← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 57

Sashe 10

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka suka fito daga ɗakin har bakin ƙofar bukkar Inna Laure Muzaffar ya tsaya tareda durƙusawa ya kalleta yace "To Inna ni zan wuce gida ina roƙon Allah ya saka muku da alkhairi bisa taimakon da kukayi min a rayuwa ta, a zaman danayi dake idam har na taɓayi miki wani abu mara daɗi don Allah ki gafarce ni pls. Ya faɗa yayinda yake miƙewa daga ƙofar ɗakin ya juya

Taɓe baki Inna laure tayi sannan tace "o'o ɗannan bakamin komai ba, hasalima ni daɗin tafiyar taka nakeji har Raina sabida bansan tsiyar datake tareda kai ba, nida zaka temakeni ma wllh idan ka futa daga Rugar nan ka roƙi Allah mantar dakai hanyar shigowa garin nan gaba ɗaya.

Murmushi kawai yayi sannan yace "insha Allah zanyi Addu'ar amma sedai nace Allah ya mantar dani ƙofar ɗakinki badai ta Rugar nan gabaɗaya ba. Be jira cewarta ba yayi gaba abinsa

Har cikin zuciyar Moddibo yaji tafiyar yaron sabida yanda yakejinsa a Ransa, Babur ɗin malam Iro moddibo ya karɓo Aro sannna ya ɗauki muzaffar a bayan Mashin ɗin suka Tafi donya kaishi tashar dake cikin Gari.

Har tasha yakaishi sannan ya biya masa kuɗin mota ya juya ze tafi, da sauri muzaffar ya biyoshi ya Ringumeshi tareda kama Hannunsa yace "Banida isassun kalmomin dazanyi godiya a gareka Baba amma ina roƙon Allah ya gina maka gida a gidan Aljanna!!

Zare jikinsa Moddibo yayi daga nasa sannan ya juya da Sauri yana hawaye batareda ya juyo ba ya kunna mashin É—in yabar Gurin muzaffar na kallonsa.

Sosai yaji shima zuciyarsa tayi mugun Rauni amma kuma bashida wani zaɓi dole ne ya koma gida kodan sabida iyayensa da sauran ƴan Uwansa. Yana nan tsaye har motar ta cika suka kama hanyar Abuja zuciyarsa a cike Fal da kewar Fulanin Dajin.......

*_Naga ƙaunar ku da Soyayyarku akan wannan littafi gamida Addu'o'in alkhairinku gareni, thank you all for the Support and Comment ubangiji yabar zumunci_*

Comment
And
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :15_*

_Sisters wllh biki mukeyi shiyasa kuka jini Shiru amma dazaran mun gama to har sekun gaji dani Aradu.🥰_

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️Tunda ya shiga motar abu guda biyu ne keyi masa yawo a saman zuciyarsa, na farko shine ƙwallar daya gani a kwance cikin ƙwayar idon Modɗibo wanda yakeda tabbacin cewar ƙaunar dayakeyi masa ce sular faruwar hakan, abu na biyu kuma shine sabon daya bari har ya shiga tsakaninsa da ƙaramar yarinyar da ko'a mafarki be taɓa zaton ze iya samamata gurbi a cikin zuciyarsa ba domin kuwa shi'a tsarinsa babu maganar Soyayya a cikinsa, shin yanzu a wani hali zata kasance bayan tafiyarsa?

Ajiyar zuciya ya sauke a karo mara adadi basu suka iso garin Abuja ba se ƙarfe 8pm na dare, kuɗin da modɗibo ya bashi ya kalla sannan ya tare Taxi yace "Maitama zaka kaini. Daga haka ya buɗe motar ya shiga ciki suka ɗauki hanyar Maitama, har Suka isa cikin Maitama Muzaffar na tunanin makomar Yanda Rabe Zata kasance a sanadin tafiyarsa. Me taxi ɗine ya katseshi ta hanyar cewa "malam mun iso maitama fa a ina zan ajiye ka?

Shiru yayi kimanin ƴan sakanni sannan ya faɗa mishi inda ze kaishi, a bakin ƙofar makeken get ɗin gidansu me motar ya faka sannan Muzaffar ya fito tareda miƙa masa kuɗin motar, yana karɓa yaja motar yayi gaba abinshi a ransa yana mamakin ganganci irin na wannan Bafulatani

A nitse yake takawa harya kai jikin Get É—in tareda Sanya babban yatsansa na hannun damansa a jikin tompprint É—in dake Jikin Get É—in take get É—in ya buÉ—e yana shiga gidan ya juyo da sauri kafin Get É—in ya rufe kansa yace "Nande feri miwarti insha Allah Rabi'atou!! MimeÉ—ataye yejutugo beko awanniyam dole watarana Zan dawo gareki Fulani girl. Ya faÉ—i hakan yayinda get É—in ke Rufewa

A nitse yake takawa harya isa tsakiyar farfajiyar gidan tun kafin ya sake ɗaga ƙafarsa guards ɗin dake tsaron gidan ta ciki suka kewayeshi lokaci gududa kuma suka wurga masa tamyar shi waye bakinsu a haɗe lokaci guda?

Tsura musu idanu kawai yayi lokaci guda kuma takaicinsu ya cikashi amma still ya kasa ce musu komai Kuma bebar kallonsu ba. Kayan jikinsa ya kalla lokaci guda kuma ya maida hannunsa kan lallausar Sumarsa data fara fitowa sosai kuma tayi yawa sabida Askin da Moddibo yayi masa a lokacin daya tsince shi sakamakon saran dake kansa a lokacin yayi tareda datse lips ɗinsa da Fararen haƙoransa yace "who the hell are you to stop me and asking who I'm? Muzaffar ya faɗi hakan yayinda yake gyara tsaiwarsa irin wadda ya sabayi yayinda yaci nasara a kan dukkan abinda yasa a gabansa.

Take idanunsu ya firfito wajen yayinda kunnuwansu sukai Arba da Amon muryar muzaffar me cikeda tsantsar izza gamida yarda dakai zubewa sukai a ƙasa gabaɗayansu suna masu ban haƙuri a gareshi tareda murnan ganinsa, kallon tsaf yayi musu sannan ya daɗa gyara tsaiwarsa yace "duk kanku ku miƙe inada saƙon baku, banaso kowa yasan ina cikin gidannan har zuwa lokacinda zan baina kaina a radin kaina. Yana gama faɗar hakan ya juya ya fara tafiya

Da sauri ɗaya daga cikin Guards me Suna Selomon yace "but why sir Amma kullumfa se babban megida ya shiga damuwa wasu lokutan ma har ya zubarda hawayensa duk a sanadin ɓacrwarka, amma kana ganin hakan baze zama illa ga lafiyarsa ba?

Tsayawa cak yayi batareda ya juyo ba yace "abida na baɗa kenan Selomon kuma duk wanda ya saɓawa ƙa'idata tabbas ku sani to a bakin akinsa. Ya faɗa yana barin kurin Direct Side ɗinsa ya nufa tareda murɗa haɗaɗɗen Handile ɗin dake jikin ƙofar wanda yafi kamada na musamman sannan ya shiga falon

Masha Allah haƙiƙa wannan falo ya gama ƙawatuwa da dukkan ababan ƙyaleƙyale na Duniya, dukda cewar babu wani tarkace a falon amma komai na ciki Expensive abu ne hular dake rataye a bayansa ya cire tareda hurgata a saman manyan Royal chairs ɗin dake falon masu launin Golden da yarfan Ruwan Zinare a jikinsu, maida kallonsa yayi kan makekiyar flaczima ɗin dake falon wanda take very slim babu wani tudu a tareda ita, ɗan tsaki yaja kaɗan sannan ya wuce Bedroom ɗinsa

Nan ma faɗar irin haɗuwar ɗakin wllh ɓata lokaci ne a gareni tareda ku masu karatu, amma hasashen haɗuwar ɗakin C.E.O of xafar ɗin ya rage gareku readers😂 kusan abinku da matashi me jini a jika kuma ɗan ƙwalisa me citta a hannu dole ne komai nasa ya zama Very Expensive

Toilet ya nufa Direct ya buɗe shima nan ɗin dai ba'a magana domin kuwa babban guri ne me zaman kansa wanda ya haɗa da kayan ƙawa na ban mamaki, babban jakuzi ne daga can gefe se kuma wani falelen abu daga gefe wanda yafi kamada bahon tare ruwa amma sedai shi yanada girma sosai don mutum ze iya shigewa cikinsa complite

Gefansa kuma wata slim drower ce wadda aka zuba towels farare masu azabar kyau gamida burgewa, Direct kusa da wannan abun me kamada bahon wankan ya nufa sannan ya kara hannunsa daga gefan wani Rami dake jikin abin take ruwa ya fara ɓulɓulowa daga cikin abin, kafin kace me tuni Ruwan ya gama taruwa kuma still ruwan da zafinsa daidai yin wankan mutum zare rigar dake jikinsa yayi tareda dogon wandon saƙin take wurɗaɗɗen jikinsa gamida faffaɗan ƙirjinsa suka baiyana, se'a lokacin na fahimci cewar lallai matashin ma'abocin cikar zati ne gamida haiba duba da irin yanda zanen 6part ɗin dake cikinsa suka baiyana a fili, cikin bahon ya shiga ya zauna tareda lumshe manyan idanunsa sabida yamda zafin Ruwan yake ratsa duk wata gaba dake jikinsa, seda ya shafe kusan 30mnt a haka sannan ya fito tareda danna wani buttum dake jikin abin take ruwan ya tsiyaye sannan ya shiga jakuxi ɗin yayi wanka ya ɗauro wani babban towel a jikinsa tareda ratayo wani ƙaramin towel ɗin a kansa

Goge gashin kansa yayi da ƙaramin towel ɗin dake wuyansa sannan ya buɗe Makekiyar closets ɗinshi dake manne a jikin bangon ɗakin, ɓangaren ƙananan kayanshinya bude take Sportwears ɗin suka baiyana tareda Sleeping dress ɗinshi wanda gabaɗayansu suka kasance mallakin Companyn Armany.

Wata lallausar riga blue ya jawo da wandonta ya sanya a jikinsa sannan ya tada Sallar magrib dake kansa sannan yayi isha gaminda shafa'i da wutiri, seda ya gama tasbihinsa sannan ya miƙe a matiƙar gajiye yayiwa kansa masuki a kan makeken Royaƙ bed ɗinsa wanda yayiwa ɗakin ƙawanya, yana kwanciya wani gajiyayyen bacci ya ɗaukeshi.

Ɓangaren Abie kuwa sosai suka sake dagewa da Addu'o'i akan ɓatan ɗan nasu, Momy ce zaune bisa Daining ta zubawa abincin da zainab ta zuba mata idanu batareda takai koda cokali ɗaya bakinta ba, hakama Abie wanda ke gefan momyn cikeda damuwa Zainab ta kalli iyayen nata tace "Haba Abie don Allah ya kamata kuyi haƙuri da jarrabawar da Allah ya aiko mana, idan har ku iyayenmu kunasa damuwa a zukatanku irin haka mukuma idan wani abun ya sameku a sanadin hakan ya kuke tsammanin zamuyi da Rayuwar mu?

Ajiyar zuciya Abie ya sauke lokaci guda kuma ƙwalla ta samu gurɓi a cikin ƙwayar idonsa yace "kiyi haƙuri daughter ni kaina abin ne yakeso yafi ƙarfina kaina duk ya kulle duk a sanadin ɓatan yaron nan taya kike zaton zamu iya kwantar da hankalin mu ?

"Amma Abie ai....

Ƙarar wayar Abie ce data gauraye falon gaba ɗaya yasa Zainab tayi shiru tana kallon Abie ɗin Ƙurawa wayar idanu yayi yana kallon screen ɗin tareda sunan wanda ke kiran nashi, abokin kasuwancinsu ne wanda zasu zauna dasu gobe da safe akan harkar kasuwanci kuma ya tabbata cewar idan mutumin yasan Muzaffar baya nan tabbas zecire hannun jarinsa dake Companynsu.

Fadilah dake ta bugar abincinta ta É—ago ta kalli Abie tace "ka É—aga wayar hankalinka kwance kuyi magana dashi I'm sure of that idan har yayi magana dani baze sake ambaton Muzaffar ba sedai Fadilah MD ZAFAR ENTERPRISES.
Chapter 10 · 0% Book details