu shakka wannan yaro yanada sufa irinta ƴan aljanna wato cika alqawari, kamar yanda yay mana alqawari akanka gashi kuwa ya cika cikin yardan ubangiji da kuma amincewansa, tabbas yayi namijin qoqari musman yanda yake ɗaukar nauyin duk wani ci da sha na iyalinka har zuwa yau da Allah ya nufeka da dawowa garemu, bama iyalinka kadai ba kaf wannan Rugar babu wanda be amfana da arziqin wannan yaro ba, haqiqa duk inda wannan yaro ya fito to tabbas iyayensa mutanan kirki ne kuma masu karamci.

Ƙura masa idanu Moddibo yayi babu ko ƙiftawa harya gama magana bece da malam iron Qala ba, haka kuma shima malm iron sam be damu da yanayin dake kan fuskar moddibon ba yafi danganta hakan da ƙaton cikin dake jikin Inna laure ne ya haifar da wannan sauyin a fuskar abokin nasa. Ajiyar zuciya malam iro ya saki a ransa yace "toya muka iya da lamarin qaddarar da Allah ya hukunta?

Se'a lokacin Moddibo ya lura da Laure dake zaune bisa ƙofar ɗakinsa ta miƙe ƙafafunta Ga uban Ciki ya fito yayi girma ta tsareshi da manyan idanunta da suka gama koɗewa sabida kukan daya zama abin yinta koda yaushe.

Wani irin bugawa qirjin Moddibo yayi lokacin dayay arba da wannan tulelen cikin dake jikin laure, kasa magana yayi illa wani irin ja da idanunsa sukayi lokaci guda kuma jijiyoyin kansa suka mimmiƙe kamar wanda ke shirin gabza dambe a filin daga, da ƙyar ya iya tattara kalmomin bakinsa ya firta "Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!!!!

Hakanne yay daidai da tsaiwar wata jibgegiyar baƙar mota jib ƙirar companyn Ford gabaɗayanta an lulluɓeta da baƙin tinted wanda ya mugun ƙarawa motar kyau da kwarjini........

Comment
Nd
Share

Thanks 4d love💕 yanzu kam insha Allah babu tsayawa harse mun gaba dukda cewan befi 3 pages or 4 mu gama book ɗin gabaɗaya ba, ammafa idan naga Ruwan comment ne zanyi hakan 😁

Sushmah ✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :45

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️Tun daga cikin motar yake kallon yanda jama'ar rugar suke gudu suna neman maɓoya wasu wasu kuma na tsaye ƙyam hannunsu riqe da sandinansu sunyi shirin kai duka, ganin da sukai babu wanda ya fito daga cikin motar ne yasa suka qara himma wajen damqe sandinan dake hannun nasu tamkar kace ket su zura a guje.

juyawa yayi a sanyaye yana kallonta da manyan idanunsa waÆ´anda suka faraa sauya launi tun bayan tasowarsu daga Abuja, cikin tattausar muryanshi me É—auke da amo a cikinta yace "kin tbbata nan shine garinku mulaikha?

Sunkuyar da Kanta tayi tana wasa da igiyar belt É—in motar dake daure a jikinta kamar wadda ya tilasta mata dole setayi maganar tace "Sure.

Kallonta yayi kimanin 4second sannan ya ɗauke fuskarsa ya maida kallonsa waje yana nazarin mutanan dake tsaye suna jiran fitowar mamallakin motar da wannan uban daren, hasken ƙwan gaban motar ne ya zame abin kallo wanda shi kuma ta ɓangaren Edyan hasken shine ya bashi damar qarewa mutanan dake gurin kallo harya karancin yanayinsu, ba zato ba tsammani ya bude murfin motar ya fito sanye yake da jeans and Tshirt wanda sukai masifan yi mishi kyau dukda cewar baya cikin yanayi me daɗi amma sam hakan be hana baiyanar kyansa da kuma kwarjinin dayake dashi ba, ganin hakan yasa itama ta buɗe murfin motar ta ɓangare ta ta fito idanunta nakan mutanan dake tsaye suna kallonsu tamkar sun samu Tv, nan take su Bamanga dukai kan Edyan da nufin su Rufeshi da duka cikin wani irin yanayi me fitar da Amo ta kallesu cikin tsawa tace "Shin mutumin dayay wa ɗiyarku alkhairi ya taimaketa a lokacin datake buqatar taimako shine kuke qoqarin illatawa?
Chapter 46 · 0% Book details