← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 57

Sashe 7

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙasaice take takowa harta ƙaraso inda ƴan jaridar suke ta tsaya daga gefan Dattijon tace "duk wanda keda burin yiwa Mahaifina tambaya toya dunƙuleta a guri guda ya faɗeta don bamuda lokacin ɓatawa, sannan ta kalli Mahaifin nata tayi murmushi tace "Abie ya kamata kayi magana dasu koda kaɗan ne.

Cikeda ƙosawa ya dubeta yace "Fadilah I can't say anything about my son at this moment, please tell them to leave Don Allah ya faɗa yayin da aka buɗe masa mota ya shiga sukabar harabar gurin zuciyarsa a cike tab da kewar Ɗansa.

*_Thank yo so much my dearest sister's, wllh har zuciyata nakejin dadin comment ɗinku akan wannan littafin, ngde sosai da qaunarku gareni sonso fisabilillah❤_*

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page : 10 - 11_*

*_Naji qorafin wasu daga cikin masu bin wannan littafin kan cewar typing Error yanayin yawa, to magana ta gaskiya sedai ince kuyi haquri dani a haka amma maganar Editing kam bazan iyayi muku shi ba, sabida a kwai abubuwa masu yawa dake gabana a halin yanzu. Ina muku sonso Fisabilillah duk masu bin wannan lottafi 🥰_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

____✍️Sam ba haka Fadilah taso ba taso Ace Abie yayi magana da ƴan jaridar a ƙalla ta samu Sunanta itama ya ɗagu a duniya kamar na YayantA Muzaffar, tsaki taja lokaci guda kuma ta faɗa motar dake bayan ta Abie sukabar harabar Companyn

A cikin wata ukun da suka shuɗe na ɓatan MUZAFFAR ABDULWAHAB ABDULLAH THE C.E.O OF ZAFAR ENTERPRISES, ba ƙaramin girgiza Al'uma abin yayi ba abinka da masu hannu da shuni duk sanda ka kunna Redio da gidajen talabijin koda yaushe zancen akeyi tareda yaɗa hotunansa a shafukan sada Zumunta, koda yaushe zancen akeyi tamkar baza'a dena ba amma still babu wanda yaji labarin sa kokuma wata ƙwaƙƙwarar magana a kansa.

MAITAMA WUSE II ABUJA

Unguwace data haɗa manyan Ginagine na alfarma hakakuma wadda aka ƙawata da abubuwa dayawa na jin daɗin Rayuwa a gurin, duk wanda kagani a gurin tofa yaci ya tara dukiya ne ba kaɗan ba, a haka motocin daƙe ɗauke da tambarin Sunan Alhaji Abdulwahab Abdullah suka sulalo cikin Unguwar suna masu tsala gudu, a gaban wani tangamemen gida suka tsaya lokaci guda kuma suka zabga uban horn Get ɗin da kansa ya wangale kansa sannan suka danna hancinan Motocin zuwa cikin babbar harabar gidan wadda taji kayayyakin ƙawa na ban mamaki.

Fitowa sukai da Sauri Guards ɗin suna masu Azamar buɗewa me gidan nasu ƙofa ya fito, Direct ƙofar dazata sadashi da maine Perlour ɗin dake gidan ya nufa still damuwa kwance akan Fuskarsa, Hajiya Sakinah ce zaune kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman manyan Royal chairs ɗin dake falon hannunta ɗauke da Rumote tana kallon abinda ke faruwa a duniya, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci tana cikin babban tashin hankali mara misaltuwa, da hanzari ta miƙe ta nufi me gidan nata idanunta na shirin kawo ƙwalla tace "Abie har yanzu babu wani labari akan Muzaffar?

Kasa ce mata komai yayi sabida damuwa lokaci guda ya zube akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon yace "har yanzu babu wani labari Sakinah wllh inaji a jikina tamkar wani babban lamari ya faru da yarona! Kullum bana iya bacci sabida tunanin Halin dayake ciki, jiya naje mun zauna da IG akan lamarin yace zasu ƙara tsaurara bin ciki wllh Hajiya Sakina tabbas nima kuna dabda Rasani muddin Ba'aga Muzaffar ba.. Ya faɗa yana dafe kansa da a lokaci guda sabida wani irin Sara masa da kan yayi

Ƙwalla ce ta taru a idanun Hajiya Sakinah lokaci guda kuma suka zubo sannan ta zube a gaban Abie tace "Haba Abie kaifa musulmi ne ya kamata kayi imani akan dukkan abinda Allah ya aiko maka, muzaffar fa ba ɗanka bane kaikaɗai nima kaina ɗana ne amma meyasa kakeso ka dinga nuna gazawarka a gabana ne shin baka tunani akan tawa damuwar ne?

Kasa bata Amsa yayi har Fadilah ta shigo Falon kanta tsaye ta zauna daga gefan Abie batareda tace dasu ƙala ba. Wata uwar Harara Hajiya Sakinah ta sakarma Fadilah Sannan tace "waike meyake damun tunaninki ne Fadilah?

"wannan wace irin shiga ce haka sekace É—iyar Kafurai? Har zuwa wani lokaci zaki É—auka a haka kafin kiyiwa kanki faÉ—a a Rayuwarki?

"kai Momy Don Allah to meye aibun shigar tawa ?

"Uwarki ce aibun ai, nace Uwarki ce aibun Fadilah. Momy ta katseta ta hanyar faɗar hakan sannan ta ƙara da cewa "bazance komai ba a kanki tunda Allah ma sheda ne akan irin tarbiyar dana baki, yanzu ke don Allah ko kunya bakiji ba Ace ɗan uwanki namiji Guda ɗaya tilo yau an nemeshi an rasa tsahon wata huɗu kenan amma ke kina nan kina yawo a gari da shigar ƴan iska?

"anya kuwa Fadilah Rayuwa zatayu miki a haka kuwa?

Miƙewa Fadilah tayi tana tura baki tabar Falon tana faɗin "aini dama an daɗe da tsanata a gidan nan kowa yafi fifita Yaya Muzaffar akan kowa da ace nice ma na ɓata I'm sure of that wllh babu wanda ze damu irin haka daga ke har Abie ɗin. Ta faɗa tana biga ƙofar glass ɗin dake falon

Da ido kawai iyayen nata suka bita batareda iya furta komai ba.

GYAMBU RUGAR ARÆŠO

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau Matashin ya cika wata Uku cur a Gidan moddibo cikin ikon Allah ya samu sauqi sosai, a É—an watannin daya shafe taredasu yasa har ya canzawa Modibbo matsayi daga wanta ya taimaki Rayuwarsa zuwa muhalli na Uba, tabbas moddibo mutum ne na musamman wanda ya kamata ya bawa muhali mafi daraja daga zuciyarsa, sabida Samun irinsu a wannan lokacin abune mawuyaci

A ɗan zaman dayayi dasu ya ƙara ilimi akan zamanta kewar Rayuwar duniya musamman ta ɓangaren mu'amala da jama'a

Rabe ce ta fito ɗauke da babbar Fanteka zataje ɗebo Ruwa, a zaune ta samu Muhammad Ali ya zubawa Shanun dake cikin garkensu idanu tamkar me nazari akan wani abu, harta ƙaraso gurin besan tazo ba hakanne yasa ta ɗauki wani ƙaramin sanda ta jefa masa.

Miƙewa yayi da Sauri yana kallonta sannan ya Haɗe Rai yace "what's that does mean? Tsaki yaɗan ja sabida sanin ba gane abida ya faɗa take ba common Hausa ma wani abun se yayi da gaske sannan take Fahimta balle kuma turanci sannan yace "meye haka ?

Dariya tayi har seda beauty point É—inta suka lotsa sannan tace "kawai na gwadaka ne don na gane ko kanada tsoro

Turo baki yayi yana kallonta sannan yayi murmushi yace "ni sam ba matsoraci bane I'm a hero. Ya faÉ—a yana É—aga mata hannayensa duka biyu Sama

Dariya ta sakeyi sannan ta ƙurawa bayan sa idanu batareda tace dashi ƙala ba. Ɗagowa yayi yana kalonta yace "meye kike kallo haka?

ÆŠaga kafaÉ—unta tayi sannan tace " ba komai kawai Gizo-Gizo nakuma shaquwa na gani a kan rigarka ta baya.

Ihu ya saka yana tsalle lokaci guda kuma ya faɗo kanta suka faɗi ƙasa still yana zuba mata ihun likaci guda kuma ya ƙanƙameta yana Rintse idanu.

Tureshi tayi da Sauri lokaci guda kuma ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta ɗauki Fantekarta ta nufi Hanyar Rafi tana me ƙyalkyala masa dariya.

Tsaki yayi lokacin daya kalli gwiwar hannunsa yaga yaji ciwo kaɗan jini na fitowa kaɗan-kaɗan abinda da Ajebo 😂

Bayanta yabi fuskarsa a ɗaure treda ƙudurtawa kansa cewar seya Rama abinda tayi masa, a haka har duka ɗebo Ruwan suka ɗauki hanyar komawa gida, tafiya kawai suke bame cewa wani ƙala a tsakaninsu har suka iso hanyar data raba Rugarsu Rabe da kuma tasu Bamanga.

Lokaci Guda sukaga an kewayesu, Bamanga ne dashi da jama'arsa ko wanne hannunsa É—auke da Sandar gado lol

ÆŠaure Fuska Rabe tayi tana kallon Bamanga cikin harshen fulatanci tace "meye haka zakuzo ku tare mana hanya kamar wasu Æ´an Daba?

Kallon Tsaf Bamanga yayi mata Sannan yace "yanzu ke har kinada bakin magana akan na tareku? Yau kwa nawa kenan ina zuwa gidanku kullum seki ce min in tafi baki da lfy Ashe wannan KaÉ—on shine ciwon dake hanaki fitowa gurina ? Bamanga ya faÉ—a yana nuna Matashin dake gefan Rabe a tsaye yana kallon ikon Allah.

A ƙarshe da abin ya isheshi Fantekar Ruwan yasa Hannu a kanta ya ɗauke sannan ya kalleta yace "if you handle the game with this guy you will meet me at home ya faɗa yana barin gurin gabaɗaya

Be jima da tafiya ba Rabe tabi bayansa da gudu lokaci guda Su Bamanga suka bita da idanu baki a Sake.

A iya ɗan wannan lokacin da suka kwashe tare da Rabe za'a iya cewa a kwai shaƙuwa metarin yawa wadda ta samu gurbin shiga tsakanin SuRabe sedai bazamu fassara shaƙuwar da sunan syayyah ba, sedai kawai mu kirata da sunan ƴan uwantaka sabida a tsarin matashin babu batun soyayya a lamarin sa.

Wannan shi bahaushe ke kirada sabo tirken wawa, a haka suka shafe kwanaki a ƙarƙashin muhali guda ɗaya

Sosai yakejin daÉ—in Rayuwar gurin sedai har cikin Zuciyarsa yana kewar Mahaifinsa da mahaifiyarsa, idan tunanin ya isheshi se kawai yabi Rabe su tafi kiwo, sosai yakejin daÉ—in hakan har zuciyarsa

******
*BAYAN SATI BIYU*

Washe garin da safe moddibo ya gama haɗa masa komai nasa wanda ya tsinceshi dashi saɓanin Rigarsa wanda jini ya ɓata da kuma yagewar dake jikinta yasa moddibo ya jefar tun a washe garin Ranar daya tsince shi, Wata Rigar Farin Saƙi irin tasu ta Fulani ya Ɗakko masa tareda miƙa masa yace "karɓi ka sanya a jikin ka tare da wandon shaddar taka na tabbata wata rana a ƙalla idan ka kalli Rigar zaka tuna damu.

karɓar rigar matashin yayi ya sanya a jikinsa lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga Moddibo, ba ƙaramin kyau Rigar tayi masa ba domin kuwa tsayawa faɗin irin kyan datayi masa ma ɓata lokaci ne
Chapter 7 · 0% Book details