← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 57

Sashe 13

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan dawowarsa da minti goma sega Fadilah ma ta dawo, buɗe motar tayi ta fita tana kuka batareda ta jira gurds ɗinta sin buɗe mata ba kamar yanda ta saba ba, cikin gidan ta nufa da cogalelen takalminta tana kuka a haka ta shiga falon ko Sallama babu, gabaɗayansu ido suka zuba mata daga Momy har Abie zainab kuwa baki ta saki da hanci tana kwasar kallo sabida a iya zaman da sukayi tare kafin ta tafi India bata taɓa ganin Fadilah tana kuka irin haka ba se yau itako meya sameta haka?

Bata kulawa kowa ba ta kwasa da gudu ta nufi Upstairs tana ƙara sautin kukanta Al'amarin daya ƙara ɗagawa su Abie hankali kenan sukabi bayanta, duk yanda sukaso su cimma Fadilah abin ya faskara tana shiga ɗakinta ta murza key ta faɗa gado ta shiga rusa wani sabon kukan baƙin cikin, duk irin rarrashi da ban bakin dasu Abie keyi kanta buɗe musu ƙofar fur Fadilah taƙi buɗewa dole yasa suka haƙura suka barta.

*******

*Gyambu Taraba state*

Zuwa yanzu kam moddibo ya gama sarewa da lamarin Rabe sabida yanda yarinyar ta rame kuma ta fita haiyacinta, bata da aiki se kuka da keɓe kanta daga shiga cikin mutane wannan al'amarin ne yake ƙara ɗaga masa hankali, ko abincin kirki bata iya ci yau tunda sanyi safiya take fama da wani irin ciwon ƙirji me matiƙar zafi, buguda ƙari ga wani irin nauyi da saitin zuciyarta keyi mata.

Kokaɗan bataso ta nuna gazawarta a idon Mahaifinta wadda yanke kallonta a matsayin sanyin idaniya a gareshi, tasan dolene idan ya fahimci irin halinda take ciki beze taɓa samun kwanciyar hankali ba shiyasa ta zaɓida ta boye masa lalurarta, kwance take kan katifar ciyawarta idnunta na kallon saman bukkar dake ɗakin wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata a lokacin data tuna abinda ya faru a tsakaninta da Muzaffar ranar da suka tafi kiwo na ƙarshe dashi.

*Flash back*

tunda suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallonta haka kawai yaji cewar yana shi'awar kallon nata dik inda tabi idanunsa na kanta tamkar baze dena kallonta ba, ita kuwa sabgar gabanta kawai take ba tareda ta lura da irin kallon dayake binta dashi ba tana ɗagowa a karon farko idanunsu ya sarƙe cikin na juna
A hankali ta buÉ—e baki tace" Hamma zafar meyasa kake yawan kallona a Æ´an kwanakin nan?

Murmushi yayi sannan yace"sabda zanyi missing naki.

Sosai take kallon sa tace " meye kuma mushin ke nufi?.

Dariyace ta kamashi amma kuma ya danne yace "kalmar tana nufin zanyi kewarki ne to.

Wata irin Dariya ce ta kamata sosai irin wadda bata tabayin kamarta ba a gabansa ba a Iya zaman da yayi tareda dasu, daƙar ta iya saita kanta ta dena dariyar tana kallonsa tace "amma Kaɗo ka iya tsiya Aradu.

Tunda ta fara dariyar yake kallonta kamar zeyi kuka yace, meyasa kik dariya irin haka bakisan yawan dariya yana gusar da imani ba?

Murmushi tayi tace abinda ka faÉ—a ne ya bani dariya, Aradu senaji Kalmar taban tamin daban a shikin kaina.

Hade rai yayi yace " to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni kuwa?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riƙe kunnuwanta guda biyun kamar yanda yakeyi mata idan ya ɓata mata rai kamar zatayi kuka ta tsuguna ƙasa tace "waɗu munyal Hamma zafar badan ƙara ba!

Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace "uhm that's my Fulani girl shikenan na haƙura amma kaɗan.
Dariya sukayi gaba É—ayansu dukansu, a haka wannan Ranar ta kasance daban a garesu koma a kirata da Rana ta musamman a gareta.

A zaman datayi dashi kullum ƙara samun kusanci yake da zuciyarta batareda ita kanta tasan hakan ba, wasu Zafafan hawayene suka shiga zubo mata yayi data farka daga duniya tunanin data Afka akan matashin ɗan kasuwar mejida kuɗi da ƙwalisa wanda a gurinta ya kasance tamkar wani mutum na daban wanda take kallo tamkar wani waliyi a birnin zuciyarta Saɓanin shida ya mance da batun wata fulani girl dake Rayuwa a wani ƙaramin daji wanda sam be gina masa wani muhali a cikin filin zuciyasa daze iya tunawa nan kusa ba.

Zuwa yanzu kam ta sare kan cewar Zafar baze taɓa cika alƙawarinsa gareta ba na cewar ze dawo gareta komai daran daɗewa koda kuwa ba nan kusa bane yau gashi ya kwarari kusan shekara da tafiya ba tareda ya juyo gareta ba. Burinta a yanzu shine Allah yasa a duk inda Hamma zafar yake ya kasance a cikin Farin ciki da ingantacciyar rayuwa koda ace baze ƙara tunata a cikin Rayuwarsa ba har Abada zata cigaba dayi masa kyakkyawan fata har zuwa ranar da Ranta zebar jikinta.

*Abujah*

Tunda ya dawo ya kasa gudanar da komai sabida ɓacin ran daya dawo dashi daga office, ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan ya miƙe ya faɗa toilet donyin wanka be jima ba ya fito ɗaure da towel ɗaya a ƙungunsa ƙarami kuma bisa wuyansa, goge jikinsa yayi tsaf batareda ya shafa maiba ya buɗe tafkekiyar drower ɗinsa dake manne a jikin katafaren bangon dake ɗakin ya fito da wasu ƙananan kaya marasa nauyi ya sanya a jikinsa, tareda yin cumming lallausar Sumar dake kansa ya fita harabar gidan.

Da Zainab yaci karo tana mishi murmushi tace "bro Anul Abie da momy ne sukace y nazo na dubaka ko lfy sunji ka dawo amma bakazo kayi lunch ba. Dafa kafaɗanta yayi suka fara tafiya tare har suka isa maine falo ɗin Momy suna ɗan taɓa hira sannan yace "Cutie zee jeki haɗamin ouds pls banson cin komai yau

Da kalli Momy ta bishi wanda yafi kamada na mamaki tace "Son a kwai abinda ke damunka kenan tunda naji kace Zainab ta haÉ—a maka ouds meyake damunka?

Ajiyar zuciya ya É—an sauke kaÉ—an sannan yaja É—aya daga cikin kujerun dake zagaye da daining É—in yace "Mom ba wani babban al'amari bane fa. HaÉ—e rai tayi tana kallonsa da sauri ya janye idinsa ya kalli Abie yace "pls Abie kace mom ta bar yimin irin wannan kallon don Allah wllh xan faÉ—a muku komai.

Murmushi abie yayi me cikeda dattako sannan yace "to naji gaya mana meke faruwa. Ɗan jim yayi sannan ya shiga sanar da Abie kaf abinda ya faru a tsakaninsa da Fadilah ba tareda ya rage komai ba. Ƙura masa ido mom tayi bakinta a buɗe sabida tsabar mamaki...........

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :19_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Not Edited
____✍️nausawa tayi cikin jejin babu abinda takeyi se kuka sabida rabuwar datayi da mahaifinta, jefa ƙafarta kawai takeyi batareda tasan inda take jefata ba ga dare daya farayi, babu komai cikin dajin face kukan gyare da kuma na tsintsaye kasancewarta Bafulatanar Daji hakan besa taji tsoro ba becouse dama a cikin dabbobin ta tashi kuma take rayuwa so babu wani baƙon Abu a gareta , babbn abinda zuciyarta ta yarda dashi shine there's nothing can happen to her because her father prayer is still by her side, da wannan tunanin kawai tke tafe zuciyarta nayi mata zafi.

Ta sani sarai cewar ita kaɗaice ta ragewa mahaifinta a halin yanzu haka kuma ƙaunar dayake mata me girma ce, batajin ze iya sadaukar da wannan babbar ƙaunar dayake mata a banza becouse ruwa baya tsami banza inji ƴan magana. Dole yanada dalilinsa me ƙarfin gaske da har yasa yashi rabuwa da ita a wannan lokacin. Ƙirjinta ne ya amsa da sauri lokaci guda kuma ta zuɓe akan gwiwoyinta tareda ɗora hannunta na dama a saitin zuciyarta, rarrafawa tayi tareda gyara zaman wannna jakar saƙin da moddibo ya rataya mata a kafaɗarta batareda ta bari jakar ta faɗi ba, a haka ta jingina bayanta da wata ƙatuwar bishiya tana maida numfashi.

*_ABIJA NIGERIA_*

yau tunda sanyi safiya Muzaffar ya gama shirinsa cikin wata Ash ɗin Korean suits iya gwiwa kasancewar garin da ɗan sanyi sosai, tsaye yake jikin makeken Dressing mirror ɗin dake manne jikin bangon ɗakin yana gyara zaman agogon rolex ɗin dake hannunsa, ƙurawa kansa idanu yayi kamar meson gano wani abu a tattareda kansa, lumshe idanunsa yayi sannan ya buɗe wanda hakan yayi daidai da saukar idanunsa kan tabon ciwon da lallausan gashin kansa ya fara rufewa, hanunsa yakai gurin ya janye lumsasshen gashin kansa yana kallon tabon lokaci guda ya dafe kansa yace "ya Rabbi!!

Juyawa yayi da sauri ya fita daga bedroom ɗin nasa zuwa falo, koda ya fito falon ma tsayawa yayi cak becouse ya kasa tuna actual abinda ya fito dashi daga ɗakin, zibewa yayi akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun royal chairs ɗin sukayiwa falon ƙawanya.

Wayarsa ce ta É—auki ruri yana dubawa yaga sunan Abie yana yawo akan screen na wayar, ajiyar zuciya ya sauke meÉ—an nauyi sannan ya answer call É—in Abie yace "son gobe ne fa meeting É—in daza'a gabatar a India ya kamata ka fara shiri akan tafiya zuwa gobe da yardan ubangiji lallai ya kamata ace kana guri za'ayi komai becouse hajiya Aisha she's not feeling fine.

"insha Allah zanyi ƙoƙarin yin hakan Abie and then you should send me her number so that na kirata na dubata. "Ok son i will send it for you. Abie ya faɗi hakan yayinda yake katse kiran

Ajiye wayar shima muzaffar yayi haka kawai seya samu kansa dajin wani baƙon yanayi wanda ya kasa misaltashi, ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu a lokacin da Babban Amininsa Edress Adam ya faɗo masa a rai, wayar dake gefansa ya zaro lokaci guda kuma ya fara ƙoƙarin lalibo number ɗin Edrees ɗin tareda kira, harya katse amma Edress sam be ɗaga ba har seda ya sake kiransa a karo na biyu sannan ya ɗauka tareda faɗin "shugaban masu kirki WhatsApp?

Tsaki muzaffar yaja kaɗan sannan yace "fine ya kk?. " I'm fine and you? Edrees ya faɗi hakan yana wani male baki kamar an masa dole. A daƙile muzaffar yace "ban sani ba ɗan renin sens you but you know what?
Chapter 13 · 0% Book details