← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 57

Sashe 15

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"amma baba meyasa se kalmar rabuwace zata fito daga bakinka a lokacin danafi kowa buƙatarka? Wllh baba tunani na ya gaza kamar yanda shekaruna suka gaza wajen fahimtar kalmar da kake nanata min ta Rabuwa..... Don Allah baba kada ka bari bakinka ya sake furta wannan kalmar tabbas zuciyata da gangar jikina bazasu taɓa iya fahimtar abinda kakeso su fahimta ba Baba!!!!!? Ta faɗi hakan tana wani irin rushewa da kuka a jikinsa.

Sautin kuwar jama'ar dake rugar kawai kakeji tareda ƙara kusantowar ƙarar harbin bindigar wajen bukkokinsu, fusgeta Modibbo yayi daga jikinsa lokaci guda kuma ya daka mata tsawa yace "lallai ya zama wajibi ki saurareni a matsayina na mahaifinki, idan har Allah ya hukunta cewar zamu sake haɗuwa tabbas zamu haɗu amma kuma idan Allah ya raba ganawa a tsakanin mu lallai ki kasance me kare martabar mutuncin ki har zuwa muhalin daya dace, sannan idan ƙaddara ta sake haɗaki da Muzaffar lallai ki gaya masa cewar idan da hali to ya cika alƙawarin daya ɗaukarmin a kanki, idan kuma ƙaddara bata haɗaku ba lallai karki kuskura ki ƙara tako ƙafarki cikin Gyambu har rayuwarki ta ƙare a inda kikaj........! Ya faɗi hakan wani irin kuka yana taso masa.

Wani irin tausayinta yakeji sedai vayajin cewar ze iya barinta a taredashi a wannan halin sabida sam baze juri ganin mutuwarta a gaban idanunsa ba, ya sani cewar abu ne mawuyaci mace ta rayu a inda bata babu wani nata kuma ta rayu ciki salama kokuma cikin Aminci batareda ta lalace ba, sedai babu yadda ya iya dole hakan shine mafita a garesu gabaÉ—aya. ÆŠaga hannunsa yayi sama yana kuka yace "ya ubangiji na ga Amanar daka bani nna ta Æ´ar dana haifa, ya Rabbissamawati wal'ardi ka kulamin da ita a duk halinda zata samu kanta a ciki, ya Allah kada ka barta da iyawarta ka Iya mata da iyawarka ya Allah!

zata sake magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar jan hannunta suka fito daga bukkar yana share hawayensa.

Koda suka fito basu cimma inna laure a tsakar gidan ba hakanne yasa moddibo leƙawa ɗakinta don ya tabbatar da tana ciki kokuma ta tsere, can ya hangeta ta haye kan katifar ciyawarta jikinta banda rawa babu abinda yakeyi, takawa yayi da sauri ya fuzgota tana tirjewa a haka ya janyota suka fito, gabaɗaya babu abinda ke tashi a rugar face sautin harɓin bindigar da ƴan fashin ke amfani da ita, baka ganin komai se ƙurar jar ƙasar dake tashi a gurin hakanne ya haifar hargitsewar dabbobinsu, hatta shanunsu duk sun kwance sun fazama cikin daji a gigice.

Cikin jeji moddibo ya nausa dasu banda gudu babu abinda sukeyi a haka har suka fara nisa da rugar, fusge hannunta Laure tayi daga cikin na modibbo tace "Sakarni Moddibo wllh ban ƙara ko taku guda daga nan, kana nufin haka zamubar dukiyarmu da kuma ƴan uwanmu ɓarayi na kashesu kamar tsintsaye?

Hawaye ne ya zubo masa a lokacin daya tina Wasiyar mahaifinsa na cewar" a duk sanda masifa ta afka muku modibbo da zarar ka samu nasarar fita daga gurin da masifar ke faruwa kaida iyalanka koda wasa karka bar É—ayansu ya koma inda abin ke faruwa idan kuwa har hakan ta faru lallai É—ayanku ze mutu idan kuwa har ba'a mutu ba to zaku tabka babbar Asara cikin biyu za'ai É—aya.

Fashewa yayi da kuka ya janyo Rabe yana kuka ya Rungumeta lokaci guda kuma ya zare jikinsa daga nata yace "lallai kiyi nisa da wannan jihar tamu nisa me tsahon gaske sannan ki sanya a ranki cewar idan da rabo wata rana zamu sake haɗuwa. Juyawa yayi da sauri zebi bayan Laure da hanzari ta riƙe hannunsa tana kuka tace "kayimin alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da ƙaddarar data rabamu zata dawo dani babana. Zeyi magana ta dakatar dashi tace " nidai kayimin alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da zan dawo gareka a raye batare da kabari muwa ta riske ka ba.

Gabaɗayansu kuka sukeyi me taɓa zuciyar duk wani me imani, da sauri ya ɗaga mata kai yace "nayi miki alƙawari ƴata tabbas zan jiraki har zuwa ranar da ƙaddara zata dawo min dake. Yana faɗin haka ta saki hannunsa tana kuka ta juya ba tareda ta sake juyowa ba ta nausa cikin jeji batareda sanin inda ta nufa ba.

Zubewa yayi a ƙasa ya fara sharɓar kuka musamman daya tuna alƙawarin daya ɗaukarwa ɗiyarsa wadda be taɓa gaya mata abinda yake ba gaskiya ba daga bakinsa, se gashi yau an wayi gari yayi mata alƙwarin da baze iya cika matashi ba.

Ya jima yana kukan sannan ya miƙe yabi bayan laure yana me ƙara jaddada Amanar Rabi'atou ga ubangijinsa....

*Chai nasha ƙorafi mara adadi dik akan wannan littafi 😂*

*Yasin idan banga ruwan comment ba se bayan sati biyu zaku sake ganina koma na ajiye alqalamin gabaɗaya Huta roro waken gixo yaqi ƴaƴa🤷‍♀️*

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :20_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️ Da kallo kawai hajar tabishi tana me tausayin kanta a nan gaba, Allah ne kawai shedarta akan irin son datakema wannan bawan Allahn tun daga ranar data fara ganinsa zuciyarta ta amsa, batajin cewar zata jurar rashinsa koda na kimanin ƙwayar zarra ne.

Share hawayen dake xubo mata tayi sannan ta ƙara gyara zamanta akan kujerar datake kai, a yau dai kam ta lasarwa kanta takobin cewar bazata taɓa barin falon nan ba harse taji matsayinta a gurin Muzaffar koda hakan ze zama wani abu me zaman kansa ne a tsakaninsu. Tambaya ɗaya ce taƙe mata yawo a zuciyarta shine wacece wannan Fulani girl ɗin da cikamakin Rayuwarta yake Ambaton sunanta haka a gabanta batareda shakka ba?

A ƙalla ba ƙasaru ba Hajar seda ta shafe Awanni uku chur zaune a falon batareda uban gaiyar yasan da ita a gurin ba har yayi baccinsa ya tashi kana yayi wanka ya canza kaya zuwa launin ƙananan , Black jeans with Sky blue T-shirt Sosai kayan ya karɓi jikinsa tamkar dama danshi akayisu, komai nasa tsaf-tsaf dashi shiyasa yake classy guy. silifas ya ɗauko a cikin shoe rack ɗinsa me launin baƙi ƙirar companyn Batozy ya sanya a ƙafarsa, hakanne ya sake fito da ainihin kalar hasken fatar jikinsa gaba ɗaya, a nitse yake takawa harya fito daga Bedroom ɗin ya ƙaraso cikin falon tsayawa yayi chak yana kallon hajar wadda ke bacci da mamaki kwance akan fuskarsa yace "ya salam what kind of lady is this?

Haɗe rai yayi sosai tareda bugawa gefan kujerar firgigit Hajar ta tashi tana kallonsa, ƙura mata idanu yayi with serious face yace "me kikeyi har yanzu baki tafi gida ba?

"taya zan tafi bayan har yanzu bansan matsayina a gareka ba? Hajar ta faɗi hakan idanunta na shirin kawo ƙwalla.

"look hajar ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci manufa ta, ni gabaÉ—aya yanzu babu soyayyah a tsarina a zatona ya kamata ace zuwa yanzu kin daÉ—e da cireni a ranki tunda na gaya miki abinda ya kamata ace kin gane kokuwa?. Ya faÉ—i hakan yana kallon tsakiyar idonta

Kuka Hjaar ta fashe masa dashi al'amarin daya ƙara ɗaga masa hankali kenan, a rayuwarsa ya tsani kukan mace ballantana kuma ace shine silar yin kukan nata da sauri yace "its ok hajar pls stop crying yanzu kije gida insha Allah idna na dawo daga india satin gaba me zuwa zanzo gidanku se muyi magana ok? Da sauri ta ɗaga masa kai tana share hawayen dake idonta ta miƙe tsaye, kusan a tare suka fito daga part ɗinsa har suka iso maine falon Momy

Waya suka samu Momy nayi tana ganinsu ta katse kiran tace "bari zamuyi magana zuwa gobe. Daga hakan ta katse kiran tana binsu da kallo

Sunkuyar dakai hajar tayi cikeda jin kunyar Momyn tace "mom zan wuce gida. Kallon tsaf mom tayi mata sannan ta ɗaga mata kai tace "kigaida mamanki. Bata ƙra cewa komai ba ta nufi daining batareda tace da muzaffar ƙala ba, sosai yasha jinin jikinsa da irin kallon tuhumar da Momy ke binsa dashi yace "mom pls me namiki?

Tsayawa tayi ba tareda ta juyo ba tace "Au tambayata ma kakeyi donka rainani? Me wannan yarinyar takeyi a part É—inka har tsahon wannan awannin kuna tare?

Da sauri yace "Mom!!!! Are you suspecting me for doing something with her?

Ba tareda ta kalleshi ba tace "no at all but bari Abie ya dawo dolene a tsayar da maganar Aurenka koma da wace yarinya ne sabida ni bazan ɗauki iskancin nan a gidana ba, and let me tell you something muzaffar wllh dole ne kayi Aure idan har baka son ganin ɓacin raina. Damn sauri yace "mom Aure Kuma? But senake ganin...... "ya isheni haka nan malam ka wuce kawai ka bani guri.

Jikinsa a mace yabar falon ransa a matiƙar ɓace, yana fita harabar gidan ya nufi mota ze shiga da sauri Selomon ya nufoshi ze buɗe masa ƙofa ya dakatar dashi yace "ban key yau ni kaɗai zan fita. Ba mutsu ya miƙa masa keyn ya shiga motar ya buga mata key ya fuce daga gidan gaba ɗaya, tabas dole ne ya zauna da Abie tun kafin mom ta rigashi yin hakan yasan dole Abie ze fahimce shi becouse baze masa dole akan abinda bayaso ba ko kaɗan, tsaki yaɗan ja kaɗan lokacin da Hajar ta faɗo masa a rai yace "komai ya faru itace silah.

Murmushin mugunta yayi daya tuna zainab, tabbas yasan itace ta haÉ—a masa komai tunda ai seda ya gaya mata cewar karta faÉ—awa hajar yana gida amma kuma seda ta gaya mata, dole ne ya hukunta ta akan hakan.

*_GYAMBU TARABA STATE_*
Chapter 15 · 0% Book details