← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 57

Sashe 22

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen shiga mota ba ƙaramar ɗirama akayi da ita ba ihu ta dinga zuba musu seda Edyan yay dagaske sannan ta yarda ta shiga suka tafi gida gabaɗaya, duk a tsorace take kallonsu kawai take itako zeeyadah gabaɗaya tausayin yarinyar ya gama cika mata zuciya.

India🇮🇳

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah a ɗan wannan tsukun lokacin abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa dadi, a ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi dukda irin ɓarnar da poison ɗin yayi masa a ciki, ada sam baya iya zama amma yanzu kam yana iya zama da kansa harma yayi tafiya koda bame tsaho bace. Sosai hkaan yawa Su mom da Abie daɗi har hakan ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinsu.

Bayan sati biyu da samun lfyar muzaffar Muhammad Karim Ahmad ya tura case ɗinsu zuwa Nigeria tun kafin su dawo ƙasar aka fara bincike akan case ɗin kasancewar Ummie ta amsa Laifinta na cewar ita ta bashi gubar da hannunta yasa al'amarin yazowa masu yanke hukuncin da sauƙi, wahe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria.

Sosai Ummie ta fita daga haiyacinta kamar ba ita ba, tun Doguwan rigar da aka Kamata da ita sanda abin ya faru har yanzu itace a jikinta idanunta duk sun zurma sunyi ciki tamkar bana Hajiya Aisha ba mata ƴar ƙwalisa da son kwalliya a haka aka sake jefata cikin magarƙama aka rufe.

Mom sun koma gida lfy kullum.ƙara tattalin ɗanta takeyi kasancewar Zaynab sun koma makaranta ne yasa komai yazo Musu da sauƘi, komai nasa mom ce keyi da kanta wasu lokutan abin har yana bawa Abie mamaki, Baba Hajarah ma ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba santa tayi arba da Muzaffar gabaɗaya ya rame yayi duhu kamar bashi ba, kuka ta dingayi itama daga bisani kuma ta haƙura tacigaba dayi masa addu'o'in Alkhairi da kuma na samun lfy.

Washe gari da safe mom ta kira Baba Hajara tazo ta sameta a falo tareda maryam me aikin Hajiya Aisha a zaune, da girmamawa Baba Hajara ta gaida Momy sannan ta sunkuyar da kanta

Mom ta kalleta tace "Hajara ga maryam nan zaku zauna tare kuci gaba da gudanar da hidimomin gidannan don Allah seku haÉ—e kanku kuma ku zauna da juna lfy.

Murmushi Baba Hajara tayi tace "to Hajiya insha Allahu. Mom ta kalli maryam tace "ki ɗauki kayanki ki bita zata nuna miki ma saukinki. Da to Maryma ta amsa sannan ta miƙe tabi bayan Baba Hajara suka nufi ɓangarensu.

Tunda Abie ya dawo daga india be samu ya zauna ba sabida ciku2 shariyarsu da Ummie, so yake ayi abin bisa sirri don bayaso kimarsa ta taɓu a idanun al'uma dakuma na ƴan jarida kasancewarsa babban mutum kuma wanda ƙasa kejidashi. Be wani sha wahala ba me shariya ya amince da batunsa na mayar da shari'ar tasu ta sirri because this is the only thing dayake ganin ze iyayiwa ummie a rayuwarta don bayaso ta wulaƙanta a idon duniya har yanzu yana ƙaunarta a cikin zuciyarsa ƙauna me tarin yawa bata wasa ba.

Washe gari Ya kama litinin ne kuma a ranar shariyar zata fara, Mom ce ta fito cikin shigarta na alfarmar a nitse ta gama sakkowa daga sters É—in sannan ta samu Fadilah a falo tana kallon news.

Da kulawa mom ta kalleta tace "dota idan kin tashi kije ki duba yayanki sannan kisa Hajara ta dafa masa abu meÉ—an ruwa2 wanda zeji daÉ—in ci seki kai masa kinji ko?

Fadilah tayi musmushi tace "ok mom sekin dawo Abie ya shigo tun É—azo da alama keyake jira. Shafa kanta mom tayi tareda sumbatarta sannan ta fice a hanya sukaci karo da Baba Hajara ta dawo daga rabawa masu gadi da masu yankan flowers abinci.

Cikeda girmamawa suka gaisa sannan tace "to semun dawo Hajara. Da murmushi a akan fuskar baba hajara tace "hajiya yau kece da fitar sassafe?

Tsayawa mom tayi cak sannan ta juyo da murmushi tace "wllh fitar ta dole ce kotu zamu kinsan mun shigar da ƙara akan Aisha.

Take gaban Baba Hajara ya buga da ƙarfi tanaji tana gani a haka mom tayi gaba ta barta zuciyarta na dukan tara2.

Thanks 4d love sisters naga addu'o'inku Allah yabar zumunci👏

Comment
Nd
Share

Sushmah💋[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :22

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

___✍️murmushi yayi sannan yace "ngde Ummie kusan a tare suka shiga cikin gidan wanda aka ƙawata da kayan ƙwa na zamani kuma masu matiƙar tsada, miƙewa yayi Direct zuwa inda ya saba sauka idan yazo ƙasar harya kai bakin ƙofar part ɗin Ze murɗa handile ɗin ƙofar Ummie tace " idan kayi wanka ka huta sekazo daining kaci Abinci.

Da to ya Amsa mata yana me ƙara faɗaɗa murmushin dake kan Fuskarsa sannan ya kunna kai zuwa cikin haɗaɗɗen falon, bedroom ya shige tareda rage kayan dake jikinsa zuwa singlet with boxer wanda hakan ya baiyana santala-santalan legs ɗinsa, a hankali yake takawa harya isa cikin ƙayataccen toilet ɗin wanda aka wadashi abubuwan ƙyale-ƙyale iri-iri, tsayawa yayi cak yana kallon kowace kusurwa dake toilet ɗin bisa ga mamakinsa komai an sauya masashi daga waƴanda ya sani a baya zusa Sababbi, a nitse yake takawa cikin takunsa harya isa gaban wani baban Abu wanda yafi kamada bahon wanka na zamani, ruwa ya tara a cikin ƙaton bahon me ɗan zafi tareda zuba shower gel ɗin daya saba amfani dashi mallakin Companyn Olay me bala'in ƙamshi take kumfa ta cika bahon ,

Murmushi yayi me kyau tareda shiga cikin Ruwan ya zauna tareda lumshe manyan idanunsa zafin ruwan na ratsa duk wata gaba ta jikinsa, sosai yakejin daÉ—in yanda zafin ruwan ke Ratsashi ya jima a ciki daga baya ya buÉ—e ruwan ya wuce sannan ya tare wani yayi wankan ya fito. Bayan ya fito daga wankan be wani tsaya shafe-shafe kamar yanda ya sababa ya shirya cikin kayan sport marasa nauyi tareda kabbara sallar dake kansa, ya jima yana sallar sannan ya idar taredayin Azkar É—insa kamar yanda ya saba a kowace Rana.

Yana miƙewa kiran Abie ya shigo wayanshi daga yanayin ringing ɗin ya Fahimci cewar Abie ne, zama yayi daga bakin gadon dake ɗakin tareda kara wayar a kunnensa da sallama yace "Abie ya gida? Ɓangaren Abie yayi murmushi yace "lfy lau Son ya gajiyan Hanya? Ɗan shagwaɓe fuska yayi sannan yace "uhm wllh Abie a kwaita kagafa se yanzu na yi wanka tun shigowana ƙasar. Dariya Abie yayi me Sauti sannan yace "ka kula da kanka sosai I'm sure of you will do your job with full success. Muzaffar yayi murmushi yace " sure Abie insha Allah.

Mom dake zaune gefan Abie haka kawai seta samu kanta da rashin samun kwanciyar Hankali tunda muzaffar yayi tafiya, haka nan seta samu kanta da rashin Amintuwa da tafiya jiki babu ƙwari ta karɓi wayar daga hannun Abie cikin tattausan lafazi tace "Boy ya dai ina fatan kana lfy? Ɗan shafa gefan fuskarsa yayi kana yace "I'm fine mom and why your voice was so cool? "I don't know why darling I'm just feel like something is definitely going to happen to me. Pls take good care of yourself kaji yaron kirki? Sannan ka kula da makircin Hajiya Aisha ok.

Shiru yayi bece komai ba a haka suka katse wayar Abie na binta da kallon mamaki yace "why are you behave like that Hajiya Saratu? Meyasa ke bakya ƙaunar kiga an zauna lfy ne?

Yau kimanin shekaru nawa ana wannan abin ai yaci ace yanzu kun haƙura kuma kun zubar da komai kodan kwanciyar Hankalina. Cikeda karyewar zuciya mom tace "Abie bazaka gane komai ba shiyasa kake faɗar hakan, taya matar dta nunawa ɗana tsana tun yama ɗan ƙarami kayi tsammanin cewar yanzu bazata iya cutarmin dashi ba?

Nifa uwa ce Abie taya bazanyi yaƙi da duk wani me neman cutar min da rayuwar ƴaƴana ba? Kada ka manta da wacece matarka Aisha kasancewar bata taɓa haihuwaba tunda ta hafi ɗanta bezo da raiba take ƙoƙarin ganin bayan nawa ɗan har zuwa lokacin daka ɗauketa tabar ƙasar nan. Wllh nasan she can do anything don ganin ta lalata min rayuwar Ahalina amma nasan onday one time you will understand what I mean insha Allah.

Shidai Abie girgiza kai kawai yayi tareda miƙewa ya faɗa toilet tana binsa da kallo,

*******
Ɓangaren Muzaffar kuwa Ajiye wayar yayi ya fita sabida wani irin juyawa da cikinsa keyi sabida yunwa yana fita a falo ya samu Ummie tareda wata ƴar aikinta Maryam kallo ɗaya zakayi mata kasan ƴar Nigeria ce, a ƙalla shekarun Maryam zasu kai 40 tun lokacin da Ummie tabar nigeria Suka taho tare.

da fara'a Ummie ta tarbeshi suka nufi daining ita kuma Maryam ta durƙusa tana gaisheshi with so much respect, murmushi kawai ya sakin mata sannan ya wuceta ba tareda ya amsa ba Hajiya Aisha da kanta tayi sarving nashi Abincin wanda keta zuba uban ƙamshi sannan ta miƙa masa itama ta xauna ta fara zuba nata Abincin wanda keda banbanci danasa kasancewar tanada ciwon suger

Kusan a tare suka fara cin Abincin har wani lumshe ido Muzaffar keyi sabida DaÉ—in Abincin hakan ne yasa yaci sosai har ummie tayi mamakin hakan, dabida a iya sanin datayi masa bayacin abinci sosai.

bayan sun gama cin Abincin ne Maryam ta miƙe ta kwashe kayan Abincin takaisu kicin tareda gyara gurin, zama sukai a falon suna ɗan taɓa hira duk akan abinda ya kawoshi Indian wani tayi murmushi wani kuma ta kalleshi, wayarta ce tayi ƙara hakan yasa ta maida hankalinta ga wayar tareda karawa a kunnenta Tace "bayi zamuyi magana yau insha Allah komai ze kammala ba tareda anci lokaci sosai ba. Ta faɗi hakan tana satar kallon muzaffar wanda ya maida duk hankalinsa akan System ɗinta dake gabansa,
Chapter 22 · 0% Book details