← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 57

Sashe 35

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___Kafeta da ido Alƙali yayi take Maryamu ta ida fita cikin duk wata nutsuwarta can kuma seta fashe da kuka tana kallon Alƙali tace "Ranka ya daɗe don girman Allah kaimin Rai karka hukuntani da abinda bazan iya jurewa ba wllh tsautsayi ne yasa na aikata hakan. Maryamu ta faɗi hakan tana kafeshi ida ƙananun idanunta se kuma can ta bushe da dariya hartana neman shiɗewa tace "Haka kakeso kaji nace ko Alƙali?

Wani ɗan iskan murmushi ta saki sannan ta tacigaba da cewa"wannan kukan dakaga inayi bana komai bane face na zalar baƙin ciki da namar cewar haƙata bata cimma ga ruwa ba tunda har ban samu nasarar dazanga bayan Aisha ba sabida tsabar tsanar danayi mata, a Rayuwata idan akwai wanda na tsana fiyeda mutuwata to wllh Aisha ce dukda kasancewarta mutuniyar kirki hakan besa na taɓajin ƙaunarta a raina koɗa kimanin girman ƙwayar zarra ba. Naso ace na samu nasarar kashe muzaffar kodan a yankewa Aisha hukuncin Kisa ta hanyar Rataya kokuma a jefata cikin babbar kurkun da zata haɗu da bala'in dazefi ƙarfinta a ƙarshe harma ya zama ajalinta amma kuma kash se gashi ta fita cikin sauƙi daga cikin ramin muguntar dana gina mata.

Gabaɗaya falon kallonta akeyi especially Ummie da idanunta suka firfito sabida tsabar mamakin kalaman na maryamu, wani irin ƙululun abu ne ya taso mata ya tsaya mata a maƙoshinta sabida yanda yawun bakinta ya ƙafe daƙyar ta iya haɗo kalaman da suka rage mata akan harshenta tace "Maryamu me nayi miki kekuwa a Rayuwa da har zakiyi min irin wannan gagarumar tsanar?

Murmushi maryamu ta saki wanda iyakarsa laɓɓanta wanda yafi kamada na zallar tsana mara tushe balle makama tace "wllh bakiyi min komai ba Aisha Hasalima se alkhairi da kikayi min a Rayuwa tareda duk wani ma dake kusa dani, kawai dai laifinki ɗayane a gurina shina na tsaneki kuma bana ƙaunarki wannan kawai shine dalilina kuma wllh na ƙudurtawa zuciyata cewar muddin ina numfashi a doron ƙasa tofa senaga bayan.....

Saukar wani lafiyayyen mari Maryamu taji a saman fuskarta wanda yasa ba shiri ta haɗiye maganar datake faɗa tareda zubawa wanda ya wanke mata fuska da marin, tun kafin ta ida ƙare mata kallo ta sake ɗauketa da wani hamshaƙin marin wanda yasa kunnuwanta suka toshe kimanin wasu mintuna sannan ta nunata da yatsa tace "Amma kedai wannan mata anyi cikakkiyar shaiɗaniya kuma butulu mara tabbas, lallai keta musammance a cikin jami'ar bada horo ta musamman tareda ƙwarewa a fanin Butulci da kuma cin amana, koda yake banyi mamaki ba idan akace gabaɗaya shekarun nan naki sun zama na banza shiyasa tunda idanuna suka sauka a kanki naji cewa har cikin zuciyata bana ƙaunarki ashe abinda ban saniba shine keɗin gabaɗayanki tamkar tauraruwa me jela kike wadda ganinki sam ba alkhairi bane.!!! Fadilah ta faɗi hakan tana wani irin huci kamar zata cinye Maryamu ɗanya.

Itadai mom gabaɗaya bin Maryamu take da kallo yayinda hawayen idanunta suka tsaya cak lallai yau kam ta yarda da cewar inda ranka kasha kallo a duniya, lallai duk tsiyarka a doron ƙasa to wllh a kwai mafiyinka a komai walau alkhairi ko sharri mom bata samu zarafin magana ba Alƙali ta buga gudumar tabbatar da hukuncinsa don kowa ya nutsu kuma ya bada hankalinsa don sauraron hukuncin daze yakewa maryamun

Alƙali ya nisa yace "bisa dubada hujjoji tareda iƙirarin da maryamu tayi na yunƙurin kashe muzaffar Abdulwahab Abdullah tareda iƙirarin cewar Setaga bayan Aisha Muhammad Lamiɗo don haka wannan kotu me alfarma ta yankewa Maryamu hukuncin life in prison har ƙarshen Rayuwarta kamae yanda hukuncin yazo a cikin littafin kunɗin tsarin hukuncin mulkin Nigeria. Ya faɗa tareda buga wannan guduma sannan ya bada umarni da akama Maryamu doka ta fara aiki akanta daga wannan rana

Wani Uban ihu Maryamu ta zunduma tareda fuzgar biron dake gaban aljiun Rugarsa tayi kan Ummie gadan-gadan har tana haɗa hanya sabida muguwar zuciya, da wani irin mugun zafin nama Muzaffar ya ture Ummie gefe Tayi baza zata Faɗi Abie ya tareda da hanzari ta faɗa jikinsa hakanne yayi daidai da saukar biron da Maryamu tai niyar cakawa Ummie a gefan hannunsa na dama take jini ya ɓalle ya fara zuba, kamata sukai da ƙarfin tsiya sukai waje da ita inda motar tafiya prison ɗin take cikin muntuna da bazasu gaza 10 ba sukabar harabar kotun da ita se Babbar Prison ɗin da ake adana manyan shahararun ƴan ta'adda waƴanda aka yankewa hukuncin kisa dake babban birnin na taraiya Abuja.

Da hanzari Ummie ta fuzge jikinta daga na Abie ta nufi muzaffar tareda sanya hannunta ta danne inda jinin ke zuba hawaye na sakko mata, yau a karon farko a Rayuwarta hannunta ya taɓa jikin Gudan jininta muzaffar tun bayaɓ shekara 35 a lokacin yana jariri, wani irin Abu ne me kamada nau'i shaƙuwa gamida zallar ƙauna da soyayyar ɗada Uwarsa tana Ratsa duk wata gaba ta jinin dake gudana a jikinsu, tabbas a yau ya gamsu da cewar Ummie itace Mahaifiyarsa because he feel something about her as a mother saɓanin mom dabe taɓa jin irin wannna shauƙin a tareda ita ba, Ashe dama wannan nutsuwra dake ratsashi a wannan lokacin a sanadin taɓashin da Ummie tayi shine abinda ya rasa a rayuwarsa tsahon shekara 35?

Janyo Ummie yayi da hanzari ya Rugumeta lokaci guda kuma ya saki kuka tareda kwantar da kansa a kafaɗunta ya shiga rera sabon kuka tamkar wani ƙaramin yaro, shafa bayansa kawai Ummie takeyi itama hawaye nayi mata Ambaliya a saman Fuskarta

Gabaɗaya falon ficewa sukai duk girmansa ya kasance daga Muzaffar se Ummie kuka kawai yakeyi tana shafa bayansa ba tareda ta dakatar dashiba sabida a wannan lokacin babu abinda yake buƙata sama da hakan da ƙyar ya iya buɗe bakinsa muryarsa na Cracking yace "Ummie why? Why Ummi....... Gabaɗaya yama kasa magana sabida tsabar yanda kukan yaci ƙarfinsa, still she's tapping his shoulder hawayenta na ƙara tsananta zubowa

Ummie ƙara rungume ɗannata tayi cike da so ganida zallar ƙauna,
Seda suka dauki lokaci me tsayi a haka babu Wanda ya samu zarafin magana

Duk abinda ke faruwa a tsakanin Ummie da ɗan nata Fadilah na zaune na kallonsu itama tana hawaye sabida tsabar yanda suka bala'in bata tausayi it almost 35 years Rabonda yaji ɗumin jikin mahaifiyarsa, A hankali Fadilah ta sakko ƙasa daidai inda ƙafafun Muzaffar batareda tayi magana ba ta wani irin fashe da kuka tareda ficewa daga falon da saurinta, wani irin kunyar Muzaffar takeji bisaga abubuwa na rashin kunya da ƙiyayyar data dinga nuna masa mara tushe takeji se'a yanzu ta fahimci cewar Ashe ba tsanarsa tayi ba kawai dai kishi takeyi dashi akan abinda take ganin nata ne ba nasa ba wanda tafi dan ganta hakan da ƙuruciya gamida wauta, harta kai ƙofar fita daga falon se kuma ta tsaya Chak lokaci guda kuma ta juyo tana kallonsu tace " haƙiƙa ina me jajanta muku akan abinda ya Sameku dakai da Ummie yaya Muzaffar Haka kuma ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai ɗin ɗan uwa na ne guda ɗaya tilo, wanda kaf duniyar nan bamuda kamar ka nasani wata rana dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba ɗaya, tunda Uwata ta haifeni ban taɓa jin kunya irinta yauba danake tsaye a gabanka nake kuka yaya muzaffar! Yaudai kam na yarda da maganganunka da kake gayamin kullum cewar idan har ban gyara wasu abubuwan na Rayuwata ba tabbas wata rana zanyi nadama to yaudai kam da alama wannan ranar ce tazo min tunda har na fahimci kuskurena tun kafin lokaci ya ƙuremin.

A madadin Mahifiyata dani kaina Don Allah Ina me roƙon ku afuwa dakai da Ummie akan abinda muka aikata muku don Allah yaya muzaffar ka yafe mana plsss. Ta faɗa tana zubewa akan gwiwoyinta still tana maganar tana hawaye.

A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Ummie tace " haƙiƙa kin cika Uwa wadda ta cancanci da a yaba mata, tunda har kika Iya sadaukar da ɗanki guda ɗaya tilo dan kawai ki sanya mikinki farin cikin wllh dik inda uwa ta gari Takai to kinkai a kiraki da wannan suna Ummie, naso ace ina ɗaya daga cikin waƴanda suka fito daga cikin cikinki tabbas danayi alfahari dake a matsayin Uwa.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye

A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Ummie da Abie ta ɓangaren Mom ma kusan hakane ko babu komai yanzu tayi karatun tanutsu da al'amarin Rayuwar duniya, haka kuma ta fahimci cewar lallai Aisha ta musamman ce tunda a ko ina take Halaiyarta ta gari itace ke jamata alkhairin Rayuwar duniya.

RUGAR HARDO
GYAMBU TARABA (STATE)

Kwance yake cikin yanayi na Rashin lfy sosai daƙyar yake iya miƙewa ya zauna sabida nauyin da gefan ƙirjinsa na hagu ne masa, gabaɗaya lips ɗinsa duk sun bushe alamar baya iya cin abincin kirki balle yasha Ruwan daze hana bakin bushewa

Inna Laure ce ta shigo ɗakin jikinta a matiƙar mace ta zauna daga gefansa hannunta ɗauke da ƙoƙo ta jiƙo masa magani, kamar zatayi kuka tace " don Allah ka daure ka tashi ko yayane ka samu kasha tunda idan kasha ɗin ciwon yanayin Sauƙi.

Hawayen dake maƙale cikin ƙwayar idanunsa ne suka samu zarafin Zubowa sannan ya sanya hannunsa na dama ya danne saitin zuciyarsa yace "taya zan iya Rabuwa da ciwon tunani gamida na Zuciya bayan Amanar da Allah ya bani bata taredani a Yanzu? Laure inaji a jikina cewar tamkar mun Rabu kenan nida Rabe har abada kuma bazamu sake haɗuwa da juna ba
Chapter 35 · 0% Book details