← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 57

Sashe 49

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta take shauqin da murna suka yaye mata hujabin tsoron lauren data daÉ—e tanaji ta nufeta da wani irin excitement on her face ta rungumeta, ko babu komai itama zata haifa mata qanin daze dinga É—ebe mata kewar kaÉ—aicin data taso a cikinsa.

Duk yanda taso ta Ta kali fuskar inna Lauren sam abin be yuwu mata ba dole ta haqura ta fara qoqarin matsa mata qafar yanda zata É—anji dama-dama

A ɓangaren zuciyar Laure nadamace zallarta dukda cewar bata fito mata da hakan a fili ba, gabaɗaya kunyar yarinyar takeji musamman idan ta tuna irin zaluncin data dingai mata a rayuwa ba tareda haqqinta ba, tayi mata alkaba'i me tarin yawa wanda bakinta baze iya qayadewa ba se gashi tun ba'aje ko ina ba Allah ya mayar matada mugun nifinta a kanta, hawayene suka zubo mata amma kuma setai saurin sa hannunta ta goge gudunɓkar Rabi'atoun ta gani.

A haka har aka kwashe lokaci meÉ—an tsayi suna tare tana matsa mata qafar.

A É—akin moddibo kuwa shirun ne ya fara gundurar kowa amma banda Ummie wadda ke zaune jefi-jefi takan É—aga idanunta ta kalli yayan nata. Abie ne ya katse shirun ta hanyar cewa "salati goma ga manzon Allah (S.A.W) nan take kowa ya amsa aka shiga jerawa manzon Rahama salati bayan sun kammala Abie ya É—aga kansa ya kalli modÉ—ibo yace "da farko dai ina mai baka haquri bisa abinda ke tsakaninka da Aisha bawai a matsayin suruki ba a'a ina magana ne a matsayina na Abdulwahab Abdalla kuma ubaga É—anda Aisha ta haifa, haqiqa Aisha tayi kuskure musamman data gaza haquri ta zauna tareda danginta sakamakon iftila'in daya faÉ—a mata, gabaÉ—ayan mu dagani harkai babu wanda ze iya misalta irin ciwon da zuciyar Aisha ke ciki tunda gabadayan maza ne ba mata ba amma kuma dazamu É—ora kanmu a matsayinta na tabbata hukuncin data zartarwa rayuwarta muma irinsa zamu yanke kokuma akasin hakan, banaso ka kalli aisha a matsayin mace mara tausayi kokuma adalci sabida sam siffarta ba haka take.

A iya zaman danai da ita kimnain shekaru talatin da biyar na karanci halaiyarta ta yanda ko ina naje zan bada labarin wacece ita.

"amma kuma ai hakan be hanata iya guduwa tabar Ahalinta ba duk sabida wani dalilinta mara tushe!!!!! Moddibo ya faɗi hakan ransa a matiqar ɓace. abie zeyi magana Moddibo ya kalli su muzaffar da Edyan se kuma zainab dke zaune suna raba idanu yace "maza ku tashu ku bamu guri zamuyi magana.

Ba musu gabaɗayansu suka miƙe suka fita kamar yanda modɗibon ya buqata sannan ya dubi Abie yaci gabada cewa "duk na saurari batunka nima yanzu zakaji abinda na riqa a matsayin hujja dukda cewar ba lallai Danejo ta sanar dakai ba, kamar yanda ka faɗa a maganganunka na baya tabbas ni kaina mai iya bada shaida fiyeda yanda ka bayar ne akan Danejo sabida tun batasan kanta ba nake rainonta da hannayena, nasha haqura da abubuwa da dama a rayuwarta don kawai na inganta Rayuwarta to amma meye laifina don kawai qaddara ta Fyaɗe ta faɗawa rayuwarta shikenan seta gudu ta barni ba tareda ta sanar dani inda zataje ba har tsahon shekara 35?

A matsayinka na uba wanda keda ƴaƴa mata ka ɗora maganata akan mizani shin wani irin hukunci zaka yankewa Aisha a lokaciɓ da qaddara ta sake haɗaka da ita?

Shiru Abie yayi zuciyarsa cikeda zallar tausayin modÉ—ibo he wish to see his sister kamar yanda modÉ—ibo yaga tasa qanwar wadda tun bayan rasuwar mahaifinsu da aka musu rabon gado ba jimawa mijinta ya É—auketa sukabar garin ba tareda ya sanar dashi ba, tunda suka tafi har yau be qarajin duriyarsu yayi neman harya gaji duk kuÉ—insa da kuma shahararsa har yau babu wani labari akan Balaraba qanwarsa. Nan take Abie ya fashe da kukan tausayin kansa

Seda yay me isarsa sannan ya ɗaga kai ya kalli moddibo yace "ina roqonka Arziqi ɗon Allah ka yafe mata wllh da kasan irin wahalar da Aisha tasha akan tunaninka na tabbata zaka yafe mata ba tareda ka tsaya dogon nazari ba, tundaga lokacin dana tsinci Aisha a bakin hanya babu numfashi a jikinta har zuwa lokacin dana fara soyayya da ita har mukai Aure Aisha bata taɓa samun kwanciyar hankalin manta ka ba, haka kuma munje numan yafi a qirga amma kuma bamu sameku ba se bukkokinku da aka sakawa wuta suka qone, dukda haka Aisha bata yanke qauna ba kuma bata fasa zuwa numan ba akan kozata samu labarin inda kuka koma.

A qarshe da abin yayi tsamari É—aukarta nayi kacokan na maida ita india da zama kozata rage yawan damuwar dake ranta. A qarshe kuma ina me maka wasilci kan cewar Allah ma munayi masa laifi kuma ya yafe mana ba tareda ya duba girman laifin da muka aikata masa ba.....

Hawayen dake idanunsa Moddibo ya share sannan ya kalli ummie dake zaune tanata gurzar kuka a karon farko tun shigowarta ɗakin yace" na yafe miki Danejo Allah ubangiji ya yafe mana gabaɗaya 😭

Zabura tayi ta riqe qafafunsa tace "nagode Hamma Allah ya qara girma.

A haka kowannensu zuciyasa ta cika da farin ciki mara misaltuwa, fitowa Abie yay daga bukkar bisaga mamakinsa muzaffar na kan wani dutse wanda ke facing É—in É—akin moddibon daga É—an nesa, fara'ar kan fuskar Abie ce ta bashi tabbacin cewar baffan ya yafewa mahaifiyar tasa. Misalta irin farin cikin da muzaffar ke ciki abu ne da baze yuwu ba don haka suka rungume juna da Abie shikuma Edyan yanata baza uban murmushi wanda ke nuna farin cikinsa ga abokin nasa.

Tun'a safiyar ranar labari ya gama karaɗe rugagen dake maqotaka datasu moddibo kan cewar Danejo da Rabe sun dawo harda ɗanta saurayi ma da kuma mijinta, don haka akwai taron al'ada wanda za'a habatarwa da Danejo da kuma ɗanta wanda ba'ayi mata ba tun shekarun baya *_(niko nace kuji bidi'a don Allah 🤣)_*

Kafin kace me jama'a kowa ya fara halarta zuwa bikin Al'adar Auren danejo da kuma mijinta.

Bayan Azahar aka kawo kayan sakin da Ummie da Abie zasu saka wanda ya kasance launin blue da yallow a cikin wasu qwarya guda biyu kowada nasa se kuma takalman roba suma guda biyu da kuma lulluɓi, su muzaffar da Edyan ma sam ba'a barsu a baya ba sedai su nasu kayan na farin saqi ne kamar na sauran ƴan gaiya, bayan anyi sallar la'asar ne Bulo handi tazi tasa Ummie ta sanya kayan saqin da aka kawoma ummien sannan ta umarceta dataje ta taimakwa mai gidan nata ya shirya tunda tasan yanda ake komai. Ba musu ta fita daga fakin zuwa inda Abie yake

Seda ta tabbatar ta taimaka masa ya gama saka komai na biki al'adar sannan ta É—akko cinkon saqaqqiyar igiyar kaban dake gefe ta rataya masa suka fito tare, a waje suka cimma su muzaffar da edyan da zainab suma sun shiya cikin farin saqin suna jiram fitowarsu.

Kusan a tare suka nufo inda ake gudanar da shagalin bikin al'adar daga muzaffar har Edyan seda abin ya nemi ya basu tsoro musamman yanda sukaga an gangama uban itace uwa naci gefe kuma nawa saniya guda ne a banqare ana gasashi gabaÉ—aya fuskokin mutanna dake gurin duk an fenteta da uban farin fenti da yellow irindai kwalliyar fulanin jeji, har aka kabbara kiran sallar magrib ba'a fara shagalinba har seda kowa yay sallar magrib tukunna

Sosai abin ya burge zainab don haka ta fito da wayarta tana É—aukar vedio tun daga zuwansu Abie har kujerar da suka zauna seda ta dauka a vedion , kafin kace me tuni shagali ya kankama abin babu kama hannun yaro sannan Rabe suka qaraso gurin itada ruqatu da kuma ModÉ—ibo, gabaÉ—yansu tsareta sukai da ido daga muzaffar É—in har Edyan É—in, nan take zuciyar muzaffar ta fara aiyana masa kan cewar yaje gareta.

Yana shirin miqewa Edyan ya rigashi miqewa ya nufeta fuskarsa É—aukeda wani hamshaqin murmushi tareda fito da wayarsa ya fara É—aukarta hotuna tana dariya, yana zuwa kusa da ita yace "looking so Masha Allah partner. Washe haqora tayi tace "thank you partner and you too.

Matsawa yayi dab da ita yace "can I snap a picture with you babe?

Why not. Ta faÉ—a tana gyara tsaiwanta sosai kusa dashi

Duk abinda suke idanun muzaffar na kansu babu abinda zuciyarsa keyi banda tafasa, a fusace ya miqe daga inda yake zaune ya nufi inda suke ɗaukar hoton har idanunsa nayi masa sabida ɓacin rai............ Hannunsa yaji an riqe ta baya don haka ya tsaya chak jikinsa na wani irin rawa yana juyawa yaga zainab ce ba shiri yay hugging ɗinta still jikinsa na rawa, a tsorace take binsa da kallo Cikeda tsoro ta zare jikinta daga nasa tace "what's wrong bro? talk to me pls.

Comment
Nd
Share

Dont forget to vote on whatpad.

ChubaÉ—o
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :48

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

*ɗan tsokaci a gameda masu cewa ya kamata ace muzaffar yasan dalilin dayasa mahaifiyarsa tabar Rugarsu zuwa wani guri na daban, ina so kuyi aiki da basirar da Allah ya baku a matsayinku na ƴan Adam masu tunani, inaso ku ɗora kanku a matsayin da Muzaffar kekai shin ya zakuji idan akace yau wani ɗan fashi ya hauro gidanka kuma yayiwa mahaifiyarka Fyaɗe? Na tabbata da ace hakan ta faru gara ace ƴan fashi sun shigo gidan ka sun kashe mahaifiyarka se hankalin ka yafi kwanciya da ace wani ɗan iskan banza ya ketwa mahaifiyarka alfarmarta, bawai ban karɓi qorafinku bane a'a kawai dai inaso ku ɗora lamarin a mizanin dedaito da hankali ne👏*

BANYI EDITING BA🙅‍♀️
Chapter 49 · 0% Book details