← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 57

Sashe 4

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rabe ce kawai take kula dashi itace ke saka masa magani har zuwa kan abinci, kunu ne kawai ke iya shiga cikinsa sabida yanda haƙoransa suka datse.

Kullum itake zuba masa kunun a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo yana shiga kaÉ—an-kaÉ—an,
Kallo ɗaya zakayiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo yazo dashi Gidan, tun ranar da aka kawoshi gdan Laure bata ƙara leƙowa dakin ba.

A cewar ta idan masifar ta zo to ta afkawa moddibo shikaÉ—ai da Æ´arsa,

Kujifa masu karatu😂

Wasa-wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta Haka kuma ko kiwo bata zuwa, amma Sam hakan baya damunta sabda Damuwar datasa a ranta, Abinda tasa a ranta kawai shine taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau A Rayuwa. Dole tasan wata rana zasuci Ribar abinda abinda sukayi na taimakon wannan matashi

Mlm iro yazo yafi a Ƙirga kan Rabe ta dawo makarantar ayi suka da ita amma fir taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita koda Ƙofar gida Ne to waye ze Kula da wannan bawan Allahn?

Moddibo ne ya shigo Ɗakin hannunsa riƙe da wata saiwa ya mika mata yace " maza jeki tafasa Min ita ki kawo min kinji.
Da sauri ta karɓa taje ta haɗo Ƙirare ta Kunna wutar ta Dora maganin, ba'a dau lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa tareda saiwar bata sauke ba hae seda Wutar ta mutu Gaba ɗaya sannan ta juye maganin a qwarya ta kaiwa moddibo, da murmushi a kan fuskarsa ya karba yana sa mata albarka, seda maganin Ya fara hucewa moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa Masa abaki.

dikda cewa ana zubawa wani na zubewa ansamu wani ya shiga cikin nasa, bayan ya gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin, tundaga ranar
Kullum Se'an masa haka har aka shafe Tsahon wata Guda anayi amma still babu wani ci gaba. Itako Rabe bata da aiki se kuka Ta wani ɓangaren kuma ga Bala'in inna Laure, nan da nan duk tabi ta rame se hanci da idanu Kamar ba ita ba.

Sosai Abin Hakan ke ƙara Ɗagawa moddibo hankali to amma bashida yanda zeyi illa kawai yayta addu'a.
Laure CE ta Shigo ÆŠakin da sallama ya amsa mata Ba yabo ba fallasa.

A dakile tace " yame jikin? Modibo yace "Da sauƙi Alhamdulillah sannan yayi murmushi a karo na biyu yace hala fita zakiyi Nenaga kin shigo min ɗaki?

Basarwa tayi kamar batajishi tace "ae Fita zanyi dama ta rasa ta Inda zata fara tambayar sa cewar zata fita, a takice yace mata"sekin dawo Indan kinje kya gaida su Iro da Gwaggoji.

Bata amsa Shi ba tayi gaba bayan fitarta Tana sababi.

hamisu Ne Ya shigo gidan hankalinsa a matiƙar tashe yace " don Allah malam modobo kazo muje ka duba mahaifina wllh jikin nasa ne ya tashi. Hamisu ya faɗi hakan yana kuka

moddibo be Ɓata lokaciba ya fito suka wuce Gidansu Hamisun, har sun fita ya dawo yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan,
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah Ya kiyaye ta koma dakin ta zauna, zubawa matashin ido tayi ba tare da tace komai ba Nanda nan hawaye Ya fara wanke mata Fusaka cikin muryar ta fara magana Kamar haka "wai kai yaushe zaka tashi ne?shin kasan yanda mukeji a ran mu Duk a gameda kai? Dan Allah ka tashi ko hankalin babana ze kwanta Na roƙeka!!

Ta jima tana suru tanta kamar wata zararriya sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta fukarta dik tayi Ja idanunta Duk sun kumbura abin ka da farar mace....

Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta,
A hankali matashin ya fara motsa hannunsa daƙar ya Iya daga hannun sa ya maidashi Ƙirjinsa Sabida tsabar Azabar dayakeji a jikinsa,

A hankali ta buɗe idanunta sabida jin da tayi kamar motsi yasa ta bude idanunta daƙar ta maida kallon ta gareshi, Nan da nan ta miƙe zaune sosai ta Ƙara buɗe Manyan idanunta sosai Tana mamaki
ya akai hannunsa ya koma Ƙirjinsa? Tambayar da take mata yawo Kenan a zuciyarta.

A nitse ta maida kallonta kan fiskarsa Ta ƙura masa idanu kamar meso gano wank abu a taredashi, ta jima tana kallon sa kamar bazata dena ba kamar a mafarki taga yana Ɗan motsa idanun sa, Ƙara zaro idanunta Tayi waje cike da mamaki Ta miƙe tsaye still idanunta akansa,

A hankali ya fara bude Idanunsa har ya gama buɗesu gaba ɗaya Yana me ƙarewa ɗakin kallo harya dauke manyan idanunsa a kan fuskar Rabe,
A firgice ya fara Ƙoƙarin tashi yana so yaja Da baya sabida Yanda ya tsorata da Ganinta.
Ƙara Ya saki sabida wani Irin azababben zafi dayaji a gadon bayan sa Har zuwa saitin gefan cikinsa na Dama, bashiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi, da sauri Rabe ta sake matsowa kusa dashi sosai sannan ta fara magana cikin harshen fulatanci take cewa "kayi a hankali sabda jikin ka akwai rauni Sosai!

Tunda ta fara magana yake kallon Yanda take motsa bakinta har ta kai Ƙarshen maganar. dikda cewa be fahimci abinda take faɗa ba hakan be hanashi Ƙare mata kallo ba, kyakkyawa ce Sosai ta gaban kwatance don tafi kamada irin larabawan yankin ƙasar Misira, tana gama maganar ta sakar masa murmushi Wanda seda tasa gabansa ya faɗi ya ɗauke idonsa da suri daga barin kallonta

mikewa ta fita daga dakin ,
Tana fita dakin ta nufaa ta ÆŠakko wani rufaffen kwano Wanda Moddibo ya bata kafin ya fita sannan ta dawo ta sake zama dab dashi Tana murmushi a karo na biyu sannan tace Dashi " zaka iya tashi kuwa ?

Kura mata ido yayi cikeda rashin Fahimtar abinda take faÉ—a. dataga be gane me take nufi ba setai mai nuni Da hannu alamar ya tashi,
A hankali ya Fara yunƙurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa ya Dole yasa ya koma ya kwanta, alama tayi masa da hannunta kan cewar ya sake ƙoƙartawa Amma kuma setaga bashida niyar yin hakan.

mikewa tayi sannan ta koma bayan sa Ta fara ƙoƙarin dagoshi,,

cike da mamaki yake kallonta tare da Girmama Ƙarfin hali irin nata, jibeta fa 'yar qarama da ita wai zata Ɗagashi, lallaima yarinya nan Ta gama raina masa Hankali ya faɗi hakan a zuciyayarsa, ba zato yaji ta cakume shi Da dukkan ƙarfinta ta fara giji-gijin ɗagashii, Wata uwar Ƙara Ya saki sabda zafin dayaji na ciwon dake bayan sa, bata damu da ihun dayeke ba har seda ta zaunar dashi,
Daƙar Sannan ta zube ƙasa tana maida numfashi.

Dakyar ya Iya ɗago idon sa da suka fara canza kalah dan azaba ya kalleta lokaci Ɗaya itama ta dago idonsu ya sarƙe cikin na juna.

gabanta ne ya Yanke ya fadi da sauri tayi Ƙasa da idonta, a nitse Takai hannunta kan kwanon da ta Ɗakko a daki ta buɗe, fura ce da nono Wadda aka zugawa uban suga ta Ɗiba ta miƙa msa Bakinsa alamar yasha, sarai ya gane nufinta a hankali ya fara Ɗago hanunsa amma kuma seya kasa, ya jima yana kallon ludayin sannan ya maida kallonsa kanta Batareda ya karɓa ba.

Tambayar Dake yaWo s kansa itace "wai shin inane nan?

"Kuma wannan yarinyar wacece ita?

"Waze tambaya ya bashi amsoshin wannan tambayoyi nasa?

Data ga bashi da niyar bude bakin ne seta sake miqa masa ludayin har yana taba lips dinsa , sa'a sannan ya dawo daga duniyar tinanin daya afka, a nitse ya buÉ—e bakin ya fara seeping Furar a hankali, se kuma ya kauda kansa da sauri kamar Wanda ya tina wani abu,
Daqar ta samu ta lallabashi ya sha sosai.

Bayan ya gama sha ne ta ÆŠakko masa maganin sa shima ta bashi yasha , tunda ta Fara bashi maganin yake mamakin yarinyar
Badan komai ba se yanda take Da zafin nama a komai nata, ƙoƙarinta ya zarta na shekarunta dubada yanda taketa dawainiya dashi, harga Allah ya jinjinawa jarumtar ta matiƙa.

tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta yana kwanciya moddibo ya shigo ÆŠakin da sallamar da gudu Rabe ta nufeshi ta rungumeshi tana fadin " baba ya tashi wllh ya tashi,
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin Farin ciki ba kaÉ—an ba.

Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi yace" to yanzu kuka ya Ƙare Kenan ko?
Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya.

Tun shigowar moddibo matashin yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta rungumeshi, se kallon su yake cike da burgewa da alama mahaifin tane ya fada a zuciyar sa, sabda suna bala'in kama da juna!

Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :6 -7_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️A nitse moddibo ya Ƙarasa kusa da matashin ya sunkuya da murmushi Kwance a kan fuskarsa yace "sannu da jiki Yaro kashe doguwar jinya.

Cikin harshen fulatanci moddibo Yayi maganar.

ido kawai matashin yake bin moddibo dashi Batareda yasan abinda yake faɗa ba. Kallon Rabe moddibo yace "da alamafa bayajin abinda muke faɗa. Ya ƙare maganar da damuwa akan fuskarsa

Itadai batace komai ba ta zuba musu idanu kawai tana kallonsu

Koda ya fahimci matashin baya gane abinda yake faɗa sabida banbanci yare se dabara ta faɗo Masa ya kalli matashin Cikin kwaɓaɓɓiyar Hausarsa yace "Shannu yaro ya shikejin ƙarfin jukin naki?

Matashin ya bude baki da nufin ya amsawa moddibo amma sedai muryanshi bata fita sosai sabda mura data kamashi Yace "Alhamdulillah da sauki.

A nitse moddibo ya fara magana kamar haka
"Yaro nasan zuciyarka a cike take da tambayoyi akan mu, haka
Kuma nasan zakaso kasan meye dalilin zuwanka wannan gurin? To magana Ta gaskia itace ina Kan hanyar dawo wata daga kiwo ne Allah ya hadani dakai A cikin mayuyacin hali kana kwance cikin jini !!
Haƙiƙa duk abinda Alla ya hukunta shiyake faruwa shiyasa ma har nabi hanyar dana Daɗe amma da Allah ya Ƙaddara haɗuwarmu dakai se Gashi ya nufeni da bin hanyar Duk dan na ceci Rayuwarka.
Chapter 4 · 0% Book details