← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 57

Sashe 24

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dakewa Ummie tayi tana binsa da kallo tamkar wadda aka dasata a gurin, gaba ɗaya ji take komai ya tsaya mata chak har motar Asibitin ta ƙaraso ƙofar gidan still tana tsaye kan ƙafafunta, Maryam ce ta fita da hanzari tayo musu jagora zuwa cikin gidan inda muzaffar ɗin ke kwance samɓal babu alamar numfashi a taredashi, kin kimarsa sukayi suka ɗorashi bisa wani siriri gado sannan suka fito dashi Zuwa cikin motar, basu jira fitowar wani daga cikin gidan ba sukaja motar sabida ganin irin condition ɗin mara lfyn se bayan sun fita Hajiya Aisha ta zube bisa doguwar kujerar dake falon tana maida numfashi

wayar muzaffar dake kusa da System ɗin Ummie ce ta fara ƙara kasa ɗagawa ummie tayi hakanne yasa maryam ta isa ga wayar jikinta na wani irin rawa ta Amsa ba tareda ta duba sunan me kiran ba, cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali mom tace "boy are you Ok?

Wani irin fashewa Maryam tayi da kuka nan ta shiga zaiyanawa Mom halinda muzaffar ɗin ke ciki. Wani irin Zabura mom tayi ta miƙe zaune daga kwancen da take cikin yanayi na fitar haiyaci tace "ɗan nawa ne yafi guba ??????

Abie wanda ke kwance ne ya miƙe idansa nakan Mom wadda jikinta ke wani irin rawa sabida tsabar tashin hankali, fashewa tayi da kuka tana danne ƙirjinta dake mata wani irin suya ta kalli Abie bakinta na rawa tace "kagani ko? Senayi magana sekace kishi ne ke ƙoƙarin hanani zaman Lfy da Aisha to gashi nan yau ta zubawa ɗana guba a abinci kuma ya........... Girgizata yayi da wani irin Sauri sabida ganin idanunta na ƙoƙarin rufewa take mom ta dawo daidai cikin haiyacinta tareda faɗawa jikin Abie ta saki wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wata uwa datasan ma'anar haihuwa. A daran ranar Abie yayi hayar privet jet zuwa ƙasar India aiko kiran sallar farko suka himmata sukabar ƙasar.

India 🇮🇳

Hajiya Aisha da ƙyar ta iya miƙewa ta koma ɗakinta tareda zubewa a bakin gadonta zuciyarta duk a cushe, gabadaya komai ya tsaya mata tayanda takejin cewar dama hakan bata faru ba do take tayi kuka amma kuma ta kasa yin hakan, dama idan wani bala'in ya sameka hawayen ma ɗaukewa yake gabaɗaya a haka har gari ya fara haske still tana zaune batareda ta rintsa ba.

cikin ikon Allah jirginsu Abie ya sauka lfy cikin mintuna kaɗan motocin company sukazo ɗaukarsu Kasan cewar basu san Asibitin da aka kwantar da Muzaffar ɗin ba dole yasa suka ɗauki hanyar gidan Hajiya Aisha, gabaɗaya mom ta birkice tamkar wata zararriya idanunta duk sunbi sun koɗe sabida kukan data gurza, a haka motocin suka tsaya a bakin ƙofar gidan cikin jerin gwano.

kokaɗan basu jira an buɗe musu ƙofar motar ba kamar yanda suka saba mom ta ɓalle murfin motar ta diro tana huci, da wani irin sauri ta shiga gidan tana kwaɗawa Ummie kira a birkice, sautin muryarta ne yasa Hajiya Aisha tasha jinin jikinta kuma ta fito daga ɗaki jikinta a saluɓe tamkar kazar da ƙwai ya fashe ma

tana fitowa idonsu ya sarƙe cikin na juna a karon farko tun bayan shekara 35, wani irin wawan Mari mom ta ɗauke Ummie dashi har seda taga taurari tun kafin ta watsetsake ta ƙara ɗauketa da wani marin, cikin kiɗima Ummie tace "ni kika mara Saratu?

cikin fusata Mom tace "na mareki Kiyi duk abinda zakiyi, Se yau na sake tabbatar da cewar ki cikakkiyar shaiɗaniya ce Aisha kuma wllh ki kwana da sanin cewar sena hukuntaki a bisa laifinki na bawa ɗana guba wllh koda kuwa abinda na mallaka ze ƙare akan shariya dake!!!!

Abie dake tsaye yana kallonsu ji yayi duk Hajiya Aisha ta sure masa a rai a sanadin abinda ta aikatawa gudan jininsa namiji tilo tabbas baze ƙyaleta ba a wannan karon dole ne shari'a tayi aiki akanta, ya juya yana kallon jami'an tsaron dake bayansa yace "ku tafi da ita!!!

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo mata daga idanunta ba tareda tayi magana ba jami'an suka tusata Station abisa yunqurinta na kisan kai..............

Har suka fita da ita bata dena kallon Abie ba lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka wanda ita kaÉ—ai tasan ma'anar abinta.

Thanks 4d love fans❤️

comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :24_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

_____✍️Har suka fita kuka takeyi sosai jikin Abie ya sanyi dajin sautin kukanta seda dukda hakan bayajin cewar ze iya ƙyaleta bisa yunƙurinta na kashe masa ɗa.

Tsaki Mom taja tana shirin magana sega maryam ta fito, ƙura mata iɗanu mom tayi a ranta tana tunanin inda tasan wannan fuskar Katse mata tunani maryam tayi ta hanyar cewa "Sannunku da zuwa Ranki ya daɗe nice wadda mukai magana dake ta waya ta faɗi hakan tana matse ƙwallar data zubo mata da gefan zanin Atamfar dake jikinta. Ajiyar zuciya mom itama hawaye na zubo mata tace "wani Asbiti aka kaimin ɗana ?

"Ghandy Special Hospital ne dake Ƙarshen Layin nan naryam ta faɗin hakan. Cikeda Masifa mom tace "taya za'ai kukaishi ƙaramin Asibiti a madadin kukaishi na Compay? Wll......" kinga Saratu pls ki nutsu ki dawo cikin haiyacin ki insha Allah komai zeyi daidai, Nasan Asbitin farin sani kuma sunada kayan aiki sosai karki manta nan ba Nigeria bace suna bawa Asbitocinsu dukkan abinda ya dace wanda za'a kula da marasa lfy dasu cikin ƙwarewa.

Kuka ta fashe masa dashi har suka fita daga gidan zuwa Asibiti bata dena kukan ba, a nitse Driver ɗin dake tuƙasu ya faka motar a harabar Asibitin inda aka tanada sabida hakan, Dukda cewar Asbitin ƙarami ne amma yana da kyau gamida tsari fiyeda zaton me karatu kusan gabaɗaya hankalin mom baya jikinta burinta kawai taga halinda ɗanta yake ciki.

A haka suka isa reception na Asbitin A nitse Abie ga ƙarasa gurin da wasu nurses ke zaune da alama sune cashier's na Asbitin, tambayarsu yayi inda aka kwantar da mara lfyan cikin harshen turanci matashiyar yarinyar tace "faɗi sunan mara lfyn sena duba maka. Cikin mintuna kaɗan ya gaya mata sunan take ta binciko musu ɗakin da mara lfyn yake suka nufin ɗakin

A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya sabida hanasu shiga da akayi seta ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin suke hangensa, kwance yake kan gadon Asbitin an saka masa uniform me launin kalar brown, fuskarsa ɗauke taƙe da oxygen inda bakinsa kuma akai warring wani dogon five wanda ya taho tundaga cikinsa sabida poison ɗin dayaci, babu abinda ke motsi a jikinsa se iskar numfashin dake fita ta cikin na'urar oxygen ɗin da aka saka masa. Se'a lokacin idanun Abie suka sauka akan Rubutun da akai bisa jikin ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin kamar haka (ICU) intensive care unit. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske a ransa yace "lallai ɗansa yana cikin tsaka me wuya tunda har aka kawoshi cikin wannan ɗakin to abin bana wasa bane. Wani iri yakeji a zuciyarsa gameda wannan gagarumin cin Amanar da Hajiya Aisha tayi masa, meyasa zata aikatawa ɗan daya haifa irin wannan zalincin?

Kuka sosai mom take hakanne yasa Abie ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta, wata irin tsanar Ummie ce take ƙara ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyarta tareda ƙudurtawa kanta cewar wllh koda abinda ta mallaka ze ƙare setayi shariya da Hajiya Aisha tayanda nan gaba koda ɗan dabba bazata sake yunƙurin kashewa ba ballan tana ɗan mutum.

*******

ƁANGAREN HAJIYA AISHA kuwa station suka hurgata suka kulle gabaɗaya komai ya tsaya mata cak ta rasa abinda ke mata daɗi a cikin wannan duniyar, bata taɓa zaton haka daga gurin Abie ba tayi zaton cewar ɗabi'arta data ɗaɗe tana nuwa masa bazata barshi ya amince da wannan al'amarin daya faru da ita cikin sauƙi ba amma kuma se gashi shida kansa yasa ƴan sandan wata ƙasa suka kamata har cikin gidanta suka fito da ita suka kawota wannan gurin mara tsabta. Tabbas tayi data sani a rayuwarta na sanin Abie da zuriyarsa tun farko, da ace bata sanshi ba da duk hakan bata faruwa.

wani irin kukan baƙin ciki ne ya taso mata tareda data sanin Abinda ta aikata a Rayuwar ta, babban tashin hankalinta a yanzu shine taya zata iya sanar da iyayenta da ƴan uwanta halin datake ciki??????

A haka Rayuwa ta dinga tafiyar mata cikin yanayi na rashin jin daÉ—in Rayuwa gamida walwala.

NIGERIA 🇳🇬

Edriss ne zaune tareda mom ɗinsa cikin danƙareren falonsu na alfarma wanda ko gidan shigaban ƙasa se haka, da damuwa kwance akan Handsome face ɗinsa yace "mom nifa hankalina sam ba'a kwance yake ba wllh inaji a jikina cewar dama banje Taraban nan ba sam wllh. Ya faɗa kamar zeyi kuka

Da kulawa matar daya kira da mom ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi tace "why are you saying that sweetie? "mom wata yarinya muka bige a hanyar dawowan mu daga Taraba. Edriss ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun mahaifiyar tasa. Be damu da irin kallon datake binsa dashi ba yaci gaba da cewa" haka kawai naji a raina ina tausayin yarinyar mom becouse ƙarama ce sosai kuma wllh mom she's pretty.

Sosai mom Edriss ta kaɗu dajin baya nan ɗan nata da ƙyar ta iya cewa " yanzu Edriss a wannan uban dajin ta ina gida ze kasance balle har a samu yarinya har ku bige da mota?

a dake ya kalleta yace "no mom ba yarinya bace kamar kowa she's Fulani girl......

Cikeda kaduwa Mom Edriss ta kalleshi tsoro ƙarara akan fuskarta tace "Fulani girl? Ta faɗa cikin karaji.........

comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :25

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

*_All Characters, place, organizations and incident of this Interesting Novel are fictitious😁, so pls my dearest sisters abinda yake me kyau a ciki to dashi zamuyi koyi bada akasin hakan ba, Allah ya bamu ikon aiki da darasin dake ciki don isar mazon Allah✊_*

___✍️ Murmushi yayi har seda fararen haƙoransa suka baiyana sannan yace "mom why are you looking so surprised?
Chapter 24 · 0% Book details