← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 57

Sashe 47

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa sukai cak suna kallonsa ba tareda sun juyo sun dubeta ba, shikuwa Edyan yana tsaya bisa digadigansan s ayana kallonsu ba tareda ya motsa ba, qraasowa tayi gurin tana kallonsu ido cikin ido suma É—in kallonta suke irin kallon nan dayafi kamada na rashin sanayya.

Se'a lokacin ta tuna da canjin da rayuwarta ta samu a Sanadin Partner É—inta Edyan kamar yanda take kiransa tun bayan haÉ—uwarta dashi. Ba lallau bane mutanan dake gurin su ganeta ba don haka da sauri ta isa gabansa ta tsaya shi kuma Edyan din na tsaye qyam a bayanta be motsa ba.

Bamanga ne ya ɗaga sandan hannunsa take ya sauke matashi a saman goshinta kafin kace me tuni gurin ya fashe ya fara fitarda jini, a gigice tayi baya zata faɗi sabida wani jirin azaba daya ɗibeta cin zafin nama bamanga ya sake ɗaga sandar da nufin ya saukewa Edyan Rabe dake qarin faɗuwa ta cikin wani irin mugun zafin nama da bata taɓa zaton tanadashi ba tayi wuf ta sake shiga gaban Edyan ɗin take sandar ta sake sauka bisa gefan fuskarta. Cikin ƴar daƙiƙar da bazata wuce 2 ba ta faɗi ƙasa sumammiya.

Ganin jinin dake fita ta bakinta da kuma goshinta ne ya mugun fusata Edyan dake tsugune bisa kanta yana ƙwala mata kira cikin wani irin karaji me cikeda nuna tashin hankali, da ƙarfi yake kiran sunanta tamkar wani zararre ya miƙe kamar mayunwacin zaki yay kan Bamanga da duka ƙarfinsa ya shiga gabza masa naushi yana faɗin "how dare you dazaka sa sanda irin wannan ka daki Mulaikha ta?

Bakajin tashin komai se ihun Bamanga wanda ya cika gurin sabida duhun daya farayi, ihunsa ne ya jawo hankalin Moddibo da malam iro wanda ke tsaye a cikin gidan da sauri suka fito don ganin abinda ke faruwa, kasancewar hasken fitilar gaban motar a kunne yake shine ya basu damar ganin abinda ke faruwa a tsakanin Bamanga da Baquwar fuskar dake gabzar bamangan kamar Allah ya aikoshi.

Da sauri suka nufeshi da nufin su ƙwaci Bamangan a hannun Edyan amma sam hakan ya farkara, daga can gefe ya tsinkayi muryar Rabe wadda ke Rawa sabida Azabar bugun datasha a hannun bamanga tace " plz partner stop beating him he's my.....uhm.. He's mmmmm.... My brother!!!!!

Cak Edyan ya tsaya da dukan kamar wanda aka matsawa remote, a hankali ta miqe tsaye dukda jirin dake ɗaukarta kamar ance ta juya idanunta suka sauka akan Mahaifinta Moddibo wanda ke ƙoƙarin ɗaga Bamanga Wanda jini ke fita ta bakinsa, da wani irin gudu Rabe ta kwasa ta nufi moddibo tana wani irin kuka tana kiran "Babana wayyo Allah babana is that you!!!!! Faɗawa tayi jikinsa ta saki wani marayan kuka wanda yasa gabaɗaya mutanan gurin suka dare suna bita da kallo.

Da qyar ta iya tsagaita kukan ta É—ago tana kallonsa cikin ido cikeda shauqin si irin na Æ´a da ubanta tace "haqiqa Babba ka cika alqawarinka gareni sedai ni ban cika maka wanda nayi maka ba babana! Ko kaÉ—an A tsakanina dakai tasirin qaddarar yayi kaÉ—an ya zama silar rabuwata dak........... Wani irin kuka ne ya sake qwace mata a karo na biyu.

GabaÉ—aya Moddibo kasa motsin kirki yayi illa wasu zafafan hawaye dake masa zarya a saman kumatunsa, qura mata idanu yayi sannan ya buÉ—e bakinsa dayayi masa nauyi yace "so tari a Rayuwa wasu al'amuran sunfi qarfi rai da gangar jiki ya iya musalta É—acinsa, shiyasa tasirin zanan qaddara yasha banban da komai a rayuwar É—an Adam, haqiqa Allah mabuwayin sarki ne kuma mai jida ganine shi shiyasa ya taqaita min zafin jarrabar rayuwar danake ciki ba tareda nasha wahala mai tsanani wajen nemanki ba!!!!

Duk mutanan dake gurin seda suka tausaya musu ciki kuwa harda Edyan wanda ke tsaye yana fitarda numfashi, ganin abin nasu bana qare bane yasa ya koma mota ya buɗe wata qaramar box dake sit ɗin baya ya ɗakko wata madaidaiciyar box ya dawo inda Rabe da moddibo ke rungume da juna suna aikin kuka ya kama hannunta ba tareda ya lura da irin kallonda mutanan gurin suke masa ba ya zaunar da ita a ƙasa dirshen sannnan ya buɗe box ɗin ya fito da soft cotton with hydrogen ya fara goge mata ciwon dake goshinta yana fitarda jini, seda ya gama tsaf sannan yasa mata flasta ya rufe gurin yana kallon tsakiyar kwayar idanunta with so much love and emotion. Sauke idanunsa yayi a hankali ya mayar kan box ɗin tareda ɗakko wani ƙaramin magani wanda aka rubuta pain reliver a jiki ya ɓallo ya miƙa mata yace "let bring the water for you. Ya faɗa yana miqewa ya koma mota can se gashida bottle water ya miqa mata ta karɓa tasha maganin tana wani yatsina fuska.

GabaÉ—aya mutanna dake gurin kowa kallonsu yakeyi inda wasu daga ciki suke mamakin rashin kunyar da Edyan, musamman yanda sukaga yana kama mata hannu, basu ida shiga mamaki ba seda sukaga ya Kama hannunta yana qoqarin miqar da ita tsaye.

GabaÉ—ayansu zaro idanu sukai suna binta da wani irin kallo se'a lokacin ta lura da abinda ta aikata É—in ba shiri ta fusge hannunta daga ruqon da Edyan É—in ya mata ta koma kuda moddibo ta tsaya se faman raba idanu take kamar wadda tayiwa sarki qarya. A haka taron ya watse kowa da abinda yake saqawa a gameda Edyan da Rabe.

Sosai moddibo ya tarbi Edyan kamar ze goyashi sabida yanda Raben ta gaya masa irin alkhairin dayayi mata a rayuwarta tun bayan haɗuwarta dashi, hakan ba qaramin dadi yayiwa modɗibo ba harya kasa ɓoye hakan a fili dukda irin tashin hankalin da zuciyarsa take ciki a gameda halinda ya dawo ya samu Laure a ciki, kasancewar dare yayi sosai ne yasa Moddibo ya raka Rabe bukkarta ya kunna mata fitilar lagwanin dake ɗakin sannan ya zaunar da ita bisa katifar ciyawar dake ɗakin ya dubeta yace "wanene wannan matashin da kuka taho taredashi?

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyin gaske a hankali ta maida kallonta qasa ta shiga korawa mahaifin nata bayani akan Edris da kuma irin kulawa da qaunar daya nuna mata a rayuwa. Shiru moddibo yayi yana kallonta bece komai ba akan maganar ya dubeta yace "ki kwanta ki huta zuwa safiya zamuyi nagana. Kwanciya tayi idanunta na kallon saman É—akin tayi lamo da ita sannan ya fita tareda kashe mata fitilan lagwanin.

Yana fita ɗakinsa ya nufa inda yabar Edyan don haka ya shimfiɗa masa zanin gadonsa meɗan haske ya kalleshi yace " Cikin gurɓatcciyar hausarsa yace ka kwanta yaro dare Yana yi kuma gashi kun kwaso hanya. Yana gama faɗin Haka ya juya jikinsa a salube ya bar ɗakin yay canta bayan bukkokinsa ya fashe da wani irin kuka..............

Chubado✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :46

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Not edited🙅‍♀️

_____✍️Wani irin kuka yakeyi tamkar ransa ze fita seda ya ɗau lokaci me tsayi yanayi sannan ya danni zuciyarsa yayi shiru, dafe kansa yayi da duka hannayensa biyu yana me tausayawa kansa bisa jarrabawar da Allah yayi masa gefe kuma ga iftila'in daya faɗawa iyalinsa wannan wace irin musiba ce haka ace iyalinka na ɗauke da cikin da Allah kaɗai yasan ubansa.

Maza sama da uku ace sunwa mace fyÉ—e at same time wa zaka nuna a matsayin uban wannan yaro?

Gabansa ne yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma ya dafe saitin zuciyarsa dayaji tana masa wani irin zafi, miqewa yayi daqyar ya nufi bukkarsa inda Ya sauki Edyan a ciki ya fara laluben ƴar qaramar jakar da ya shigo gidan da ita wadda ke ɗauke da magungunansa na Asbiti ya ɓalla ya afa a baka, ya jima zaune sannan ya ɗan samu relif da ace yabar wannan jakar a gidansu Muzaffar a sanadin Ganin Danejo dayayi da besan inda ze tsoma ransa ba.

Fita ya sakeyi zuwa bukkar da Laure ke ajiye shirginta ya kwanta acan ya barwa Edyan ɗakin shi kaɗai donya sake, yanajin fitar moddibo ya miƙe ya zauna tareda kunna fitilar wayarsa take hasken ya game ko wace kusurwa ta ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke me qarfin gaske sabida wani irin ciwo dayaji haqarqarinsa na dama ya farayi sabida rashin saboda irin wannan makwancin, ɗan buɗa idanunsa yayi tareda shafa kwantacciyar sumar gefan fuskarsa sannan ya miqe ya fara zagaya ɗakin yana tunanin yanda za'ai ya iya baci akan katifar ciyawan dake ɗakin, take yaji zuciyarsa ta mugun karye wasu siraran hawayen tausayin su moddibo ya fara zubo masa

"Taya za'ai ace mutum ya iya rayuwa a cikin irin wannan Dajin?

Edyan yayiwa kansa wannan  tambayar, take wani ɓangare na zuciyarsa yace dashi "ba gashi nan su suna rayuwa a ciki ba.

Hannunsa yasa na dama ya shafe ƙwallar data zubo masa a hankali ya furta "Alhamdulillah ya Rabb dakaimin ni'imar da ba kowa kayiwa kamarta ba, na tabbata ka haɗani da mulaikha ne don kawai a sanadinta nazo naga irin rayuwar da sukeyi Don kawai na Qara imani akan Rayuwa, ya Allah ka qara mana sutura duniya da lahira don Alfarman manzon Rahama (S.A.W).    A haka Edyan yayta tufka da warwara har bacci ya fara ɗaukarsa,

Kamae wanda aka mintsina yay firgigit ya tashi sabida wani irin kukan qwaro daya addabeshi, koya ya rufe idanunsa da nufin yayi bacci seyaji ya kasa sabida qarar kukan gyaren daya cika ɗakin, wani sirin tsaki ya saki tareda miqewa ya zauna a saman katifar kamar ze saki kuka sabida takaicin kukan qwaron da kuma rashin sabo da kwanan irin wannan gurin, duk irin gajiyan dayayi kasa baccin yayi  yanda yaga rana haka yaga dare.

         Wannan shine abinda ya faru a Rugar Arɗo.

                    *******

Ɓangaren su muzaffar kuwa basu shigo cikin Gyambu ba se wajen qarfe 11:00pm na dare,  direct wani babban hotel suka nufa muzaffar yay musu booking ɗakuna guda biyu Ummie tareda Zainab shi kuma nasu shida Abie
Chapter 47 · 0% Book details