← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 57

Sashe 44

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ikon Allah da hikimarsa mutanan India suka iso Nigeria lfy, tun kafin jirginsu ya iso garin na Abuja Abie ya turo Guards ɗin muzaffar ɗin da wasu danƙara-danƙaran Expensive motaci ƙirar companyn Ford's masu shegan kyau suka iso suna jiran saukar jirgin.

Jirgijn na sauka seda suka shafe kimanin 15 munites sannan matattakalar jikin jirgin ta fito, a hankali muzaffar dake sanye cikin wata shaiɗaniyar baƙar suite wuluk da ita wadda ta mugun karɓan jikinsa kamar dinshi akayita, sosai fuskanshi tayi wani irin haske sabida ramar dake taredashi, yanayin yanda read lips ɗinsa ya wani irin tattare kaman ya shafa Janbaki ba ƙaramin kyau hakan ya ƙarama fuskan nashi ba. Bayansa kuma moddibo ne biye dashi sanye ciki wata farar jallabiya mallakin companyn Emraty Fara tass da ita, kallo daya zakayi masa kaga zallar kamalar dayake da ita.

A haka suka Ƙaraso gaban motocin guards suka buɗe musu ƙofa bayan sun zuba kayansu a booth ɗin motar sannan sukaja motocin cikin jerin gwanonda suka saba gwanin ban shi'awa.

Tunda suka shiga motar zuciyar moddibo ke cike taf da mamakin matsayi da kuma gata irin na Muzaffar take yaji zuciyarsa ta amsa duk a lokaci guda.......

Comment
And
Share

Sushmah✍️
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_WRITING BY:CHUBAÆŠO_*

NOT EDITED

____✍️ Cikin nutsuwa motocin ke tafiya har suka samu nasarar isowa cikin Maitama, duk inda motocin suka sulala Sedai kawai kaga moddibo na baza idanu yana kallon ƙuduran Allah da kuma hikimarsa, a ransa kuma yana me girmama ƙwarewar maginan da sukai gine-ginan dake cikin garin a iya tsahon Rayuwarsa yayi yawo sosai tundaga kansu ƙasar Niger dadai sauransu amma betaɓa cin karoda guri mekyau irin Abuja ba kodan a daji ya sabayin Rayuwa oho🤷‍♀️

A haka suka iso ƙofar kantamemen gidan Me kamada aljannar duniya babu abinda ya ɗaurema Moddibo kai irin ganin yanda Get ɗin ya buɗe kansa da kansa ba tareda kowa ya taɓashi ba nan take yaji wani irin tsoro ya tsigawa zuciyarsa da gangan jikinsa, Haka suka kunna kai zuwa cikin gidan kallo ɗaya zakayiwa Muzaffar ka fahimci yana cikin Farin ciki dukda irin damuwar dake kwance a cikin ransa sam hakan be hanashi baiyana farin cikin ganin Ahalinsa ba.

Hannun Moddibo ya kama ya riƙe cikin nasa musamman daya Fahimci yanayinsa ya sauya daga wanda suka baro airport dashi suwa wani, Ajiyar zuciya ya sauke sannan yay murmushi yace "pls baffa feels free with us don Allah we are all family kasa a ranka nan ma gidanka kazo. Ya faɗa yana matsa hannun Baffan cikin nashi

GabaÉ—aya Ahalin gidan suna farfajiyan gidan suna jiran fitowansu Except Ummie dake khitchine tana shiyawa É—an nata girki na musamman don tarbarsa.

A wannan rana babu wanda beyi farin ciki da dawowar muzaffar É—in ba, bayan sun iso sun huta ne muzaffar ke sanar da Abie irin karamcin da moddibo yayi masa a lokacin dayake dabda rasa Rayuwarsa, sosai Abie ya nuna jin daÉ—insa tareda sanyawa a É—auki modÉ—ibo a kaishi masauki na musamman wanda aka qawata da karan alatu na jin daÉ—in rayuwa iri-iri.

Tabbas moddibo ya fahimci cewar muzaffar ba mutum bane gamagari kamar sauran yara ba, yaro neshi É—an gata kuma É—an asali da ga mutane masu tarin É—ukiya a haka ya kwana ya hantse a cikin wannan aljannar duniyar, sedai dukda hakan zuciyarsa naga tunanin Æ´arsa guda É—aya tillo wato Rabe.

Moddibo ne zaune qasan Makeken kafet É—in dake hamshaqin falom yana daure boronsa (jaka) da alama shirin tafiya gda yake, muzaffar ne ya shigo dakin da murmushi Kwance a kan Kyakkyawar fiskarsa yace " baba. se kuma yayi shiru da sauri ya qaraso Cikin falon inda moddibon ke zaune yana É—aure jakar kayan da suka dawo dashi daga india, cike da damuwa Ya kalleshi kaman ze sakin masa kuka yace " baba badai har ka fara shirin tafiya ba?

Murmushi moddibo yayi irin nasu na dattijawan qwarai yace "to yaro me kuma zan tsaya jira? Tunda Allah ya amince maka ka zama silar ceton Rayuwata me kuma zan zauna jira wanda ya wuce in koma ga iyalina?

Shiru Muzaffar yayi a ransa yanajin kewar moddibon ta fara addabarsa tun kafin ma ya tafi, a hankali ya buɗe jajayan laɓɓansa zeyi magana middibo ya rigashi ta hanyar cewa "zuwa yanzu Nasan Gabaɗaya jama'ar garinmu da kuma iyalina sam basa cikin kwanciyar hankali duk sabida tunanin irin halinda nake ciki Musamman ma Laure nasan Setafi kowa damuwa, da Ace ma Rabi'atou na tana tana gida tashin hankalin dazata shiyaga seyafi na kowa sabida ban taba tafiya me Nisan Irin wannan shafe watanni bana tareda ita ba, sbda tinanin Irin halinda zata shiga idan bana nan ɗin, Se gashi kuma yanzu babbar ƙaddarar Rabuwa ta gifta a tsakanin mu ba tareda mun shiryawa hakan b.......!

Wasu siraran Hawayene suka zubo masa dole ya kasa qarasa maganar yay shiru, Sunkuyawa muzaffar yayi tareda dafa kafaÉ—unda cikeda zallan kulawa yace "kayi haquri baffa amma komai muqaddari ne daga Allah kamar yanda qaddara tayi nasarar rabaku da ita isha Allah wannan qaddarar ce zata sake zama silar haÉ—uwarku, jikina yana bani cewar a duk inda Rabi'atou take sam bata cikin yanayi na rashin daÉ—i sabida muddin hawayenta suka zuba to wllh senaji haka a cikin jinin jikina so Dont worry Baffa insha Allah komai ze wuce.

Kasaƙe Moddibo yayi yana kallonsa a ransa yana girmama lamari irinna muzaffar ɗin, sam bashida yanayin izzar Da yaran Da iyayensu suka tara musu dukiya suke da ita, Muzaffar he's a nice person and social komai nasa da sauqi yake ɗaukarsa tamkar ba magajin attajirin Mamallakin companonin nan Ba Alhaji Abdulwab Abdullah ba.

KafaÉ—arsa moddibo ya dafa still yana hawaye yace "Allah ya albarkaci Rayuwarka yaro haqiqa iyayenka sunyi sa'ar haihuwa da suka haifi É—a kamar ka.

Murmushi kawai muzaffar yayi ba tareda yace komai ba, ajiyar zuciya yaÉ—an sauke sannan yace "da inada ikon hanaka tafiya wllh Baffa danayi hakan amma kum...... "Kada ka Damu yaro ai yanzu mun riga mun zama ahalin juna don haka babu me iya yanke wannan alaqar.

Kamar muzaffar zeyi kuka yace "yaushe ne tafiyar taka Baffa?

"Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda Tunda Allah ya azitani da lfyar dana daÉ—e bani da ita Wanda ta kasance kaine silar samuwarta. ya Qarashe maganar da murmushi a Kan fiskarsa

Murmushi muzaffar yayi Yace "don Allah baffa ka dena cewa hka nimafa ka ceci tawa rayuwar don haka nizan gode maka kuma har duniya ta gushe bazan taɓa dena godewa likitan gargajiya irin Baffa na ba. Ya faɗI hakan yayinda yake faɗaɗa murmushinsa gareshi.

sosai moddibo yaji DaÉ—in maganar muzaffar ÆŠin , nan dai ya shiga yi masa nasihu masu Matiqar shiga jiki, sosai
Jikin muzaffar Yayi sanyi sbda nasihun da moddibon yayi masa, a ransa seyaji dama moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo komaiba ya nufi hanyar fita Daga falon zuciyarsa a matiqar dagule.

Murmushi moddibo ya kuma yi A karona biyi sbda ya fahimci muzaffar ÆŠin fishi yayi sbda yace ze tafi gobe,
Miqewa yayi shima suka nufi masallacin tare, daidai lokacin da Ummie ta loqo ta windown falon ta Don ganin fitarsu sedai sam bataga fuskokinsu ba se bayan su Data hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining.

Koda aka idar Da sallan muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Abie ma ya fito, kusan a tare suka jera suna tafe suna hira anan muzaffar ke shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Abie ma yaji ba dadi sbda yanda ya saba dashi a kwana dayan da sukayi a gida kamar sun shekara da sanin juna, Shi kansa Abie ɗin yana buqatar ace sun samu lokaci da moddibo Donsi tattauna sosai akan wasu abubuwan na daban waƴanda suka shafi rayuwar Moddibon da kuma abubuwan dake faruwa a cikin garuruwansu na fasa qwaurin da ƴan bindiga daɗi suke musu ta hanyar yiwa yaransu qanana fyɗe kuma su qwace musu dukiyoyinsu, kodan darajar ceton Rayuwar ɗansa tilo dayayi shikuma dalilin wannan ya qudurtama kansa cewar tabbas seya taimaka musu koda kuwa hakan yana nufin ze rasa wani ɓangare na dukiyarsa ne gabaɗaya.

Har a cikin Ran Abie yaji cewar yana matiqar qaunar Moddibo sabida Yamada sauri saboda mutane Kuma ga kirki, gashi da haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da dadin mu'amala Ta kowani fanni,
Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Se Zuciyarka ta qaunace shi Koda baka shiryawa hakan ba Sbda dattijon a kwai shiga rai,
Suna shiga Falon da aka saukeshi Abie Ya kalli moddibo yace" tunda gobe zaka tafi don Allah Meze hana Kazo Muje bangarena Muci abincin dare tare Dakai?

Shiru moddibo Yayi kamar bazece komai ba sannan ya É—ago yace "ina me baka haquri akan wannan al'amari dakazo min dashi wllh bazan iya zuwa ba idan naje tamkar ka takurani ne.

Duk yanda Abie yayi dashi amma sam yaqi amincewa Dole ya haqura badan yaso ba yayiwa moddibo seda safe, sannan ya wuce bangaren Ummie.

fita Muzaffar yayi dan dakko musu abinci a bangaren Ummien sa , be jima ba ya dawo dauke da manyan food flasks guda biyu se Zaynab dake Biyeda bayan sa hannunta dauke da flat da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani Babban flet Wanda ke dauke da kosilo Wanda yaji Uban qwai da bama ansa wata fara leda an rufe farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flet din, da sallama ta shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa. da kulawa ya amsa mata tareda sakin fuskarsa dukda irin halinda zuciyarsa take ciki na kewar É—iyarsa, Jikinsa a mace ya tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace "Sunana Zaynab.

Murmushi moddibo yayi sannan yace" Ashe mata tace da kanta. dukansu suka sa dariya sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su A ranta tana mamakin kyau da cikar zati irin na moddibo.
Chapter 44 · 0% Book details