← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 57

Sashe 39

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____✍️Direct Babban Asibitin dake cikin garin na Gyambu suka wuce dashi cikin ikon Allah a ɗan ƙanƙanin lokaci manyan liƙitocin dake on duty a ranar suka rufu a kansa, sun jima suna kokawa da numfashinsa sannan suka samu nasarar daidaituwarsa, bayan 2hours likitan daya jagoranci lamarin mara lfiyar ya fito sanye da farar labcord ɗinsa wanda gefanta duk yay stain da jini, wata irin zuface kwance a saman goshin likitan alamar sun wahala sosai wajan shawa kan matsalar, a nitse yake takowa cikeda nutsuwa harya ƙaraso inda su Muzaffar da Malam iro ke zaune damuwa fal a saman fuskokinsa ya tsaya ba tareda ya iya furta musu ko kalma guda ba.

Nurse É—in dake bayan likitance ta maida kallonta ga Muzaffar tareda kafeshi da mayun idanunta kamar zata cinyeshi É—anye, ganin sam basu lura da tsaiwarsu bane a gurin sabida ruÉ—un da suke ciki Nurse É—in tai gyaran murya cikeda gwalangwaso irin na Æ´an duniya tace " Ranka ya daÉ—e Dr. Na magana.

A hanzarce muzaffar ya É—ago manyan fararen Eye ball É—insa ya saukesu kan Likitan cikeda damuwa yace "Dr. How is he pls?

Ajiyar zujiya Likitan ya sauke tareda nazartar yanayin muzaffar É—in sannan yay murmushi yace "is ok dear he is fine Alhamdulillah ya fita daga HaÉ—ari, sannan a kwai mahimman abubuwan daya kamata mu tattauna dakai akan conditon É—in mara lfyn, muje office . Yana gama faÉ—in hakan yay gaba su kuma suka mara masa baya

A tsayawa yayi a jikin wata ƙofa wadda akayi rubutu da nau'in bakin ink kamar haka Dr. Fauwaz Qaribullah. Wannan ne ya basu tabbacin cewa lallai nan ɗin shine office ɗin nasa.

A nitse suka shiga office ɗin gabaɗayansu ciki kuwa harda Dr. Fauwaz ɗin zama yayi sannan suma suka yauna tareda fuskantarsa alamar a ƙage suke suji bayanin daze musu ɗin, murmushi yayi kaɗan sannan ya gyara zaman lab courd ɗin dake jikinsa yace "im sorry to say but gaskiya he is in critical condition abu mafi girma ma shine zuciyarsa ta riga ta harbu sakamakon wani tdiro daya bito masa a tsakiyar zuciyar tasa, magana ta gaskiya a yanzu se'an masa Aiki don rabashi da wannan abin cikin sauri a hakan ma idan anyi babu tabbacin cewar ze tashi. Ya faɗa yana kallon tsakiyar ƙwayar idanun Muzaffar wanda tashin hankali mara misaltuwa ya baiyana akan fuskarsa.

Cikeda damuwa kamar ze fashe da kuka yace "pls Dr. Babu wani abu dazaka iya taimaka mana dashi akan condition É—in nasa? ÆŠan jim kaÉ—an Dr. Fauwaz yayi yace " munada hanya gudaÉ—aya wanda nake ganin a kwai yuwuwar a dace. Da sauri muzaffar yace "inajinka Dr.

Dr. Yace "ina ganin yanzu zamuyi muku transfer xuwa wani babban Asibiti dake yola im sure of that Idankunje zaku dace. Dakatar dashi muzaffar yayi ta hanyar cewa no Dr. Ka bari kawai nidai alfarma É—aya nakeso kamin shine ka haÉ—amin manyan likitocin da sukasan aikinsu wa Æ´anda kuma zasu iya taimaka masa kafin zuwa gobe inyaso semu fita dashi india akan batun aikin yanzu bari nayi waya ai mana booking jirgi semu wuce Abuja gabaÉ—aya kafin goben.

Da wannan batun suka samu matsaya, bayan sun fita daga office ɗin Dr. Fauwaz Malam iro ya kalli Muzaffar yace "yaro taya zan iya yarda dakai kan cewar bazaka cutar da Moddibo ba idan har ka tafi dashi? Hannunsa muzaffa ya kama cikin nasa yace "a halin yanzu bazan iya furta maka komai ba Malam amma abinda na sani shine wajibi ne in biya Baffa alkhairin dayayi min koda kuwa hakan yana nufin gabaɗaya dukiyata zata ƙare ne, ya taimakeni a lokacin danake buƙatar taimako shin laifine dan nima nayi yunƙurin ceton tasa Rayuwar alhalin kuma inada damar yin hakan malam?

Da sauri ya ɗaga masa kai alamar aa bakayi laifi ba, kuɗi masu yawa muzaffar ya zaro ya miƙawa malam yace "don Allah malam ga wannan kuɗin ka kula da duk wata buƙata ta iyalan Moddibo sannan kayi musu dukkan abinda sukeso, kuma ka shaida musu cewar insha Allah Baffa ze samu lafiya har ya dawo musu da ƙafafunsa da izinin Allah, sannan idan ka koma gida ka gayawa Rabi'atou cewar ina gaisheta kuma nan bada jimawa ba zan dawo gareta . Ya faɗi maganar tareda baiyana zallar soyayyarsa gareta

kallon tsaf malm Iro yay masa da dukkan alamu besan abinda ke faruwa a cikin Rayuwar Rabe ba, wata irin zazxafar ƙwallar tausayinsa ce ta zubowa malam iro lokaci guda kuma ya juya yabar harabar Asibitin, tabbas yanzu kam ya shaida wannan matashi babu shakka shine wanda ya zauna dasu har kimanin watanni huɗu a taredasu. Komadai menene yanada yaqinin cewar baze taɓa cutar da Moddibon ba.

tun kafin muzaffar subar gyambu ya ɗaga waya ya kira PA ɗinsa Mubaraq Nuhu yace yayi masa booking ɗin private jet zuwa ƙasar india, cikeda girmamawa ya amsa masa tareda katse kiran, kamar yanda ya buƙata hakanne ya kasance gurin Dr. Fauwaz ɗin shida kansa ya haɗashi da ƙwararrun likitoci tareda mara lafiyan jirginsu ya ɗaga se birnin taraiya.

koda suka iso a ɗaya daga cikin gidajen ma'aikatansu ya sauki likitocin tareda duk wani abu dazasu buƙata sabida mara lfyan dukda cewar basa tsammanin faruwar wani abu mara daɗi a taredashi, shiko daga nan gida ya wuce Direct part ɗinsa ya nufa ya watsa ruwa sannan ya shiga part ɗin mom ya shaida mata cewar zeyi tafiya zuwa india, sosai suka dinga zuba masa adɗu'a ba tareda sun damu da tambayarsa dalilin yin tafiyar tasa ba tunda dama can sunsan yakanje ɗin musamman idan yanada meeting da abikanan kasuwancinsa, ya ɗan jima a nan suna hira sannan ya miƙe zuwa part ɗin Ummie da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga falon wanda keda zuba uban ƙamshin turaren wuta, babu kowa a falon se Baba Hajarah wadda ke kallon film ɗin hausa a tashar Tauraruwa, zama yayi a kusada ita tareda sanya kansa bisa kafaɗunta yace " Me ran Ƙarfe ya kike?

murmushi tayi tace "ina lfy ƙaramin me gida ya naganka haka nan kamar bakajin daɗin? Uhmm lfy na ƙalau wllh kawai dai na gaji ne sosai gashi kuma zanje india gobe insha Allah inada meeting. Jinjina kai tayi tace "to Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya ɗan albarka. Da amin ya amsa mata yace "ummie fa? "Yanzu ta shiga ciki

miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗin Ummien , a kwance ya sameta saman doguwar kujerar dake ɗakin Direct nufarta yayi yay hugging ɗinta tareda faɗin i miss u My. "katse wayar tayi ta dubeshi tace "ya dai na ganka haka kamar kana cikin damuwa? "no lfy lau Ummie kawai dai kewanki nake tunanin zanyi sabida gobe zan wuce india inada meeting da wasu sababbin masu hannun jari a companyn mu.

nan ma Addu'ah tayita mishi kusan a tare sukai Diner sannan ya fice ya koma part ɗinsa tareda sanya ran cewa insha Allah kafin Abi ya dawo daga kano yabar ƙasar tun kafin ya ɓaro jirginsa...

A gurguje pls

cikin ikon Allah kuwa washe gari da sassafe jirginsu ya É—aga zuwa Qasar india. Semuce A sauka lfy C.E.O

*_ƁANGAREN GIDAN ME GIRMA C.P KUWA_*

Edyan ne zaune bisa makeken ƙayataccen falons wanda aka ƙawata da ababan jin daɗi na duniya gamida ƙawata guri, kallo ɗaya zakayiwa falon ka fahimci shiɗin bame yasanson shirgi bane ba, sanye yake da farar T-shirt gamida wando treequater wanda ya kasance baƙi wuluk dashi, ƙafafunsa zube kan table ɗin glass ɗin dake ajiye kusa dashi idanunsa a lumshe, turo ƙofar falon tayi tareda ɗan tsayawa kaɗan tana bin ko ina na falon da kallo hannunta ɗauke da littafin da biro kamar zata fashe da kuka, a hankali idanunta suka sauka akan Hansome face ɗinsa ma'abociyar kwarjini gamida Haiba, kafeshi tai da manyan idanunta karona Farko a Rayuwarta dataji tunanin muzaffar ya faɗo mata a cikin zuciya da kuma gangar jikinta Gabaɗaya, takure jikinta tayi guri guda lokaci guda kuma taji sanyin Ac ɗin dake falon yana nema yayiwa duk wata gaɓa dake jikinta illah.

Wani irin daskararren hawayene me cikeda ɗaci gamida Zallar muradi mara misaltuwa ne ya fara kwaranya a kan kyakkyawar fuskarta, sakin littafin tayi ya faɗi a saman haɗaɗɗen kafent ɗin daya zagaye falon ta ko' ina tareda sanya hannunta ta ƙanƙame jikinta gaba ɗaya.

FaÉ—uwar littafince ta janyo hankalin Edyan zuwa gareta, a hankali ya buÉ—e limsassun idanunsa masu cikeda da alamar bacci ya daukesu tar a kanta. Ganin hawayen dake zuba a saman fuskarta ne yasa ya mike da hanzari ya isa gareta tareda dafa kafaÉ—unta duka biyu yace "what's wrong dear? Ya faÉ—a cikeda zallar nuna damuwarsa gareta.

Kasa amsa masa tai illa ƙara matse jikinta da ta sakeyi guri guda tamkar wadda aka jefa a cikin ƙorar ƙanƙara, lumshe idanunsa yayi ya sake buɗesu akan beauty face ɗinta yace "wllh da kinsan yanda nakeji idan naga hawayenki da bazaki taɓayin shi'awar ki zubar dasu haka a banza ba, zuciyata da duk wata gabar da jijiyoyin jinina kebi sukan ɗauki wani irin zafi wanda ya zarce na tafasashiyan dalma a duk lokacin dana ganki kina kuka, kodan sabida yanda zuciyata ke zafi meyasa koda so ɗaya ne bazaki hana kanki kuka ba Mulaikha?

Kafeshi tai da manyan idanunta tana me nazari akan maganarsa, daga irin kallon da take masa kaɗai zaka fahimci cewa sarai ta fahimci inda kalamansa suka dosa, amma kuma da ace shima ze san irin halinda take ciki a wannan lokaci tabbas dayayi mata uziri koda kaɗan ne, a irin yanda taƙeji a nata ran idan aka misalta da nasa wllh tata azabar ta zarce tasa. Wasu sababbin hawaye ne suka shiga sakko mata babu ƙaƙƙautawa lumshe lumsassun idanunsa Edyan yayi tareda miƙar da ita tsaye lokaci guda kuma a karo na farko a Rayuwarsa ya janyota jikinsa yay hugging ɗinta with so much love and caring. Gabaɗayansu wani baƙon yanayi suka samu kansu a ciki me matiƙar wahalar fassarawa sedai dukda hakan batayi yunƙurin zare jikinta daga nasa ba sema ƙara fashewa datai da wani sabon kukan wanda ita kanta batasan na menene ba.
Chapter 39 · 0% Book details