← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 57

Sashe 30

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri Baba Hajara tace "tabbas ranka ya daɗe inada alaƙa da wannan case ɗin wanda kuma nake da tabbacin cewar mukullin warware wannan case ɗin ma kusan a hannuna yake don haka idan ka bani dama yanzu zan warware muku komai a gabanka inyaso bayan na gama seka yankewa Aisha hukunci kamar yanda ka fara daga farko. Sosai Ummie ta tsananta kukanta tace "kiyiwa girman Allah karki buɗe wannan sirrin da muka rufe wanda babu wanda yasanshi dagani seke Baba Hajara, kada ki kasance a cikin mutane marasa riƙon Amana da alƙawari wllh nina zuba masa guba da hannuna donyaci ya mutu kuma nayi hakanne sabida ƙiyayyar danake masa, kada ki baiyana wannan sirrin don baze taɓa canza komai ba Baba Hajara don girman Allah!!!!! Ummie ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar ƙwayar idon Baba Hajara tana kuka.

Wata uwar tsawa Mom ta daka musu tace "kai karku maidamu ƴan iska a nan gurin ku zaunar damu kuna shirya mana wasan kwaikwayon yaudara da rainin hankali, lallai Hajara na yarda rikicin tsufa ya fara taɓa ƙwaƙwalwarki shiyasa kike magana irinta marasa hankali da tunani, ɗan nawa zaki dinga dangantawa da wannan Azzalumar juyar matar bayan ina numfashi a doron ƙasa?

Shidai muzaffar gabaɗaya ya zama kamar wani mutum-mutumi sabida tsabar ruɗani da kuma ɗaurewar kai, zuwa yanxu ya fara tunanin cewar wata ƙila mafarki yakeyi ba zahiri bane yasa wannan abin me kamada tatsuniya yake faruwa a gurin. Shi kansa Abie binsu kawai yake da kallo daga mom ɗin har Ummie da Baba Hajarar batareda ya iya firta koda kalma ɗaya ba sabida ruɗani. Bakajin komai se hayaniyar mom dukta bi ta ƙanƙame muzaffar sekace wata zararriya tana zuba surutai wai babu wanda ya isa ya rabata da ɗanta wllh hakanne yasa Alƙali ya daka mata tsawa ba shiri ta tsuke bakinta still tana ƙanƙame da hannun muzaffar tana kuka

Sannan Alƙali ya kalli Baba hajara yace "ci gaba muna sauraronki kafin nan muna buƙatar jin cikakken sunanki

Ɗan jim tayi sannan tace "Sunana Hajara Ɗanladi kuma ni mutuniyar kano ce ƴar Asalin Unguwar kabara. Alƙali ya ɗanyi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago yace "meye hujjarki na cewa Aisha bazata iya kashe ɗan mijinta ba?

"hakane ranka ya daɗe kamar yanda na faɗa da farko cewar Aisha baxata iya kashe muxaffar ba to haka maganar take sabida itaɗin Mahaifiyarsa ce wannan dalilin yasa na faɗin hakan ranka ya daɗe. Alƙali yace meye hujjarki na cewar muzaffar ɗan Aisha ne?

Kallon Ummie Dake kuka Baba tayi sannan ta kalli Alƙali tace "tabbas nikeda cikakkiyar hujjar dazan tabbatar maka da cewar Aisha itace mahaifiyar wannan yaro. Gaba ɗaya falon suka zuba mata idanu suna kallonta ciki kuwa harda mom wadda itama take kuka kamar bazata dena ba hannunta damƙe cikin na muzaffar suna sauraron baba don siji jawabin dazata gabatar.

Baba Hajara ta fara magana kamar haka👇

"Shekaru 35 da suka wuce a shekarar 1985 lokacin ban daÉ—e da fara aiki a gidan Alhaji Abdulwahab Abdullah ba, lokacin matarsa Aisha tana Amarya kuma bazatafi shekaru 18 a duniya ba.

A lokacin Aisha bata da wayon dazata iya gabatar da wasu abubuwan na rayuwar gidan mijinta da sauransu, wasu lokutan nike nuna mata yanda zatayi wasu abubuwan idaɓ suka gagareta wannan dalilin yasa muka samu shaƙuwa sosai a tsakanina da ita dukda cewar ni kawai me aikinta ce amma sam ita batayi min kallon haka kallon uwa ma takeyi min

Sosai mijinta ke ƙaunarta kuma yake bata kulawa a haka har suka shafe shekara da shekaru amma shiru Aisha babu labarin ciki a tareda ita, dukda hakan mijinta be taɓa nuna mata damuwarsa akan hakanba hasali ma itace ke nuna damuwarta akan hakan har suka shafe shekaru goma da Aure amma shiru babu maganar haihuwa, wannan dalilin yasa Aisha ta da kanta ta tunkari mijinta Abdulwahab kan cewar lallai seya ƙara Aure sabida tana iya yuwuwa itace bata haihuwar bashi ba.

A wannan ranar ba ƙaramin saɓani suka samu ba har seda na shiga maganar nai musu nasiha sosai sannan suka daidaita a tsakaninsu sukaci gaba da zamansu kamar yanda suka saba, wata ranar litinin Alhaji ya dawo daga Saudiya bayan ya dawo ne yake sanar da Aisha cewar ya haɗu da wata budurwa a can kuma har cikin ransa yarinyar ta kwanta masa don hkaa yana son Aurenta.

Dukda cewar maganar ta ɗan taɓata amma sam Aisha bata nuna masa a ba sema farin ciki data tayashi tareda yi masa fatan alkhairi a cikin Auren nasa dazeyi, sosai Yayi farin ciki da hakan tareda yiwa Allah godiya daya bashi mace me kima da girmama buƙatar mijinta kamar Aisha. A wannan daren Aisha tayi kuka kamar ranta ze fita sedai bata gazaba wajen gayawa Allah matsalarta cikin dare ba kan cewar ya zaɓa musu abinda yafi zama alkhairi a cikin wannan lamari na auren da mijinta ze ƙara, lokacin da Aisha ta sameni da zancen sosai na dingayi mata nasiha tareda ƙara bata haƙuri akan ta ƙara danne zuciyarta insha Allah komai zeyi daidai.

Haka kuwa akayi Aisha tayi haƙuri taci gaba da sabgoginta har lokacin bikin ya matso kuma akayi lfy batareda wata matsala ta taso ba, haka kuma Aisha bta gajiya ba wajen bawa mjinta kulawa kamr yanda ta saba ba har Amarya Saratu ta shafe wata guda cur a cikin gidan ba'a samu wata matsala ta kunno kai ba, seda tafiya tayi tafiya sannan Saratu Amarya ta fara ɓullo da wasu mugayen halayenta a filli na makirci, idan Alhaji yana gida seta san yanda tayi ta muzgunawa Aisha don kawai ta kulata su raba abin faɗa sedai kawai tayi murmushi ta raɓa ta gefanta ta koma ɗakinta, bayan wata uku da bikin Saratu da Alhaji alamun ciki suka fara baiyana a jikin Saratu lokacin da ta fahimci ciki ne da ita ba ƙaramin faarin ciki tayi ba don hka ta fara shimfiɗa fefan iskanci kala-kala shi kuma alhaji yana biye mata, idan na dafa abinci setace ita sam ba nawa takeso ba girkin Aisha takeso dole haka Aisha zata fito ta shiga kicin ta girka mata duk abinda takeso batareda ta canza fuska ba ko kaɗan, idan na yunƙura zan taimaka mata setace na barshi ai abin cigaba ne yazo musu itada mijinta da abokiyar zaman ta.

Tun daga lokacin Aisha ta zama itace me girkawa Saratu abinci tamkar baiwa ba matar gida ba amma dukda hakan bata taɓa nuna damuwar ta ba sam

Wata ranar juma'a Aisha ta tashi da zazzaɓi me zafin gaske ranar Alhaji ba ƙaramar rikicewa yayi ba amma ita saratu ko'a jikinta lokacin da alhaji ya ɗauketa mukaje Asibiti gwajin farko ya nuna cewar Aisha na ɗauke da ciki kimanin wata 3 ashe duk wannan uwar wahalar datakeyi nayiwa Saratu girki itama nata cikin na maƙale da ita a jikinta batareda ta sani ba, murna a gurin alhaji ranar ba'a magana haka itama Aisha harda ɗan kukanta a haka muka rankayo muka dawo gida fuskokin mu ɗauke da farin ciki

Lokacin da Saratu ta samu labarin cikin jikin Aisha ba qaramin tashin hankali ta shiga ba harta kasa ɓoye hakan a fuskarta amma dayake makirace seta nunawa Alhaji farin cikinta a fili harda kukan ta na farin ciki wanda yafi kamada na munafunci, amma kuma a zuciyarta ba ƙaramin baƙin ciki taji da hakan ba, har ɗaki tabi Aisha ta sameta tace "hmmm naji ance kinyi ciki kema shiyasa naga se wani rawar kai kike kina ƙara shigewa mijin namu ko? To wllh kiji kuma ki sani muddin ina numfashi ni kuma bazan taɓa barin ɗanda kika haifa ya shaƙi iskar duniya ba Aisha don haka ki rubuta ki Ajiye wannan!.

Wannan magana ta girgiza Aisha matiƙa tareda dasa mata tsoron saratu tun daga lokacin ta shiga takatsantsan da duk wani abu daze haɗata da ita, a haka dai sukaci gaba da rayuwar har naƙudar Saratu ta tashi gashi kuma Alhaji baya gari, muda Driver ne muka kaita Asibiti Aisha kuma ta zauna a gida gabaɗaya abin duniya duk ya isheta kasancewar dare ne, Saratu tasha wahala sosai kamar bazata kai labari ba wannan dalilin ne ya haifar mata da jijjiga bayan ta haifi ƴarta mace sankaceciya fara tass da ita sedai yarinyar batazo da Rai ba. Sosai na tausayawa saratu dana tuna irin yanda take sanya rai akan ƴaƴa da kuma irin shirin datayiwa haihuwar sedai ga abinda Allah ya aiko babu yanda muka iya

washe gari da safe na dawo gida don na duba halin da Aisha take ciki jikina a masifar sanyaye tofa a nan ne na sameta akan gwiwa itama babu yanda take, tasha wahala sosai haka kuma nabuga na raya da ita mutafi Asbiti amma fir Aisha taƙi sema hannuna data rike gam cikin nata idanunta duk sun koɗe bakinta ya bushe ƙamas dashi cikin yanayi na zafin ciwon naƙuta tace "Baba Hajara Saratu ta Sauka lfy?
Chapter 30 · 0% Book details