← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 57

Sashe 36

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sedai zan mutu ne da abu guda ɗaya wanda kemin ciwo a Raina Laure, wllh ina matiƙar jin kunyar kaina dana ɗiyata tunda har na iya turata da hannuna kuma ta tafi tabarni ba tareda ta juyo koda so ɗaya ba, ina me jiyewa kaina tsoron irin halinda zata samu kanta a ciki na kaɗaici da kuma sharrin Zaman........ Kuka ne yaci ƙarfinsa haryasa maganar ta katse ba tareda ya shiryawa hakan ba, wani irin tari ne ya taso masa me matiƙar wahalar fita wannna dalilin ne ya haifar masa da sarƙewar numfashi al'amarin daya ƙara gigita Inna Laure kenan . Da ƙyar tarin ya tsaya sannan moddibo yaci gabada cewa " don Allah zan roƙeki wata alfarma guda ɗaya a iya zaman da mukayi nidake Laure, koda Ace bayan na mutum Allah ze haɗaki Da Rabi'atou ki gaya mata cewar ina matiƙar ƙaunarta sannan kuma ta riƙe alƙawarin data ɗaukar min!!!!

Ɗagoshi tayi da mugun sauri zuciyarta na bugawa da wani irin ƙarfi, hawaye ne suka shiga zubo mata tamkar an kunna fanfo sabida tsabar tausayin Moddibon bakinta na Rawa tace "don Allah ka dena faɗar haka malam ai cuta ba mutuwa bace kuma insha Allah duk inda Rabe take tana cikin hannu na gari da izinin Allah.

Murmushin ƙarfin halli ya sakar mata zeyi magana kenan harshen yaƙi bashi dama, Idanunsa ne suka fara wani irin ƙafewa lokaci ɗaya kuma numfashinsa ya fara sarƙewa cikin abonda befi daƙiƙa biyu ba jikinsa ya saki idanunsa kuma suka wani irin juye...............😭

Thanks 4d love guys i really appreciate it 🥰

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :36

*_Qaddara macece mara tabbas takan iya canzawa a kowani lokaci, kamar yanda Qaddararso kan afkawa zukata batareda zato ko tsammani ba😊 ._*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

NOT EDITED🙅‍♀️

____✍️Wai irin ihu inna laure ta kurma tareda cakumoshi zuwa jikinta lokaci guda kuma taci gaba da buga ƙirjinsa da hannunta tana wani irin kuka tamkar ranta zebar jikinta tace "kayiwa girman Allah kada kayiwa Rayuwarmu haka moddibo, ka tuna irin girman alƙawarin dake tsakanin ka da ɗiyarka kafin zannan ƙaddara ya samu nasarar giftawa a tsakanin ku, a yanzu ni kaina idan ka tafi ka barni a irin wannan halin dana samu kaina a ciki wllh banajin zan iya jurar hakan koda kuwa na kwatankwacin ƙwayar zarra ne, ko kaɗan bazanso muyi Rabuwa irin wannan dakai ba ba tareda ka yafemin ba!!!!! Hannunta tasa ta share hawayen daya zubo mata sannan taci gaba da cewa " na kasance tamkar wata shaiɗaniyar mata a gareka Moddibo, zuciyata da tunani na basu taɓa zaiyanomin amfaninka a rayuwata ba seyau dakake shirin barina a lokacin danafi kowa buƙatarka, kasha faɗamin cewar idan har ban canza halayena da ɗabi'una ba tabbas a kwai Ranar Nadama wadda zatazo min nan bada jimawa ba, naso Ace wannan ranar batazomin a haka ba seda na wanke laifina a gareka tareda nuna maka duk wata kulawa da Mace ta gari ya dace ta bawa mijin da Allah ya azutata dashi amma kash se gashi mutuwa ta gifta a tsakanin mu damu dakai batareda ta bamu damar yin bankwana ba. Ta faɗi hakan tana ƙara rushewa da wani irin kuka wanda yafi na farko

ABUJA NIGERIA

Al'amarin gidan Cp (commissioner of police) Kuwa sosai Rayuwar gidan take tafiya daidai batareda sun bari Cp yasan da batun Bafulatanar dajin dake cikin gidansa a zaune ba kasancewar be fiye shiga part ɗin Mom ba itace ke zuwa nasa, sosai suke nuna mata kulawa tamkar sun daɗe da saninta kullum Edyan ke kaita makaranta tareda gurds ɗinsa sannan ya wuce Office, kullum se sunyi daru da ita sannan zata yarda ta sauka daga motar idan ya matsa mata seda ta riƙe hannunsa taita kuka, sosai yakejin kukanta a ransa tamkar ana watsa masa ruwan narkakkiyar Dalma rage tsahonsa yayi daidai da nata tareda gyara mata zaman hular dake kanta wadda ta baiyana kwantaccen gashin dake zagaye da kyakkyawar fuskarta yace "look mulaikha kukan ya isa haka nan baran daɗe ba zanzo ɗaukanki yau kinji?

Maƙemai kafaɗa tayi tana turo baki still hawaye na fita daga cikin fararen idanunta masu masifar ɗaukar hankali, lumshe idon tayi ta wani buɗesu lokaci guda akan handsome face ɗinsa ba tareda tace komai ba, jan hancinta yayi tareda kai bakinsa saitin goshinta yay kissing forehead lumshe idanunta tayi da sauri lokaci guda kuma taja da baya tana ƙwalalo masa ido hardasa hannu a baki alamar mamaki.

Dari yayi mata tareda ɗaga mata hannu ya shige mota sukabar harabar makarantar batareda ya juyo ba, still tayi tana kallon motocin har suka fice daga school ɗin idonta na kallon get ɗin ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya a hankali tana tafiya hannunta na dama kuma riƙe da goshinta inda Edyan yay kissing a haka harta kai class ɗinsu tana aikin tunanin abinda Kaɗo Edyan ɗin yayi mata.

Wannan shine abinda ya wakana a tsakanin Edyan da Mulaikha (the fulani girl Rabe)

*****

Zaune mom take a falonta idanunta na kallon sama Zainab ta shigo bayanta ɗauke da jakarta ta goyo baƙa wuluk da ita wadda tayi mata masifar kyau, duk sallamar datakeyi Mom bata sani ba seda ta matso kusa da ita ta zauna sannan ta ɗago ta kalleta tareda ƙaƙalo murmushin dole tace " welcome home my sweetie Qurrah. Ajiyar zuciya Zainab ta sauke fuskarta ɗauke da damuwa tace "mom meyake damunki haka naga duk kinyi wani iri? Zainab ta ƙare maganar kamar zatayi kuka.

Dafata mom tayi jikinta a mace tace "karki damu Qurrah ba wani abu bane kawai dai banajin daɗi ne, maza tashi kije kiyi wanka kicanza kaya kici abinci ki huta inyaso mayi maganar ok? Ɗaga mata kai zainab tayi tareda faɗin ok . Ta faɗa yayinda take miƙewa zata bar falon

Tsayawa tayi chak se kuma ta juyo tana murmushi tace "mom banga bro ba but I'm sure he's not in the office right now so were is he wllh I want to see him nayi missin É—inshi badly. Wani irin kuka ne ya tasowa mom amma kuma seta danne tace "yana part É—in Aisha . Yarda jakar bayanta Zainab tayi ta dawo kusa da mom tace "mom kina nufin Ummie ta dawo ? ÆŠaga mata kai kawai mom tayi ba tareda tayi magana ba. Da wani irin mugun gudu zainab ta tashi ta fice daga falon tana Dariya bata dire ko ina ba se part É—in Ummie.

Zaune take kan ɗaya daga cikin maka-makan Kujerun alfarmar dake falon Inda kan Muzaffar ke kwance bisa kafaɗunta suna ɗan taɓa hira, wani irin daɗi yakeji gamida shauƙin mahaifiya na fuzgarsa gyara zaman kansa yayi sosai a kafaɗun Ummien ta yanda zejin daɗin kwanciyar yace "Ummie i want to tell you something akan wani abu dana aikata a Rayuwata, ajiyar zuciya yaɗan sauke sannan yaci gaba da cewa, last 6 months ago na haɗu da wani mutumi a can jihar taraba Ummie a lokacin da bana haiyacina. Ummie ya taimakeni a Rayuwa sannan ya sadaukar da abubuwa dayawa sabida ni nan dai ya kwashe komai ya gayawa Ummie abida ya faru ciki kuwa harda labarin Rabe.

Kallon Ummien yayi kamar ze sakin mata kuka yace " i feel something about her musamman idan muna tareda ita, a wasu lokutan ma har nakanji zuciyata na zafi idan na ganta da wani muddin ba mahaifinta bane I don't know ko menene. Shafa kansa Ummie tayi tana murmushi tace " so tari a rayuwa bama sani ma'anar waƴanda suke taredamu har semunyi nisa dasu sannan muke sanin ma'anarsu da kuma amfaninsu a taredamu, yanayin da kakeji akan yarinyar sam ba baƙo bane a idon duniya amma kuma a tareda kai hakan tamkar wani sabon al'amari ne me zaman kansa. Lallai ziciyarka ta faɗa cikin wani babban al'amari me zaman kansa wanda zan baka tabbacin cewar ba komai bane illa soyayya kuma me ƙarfin gaske ba ƙarama ba.

Miƙewa yayi da sauri daga jikinta yana kallon Ummien yace " love dai?? A hakan kuma ni Ummie?

Murmushi ta sakin masa tace " sosai kuwa tabbas ka faɗa a soyayya me ƙarfin gaske koda kuwa Ace bakasan hakan ba, ita soyayya kamar iska haka take tana tasowa ne a lokutan da bamuyi zato ko tsammani ba don haka ina me baka shawarin cewa lallai ka gaggauta shiryawa don ka cika alƙawarin da Ka ɗaukarwa bayin Allahn nan, sannan abu mafi mahimmanci shine koda ba sabida soyayyarka da ƴarsu ba lallai ya kamata ka ziyarcesu kodan kaga halinda suke ciki.

ɗaga kansa yayi alamar gamsuwa da maganar Ummien sannan ya miƙe yace "ummie barinje masallaci kafin Abie ya dawo. Turo ƙofar falon akai zainab ce ta shigo da gudu sabida zumuɗi ko sallama batayi ba ta faɗa jikin Ummie tana dariyar farin cikin ganinta, baki Muzaffar ya saki yana kallonta yace "ke yau kuma ni kika share ko?

dariya tayi tana kallonsa tace "uhm naga Ummie ai bazan kulaka yau ba sabida inason nasha miyar gyaɗa. Dariya suka saki gabaɗayansu sannan ya fice daga falon. Tunanin maganar Da ummie ta faɗa masa akan Rabe yana yawo a saman zuciyarsa da kuma ƙwaƙwalwarsa a haka yayi sallar la'asar ɗin zuciyarsa duk a dagule, koda ya dawo Masallacin ma part ɗin mom ya nufa dondai kawai ya samu ta rage damuwa akan abinda ke damunta na rashinsa a matsayin ɗa, yana shiga ta miƙe da sauri ta nufeshi tareda shafa gefan fuskarsa tace "kacin abinci dai ko?. Hawayen dake maƙale a cikin ƙwayar idanunta ne suka samu nasarar zubowa, hannayenta ya kama ya damƙe cikin nasa cikeda damuwa yace "don girman Allah mom kiɗena kuka wllh kukanki yana masifar ɗaga min hankali Pls.

Janta yayi ya zaunar da ita a saman kujera sannan yay murmushi yace "har yanzu ke uwatace kuma babu wanda ya isa ya canza hakan koda kuwa Ummie ce da kanta, so pls ki kwantar da hankalinki don Allah. "Yauwa yaya gara da kazo da kanka tun ɗazu nake fama da mom taci abinci amma taƙi se faman kuka takeyi. Fadilah ta faɗi hakan yayinda take sakkowa daga saman stars
Chapter 36 · 0% Book details