Sashe 5
Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin dana tsince ka Ban taɓa zaton zan sameka da sauran numfashi a tareda kai ba amma Dana tabaka sena fahimci kana numfashi, a haka na ɗakko ka a daji na kawo nan mukaita kula dakai tareda rauni kan Dake jikin ka har Allah ya amince mana ka tashi A yanzu.
Nan da nan idon matashin ya kawo ruwa ba komai ne yasa shi hawaye ba se irin karamcin da moddibo yay masa A Rayuwa tabbas bashida abinda ze iya biyasa dashi,
Yanzu babbar damuwarsa A yanzu Itace be San halin da Mahaifinsa yake ciki ba, sedai bashida wani zaɓi wanda ya wuce yaci gaba da zama tareda wannan bawan Allahn kuma ya mant da rayuwarsa ta baya!
Cike da kulawa moddibo ya dafashi yace "kayi haƙuri yaro nasan dole zakayi kewar gida tareda ƴan uwanka amma ka Ƙara haƙuri jikinka ya Ƙara Ƙwari Inyaso seka Koma garesu Kaji?
ÆŠaga masa kai kawai matashin yayi ba tare da Yace dashi komai ba ya mayarda idanunsa ya kulle,
Har moddibo ya mike se kuma ya sake sunkuyowa yace da matashin yaro ya sunan ka??
Gabansa ne ya faɗi yayin da yaji tambayar da Modibbo yayi masa amma, nan da nan wani ɓangare na zuciyarsa yace masa "karka sake ka faɗi cikakken Sunanka dana mahaifinka idan ba haka ba Mutanan nan Zasu gane gane waye kai cikin sauƙi kuma su mayar dakai hannun maƙiyanka waƴanda suka jefaka a wannan halim da kake ciki a yanzu!
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske Still idanunsa a Rufe ba tareda ya buÉ—esu ba Yace "Uhm uhnn Sunana Sunana Muhammad Ali.
Ɗan jim kaɗan Moddibo yayi yana kallonsa sannan yayi murmushi yace "Masha Allah Muhammad ai babban Sunana To Allah ya ƙara lfy.
Duk wannan hiran da suke Rabe na jinsu a nitse ta Ƙaraso kusa da matashin da murmushi a fiskarta tace "Anya sunan Muhammad ne?
Da sauri ya buɗe manyan idanunsa yana kallonta har seda gabansa ya faɗi sannan ya ƙaƙalo murmushi a karo na farko yace " Ae Sunana kenan kamar yanda kikaji Muhammad Ali. Ya faɗa yayin dayake ɓatar da murmushin dake kan fuskarsa a lokaci guda.
Tun daga lokacin da Matashin yayi mata murmushi har zuwa sanda ya gama magana take kallon sa ,
Ba komai take kallo ba se tsabar kyau Da tsarin halitta irin nasa, bata tabbatar da shi kyakkyawa bane seda yayi murmushi A iya Tsahon rayuwarta Har zuwa yanzu bata taɓa ganin mutum irinsa ba,
Mutane dayawa Kan fada Mata cewar tana da kyau amma yau Kam taga Wanda ya fita kyau da tsarin halitta,
(Nima kaina Danake kwaso muku rahoto seda na dan tsorata da kyawu irin na wannan matashi lol)
Seda moddibo ya dafata sannan ta dawo daga duniyar tinanin da take,,,
A daburce tace "baba yaushe za'a kuma bashi abinci?
Harga Allah ba abinda tayi niyar fada ba kenan tsabaragen daburcewa ne yasa ta fadi hakan, sosai moddibo ya fahimci halin data Samu kanta a ciki amma kawai seyay murmushi ya fita daga ÆŠakin.
A hankali A hankali ya BuÉ—e idanunsa ya É—ago kansa ya kalleta yace ya sunan ki?
A taƙaice tace" Sunana Rabe.
A hankali ya kuma maimaita sunan Yana wani yamutsa fuska yace "what's that does mean?
Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa, hakan yasa ya taɓe baki ƙaɗan Yace" ok lem me call you with Fulani, I can't even call you with that locally name is it Rabe or what ever. A taqaice Ya sake kallonta still itama kallonsa take batareda tamasan abinda yake faɗa yace "You can't thanks for everything Fulani girl. Ya faɗi hakan yana mayar da idanunsa ya kulle
ta jima tana juya kalmarsa ta ƙarshe a ranta dikda cewa bata San meyake nufi da ita ba, amma setaji Kalmar tayi mata dadi Kuma ta tsaya mata a Rai. A haka taɓar ɗakin tana ta juya maganar a Ranta
har yamma
Moddibo Rabe bata ƙara dawowa ɗakin ba Har lokacin shafa masa magani yayi Shida kansa ya shafa masa maganin, sannan yasa Rabe ta Dora masa ruwan zabi ta kawo masa tana kawowa tayi waje abinta, moddibo ya tashi ya nufi inda Matashin ke kwance a hankali ya fara kiran sunan sa,
A nitse ya buÉ—e idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Yayi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka , a nitse ya fara Ƙoƙarin tashi amma kuma seya kasa tashi moddibo ne ya taimaka masa Harya tashi zaune.
wani farin saki moddibo ya Ƙara Ɗakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasa Masa jikinsa, dik da cewa jikinsa nayi masa ciwo sosai hakan be hana moddibo gsa masa Shi yanda ya dace ba,
Yana gamawa ya ÆŠakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi alwala, Cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya shiga rama sallolin da ake Kansa.
ya Dade yana yi dik da cewa besan adadin kwanakin daya Kwashe baya cikin haiyacinsa ba a Wannan Ƙauyen,
Seda ya ÆŠau lokaci me tsayi sannan ya idar, moddibo ne ya tai maka masa ya kwanta sannan ya ÆŠakko wani zanin saki ya lullube shi ba'a ÆŠau lokaci Me tsahi ba bacci yay a won gaba dashi
*****
Æan garen Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa ÆŠakin ba
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta gabatar da aiyukan da ta saba na yau da kullum seda ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i, bayan ta idar ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Da sauri ta mike ta cire mayafinta ta nufi katifar ciyawarta Dake É—akin dan ta kwanta sbda sanyin daya fara busawa,
Kamar daga sama taji an banko mata cikin Ɗakin aiko da sauri ta miƙe sabda sanin ko wacece ta shigo Ɗin, dan indan da sabo Yaci ace ta Saba da halin Laure.
Masifa fal ranta ta shigo ÆŠakin tare da y
Binta da wani wulaƙantaccen kallo tace " to yar gatan gata rere A fito kiyi min ayki dakike Koƙarin kwanciya Bacci ƴar mowa Wato ga baiwa Ubanki ya ajiye inyi muku wahala ko ? To wllh baki isa kiyi bacci yanzu ba Har sekin gamamin aiyukan dake cikin gidan nan.
Bata jira cewarta ba ta fincikota sukayi waje, wasu tarin kwanuka ta gani an jibge Matasu gefe kuma Ruwane a cikin wata Ƙatuwar fanteka da alama Ruwan ya Dade a gurin Batun base an fada ma ya dau sanyi ba,,
Kallo daya zaka yiwa kwanukan ka fahimci babu Wani datti ko kadan a jikin su kawai tsabaragen mugunta ne yasa Laure ta Fito dasu.
Ba musu Rabe ta sunkuya ta fara Ɗauraye kwanukan tanayi jikinta na rawa sabda sanyi Dake busawa har taci Ƙarfin kwanukan, da laure taga bazata Iya jure sanyi ba setai shigewarta Ɗakin tabar Rabe a waje tana fama Da sanyi, ta ɗau lokaci me tsawo Tana ɗauraye kwanukan sannan ta gama ta kife mata su,
ta wuce daki jikinta Se rawar sanyi yakeyi, tana shiga ta kwanta dikda cewa ta lulluba amma Sam bata dena jin sanyin ba,,
Abu kamar wasa Haqoranta suka fara haduwa da juna Suna fitar da wani sauti na daban, nana da nan zazzabi me zafi ya rufeta daƙar ta samu bacci ya Ɗauke ta
Ba ita ta farka ba se bayan an idar da sallar asuba, daƙar ta samu tayi alwala ta gabatar da sallar
Ko data idarma kasa tashi tayi daga inda Tayi sallar sabda wani irin azababben jirin data keji.
Har gari Yayi haske sosai kowa ya fara harko kin Gabansa amma Rabe bata fito ba.
A Æangaran moddibo Sosai Yayi mamakin rashin ganin Giftawar Rabe har wannan lokacin Bata fitoba, azatonsa ko bacci takeyi shiyasa be wani damu sosai ba,
A nitse ya gama gabatar da komai na karyawa Wanda Matashin zeyi Karin kumallo dashi, amma
Har ya gama bega idon Rabe ba, se kuma abin ya fara damun moddibo
Æangaren Matashin saurayin kuwa tunda ya tashi daga baccin safen da yayi ya afka duniyar tunanin meyasa Yakeda tarin maÆ™iya ne a Rayuwarsa? Me yay musu suke son ganin bayansa a Rayuwa? Me kuma ya tare musu har haka?
Modibbo ne ya Katse masa tunanin dayakeyi ta hanyar shigowarsa É—akin tareÉ—a abincin Sa A hannunsa yace " ya kamata ka tashi kaci abinci kasha maganin ka ko?
Ba musu ya fara Ƙoƙarin tashi dikda cewa ba iyawa zeyi ba,,
Moddibo ya saki murmushi yace" yaro gaskiya kana da Ƙarfin hali sosai ka Ƙara haƙuri Insha Allah ka kusa fara tashi da kanka.
Tunda moddibo ya fara magana idon Matashin yana kansa se kuma Yayi murmushi yace "to baba Allah yasa Hakan Sedai bazan gaji da Ƙara jaddada godiya ta a gareka ba sabda Haƙiƙa ka taimaki rayuwata, Ablokacin dana fitar da ran akan Rayuwar duniyar gabaɗaya!! Shiru ya ɗanyi sannan ya sake kallon moddibo yace " thank you for saving my life,,, ya Ƙarashe maganar tare da hawaye
Da sauri moddibo ya dafa kafaɗunsa yace "kada ka damu yaro ni nayi maka dan Allah ne badan wani ba, dan haka ka dena zubar da hawayenka kaima kamar Ɗa kake a gurina kuma nayi maka Alƙawarin Cewar zan kula da kai har zuwa ranar da zaka Samu sauƙi ka koma ga iyayen ka. ya Ƙare maganar da murmushi A kan fuskarsa
Canza fuska matashin yayi a likacin da moddibo yayi masa zancen komawa gida, Sosai yake jin kalaman moddibo a Saman zuciyar sa harga Allah dattijon ya shiga ransa, moddibo ne ya share mai hawayen sa sannan ya fara bashi kunun Daya shigo dashi irin nasu na Fulanin Asali, Sosai Matashun ke jin daɗin kunun dan haka yasha sosai sannan yace ya Ƙoshi.
Moddibo yayi murmushi yace masha Allah tunda yanzu ka Ƙoshi bari na shafa maka maganin ka se kuma kasha na shan ko?
Matashin yace "haka ne.
Seda moddibo ya gama shafa mai maganin sannan ya bashi Nashan shima ya shanye. yana gamawa yace to yaro bari in je inga Rabe ko lafia naga har yanzu bata fito ba.
Matashin yace" hakane kam yakamata a duba agani ko lfya,
Daga haka moddibo yay waje ya nufi ÆŠakin Rabe da sallama, tana nan a Inda tai sallah jikinta se rawa yake da sauri moddibo ya nufeta yana tambayar ta Meya sameta?