← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 57

Sashe 26

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A harabar gidan suka samu Edyan yana ganinsu ya nufi wata zabgegiyar Renge Rover ɗinsa baƙa wuluk da ita se faman ɗaukar idanu takeyi da hanzari guards ɗinsa suma suka fara ƙoƙarin tada motocinsu dole hakan yasa Edyan ya fito ya kallesu yace "no base kun bini ba zanje ni kaɗai Hospital zanje. Cikeda girmamawa ɗaya daga cikin guards ɗin yace "amma ranka shi daɗe Me girma IG fa yayi mana kashedi akan barinka kai kaɗai ka fit........."tunda ni jariri ne ko ? Edyan ya faɗi hakan with so much angry.

A ladafce suka haɗa baki suna faɗin we are sorry sir. Tsaki yaja sannan ya buɗewa mom back seat na motar sannan ta shiga ya rufe zeeyadah kuma ta kame a front seat, harya shiga motar be ce da kowa ƙala ba a haka yaja motar suka fice daga gidan gabaɗaya Zuwa Asbitin, cikin min tunan da bazasu gaza 15ba suka iso babban madaidaicin private hospital ɗin wanda aka qawata da kayan qawa iri-iri tamkar ba Asibiti ba. A notse ya faka motar cikeda ƙwarewa sannan ya fito ya zagayo ya buɗewa mom side ɗinta ta fito tana murmushi sannan ya rufe motar.

Sakkowa zeeyadah tayi tabi bayansu suka ƙarasa cikin harabar Asibitin, Direct office ɗin Dr. Mujaheed suka nufa, bayan sun shiga da sallama Edyan ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan suka gaisa da mom da zeeyadah, nan Edyan yake tambayarda yame jiki?

Ɗan murmushi Dr. Mujaheed yayi sannan yace "jikinta da sauƙi sedai tun jiya data farka take mana kuka kuma taƙi bari kowa yazo kusa da ita munyi2 taci abinci amma taƙi sam. Cikeda damuwa Edyan yace "kana nufin har yanzu babu abinda tasa a cikinta se kuka datakeyi?

Dr. Mujaheed yace "sure.

Da sauri Edyan ya miƙe ya bar office ɗin ya nufi ɗakin da aka kwantar da itan, Da sallama ɗauke a bakinsa ya tura ƙofar tareda zura gaba ɗayan jikinsa cikin ɗakin sedai sam be saki ƙofar ba. A nitse yakebin kowace kusurwa na ɗakin da kallo harya sauke manyan fararan idanunsa akanta, gabaɗaya dukta takure guri guda tareda haɗe kanta da gwiwarta bakajin sautin komai sena kukanta.

A nitse ya fara takowa cikin takunsa harya ƙaraso bakin gadon bata ɗago ba hakan ne ya bashi damar ƙare mata kallo tun daga kan yatsun ƙafarta har zuwa kan manyan2 kitso biyun dake kanta ba wanda yaci uban datti gashida mugun tsayi na ban mamaki, sedai dukda hakan bazaka kasa gane irin kyanda gashin nata yake dashi ba abinka da Fulanin Usuli.

A hankali ya miƙa hannunsa ya dafa kafaɗunta a wani irin mugun furgice ta ɗago idanunta duk sun caɓe da hawaye taja baya da sauri tan me ƙara ƙanƙame jikinta still her eyes is on his handsome face. Cikin harshen Fulatanci ta fara magana kamar haka " ka matsa kusa dani banson Rayuwa a cikink........ Wani irin kuka ne ya taso mata dole yasa tayi shiru.

Jikinsa ne yay masifar sanyi dukda besan abinda take faɗi ba don haka ya sake miƙa hannunsa ze taɓata yace "its OK dear but plz stop crying don Allah kodon sabida condition ɗinda kike ciki na rashin fly plz Cutie girl. Ya ƙare maganar yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta

Ƙura masa idanu ita tayi tana kallonta a ranta tana aiyana cewar "komai nasa irin na hamma zafar har yanda yake magana yana saka wani yare na daban, sedai gashin kansu da yanayi na ƙirar jikinsu ne sam ba ɗaya ba wannan sam be kai Hamma zafar hasken fata ba seda shima ba laifi yana da kyau sosai na nunawa sa'a. Haka kawai taji zuciyarta ta amince dashi kuma ta yarda dashi, batace masa komai ba tasa hannunta ta janyo takalman robarta dake gefanta ta rungume a ƙirjinta tareda zubawa flet ɗin abincin da aka ajiye mata tun ɗazu bataci ba idanu.

Murmushi yayi yace "zakici ?

Turo baki tayi batace masa komai ba, ɗakkowa yayi ya miƙa mata flet ɗin yana murmushi jada baya tayi tana kallonsa alamar ma ita tsoro kwanon Abincin yake bata, riƙewa yayi a hannunsa sannan ya kalleta yace " ki lura da kyau ki kalleni babu abinda kwanon abincin zeyi miki ok. Still tana kallonsa sannan ya ɗebi abincin da cokalin kaɗan yakai bakinsa yaci sannan ya miƙa mata yace "oya eat.

Maƙe masa kafaɗa tayi tana shirin fashe masa da kuka yace " hay look don't cry please just eat. Taɓe baki tayi tana wani mirza ido. Ganin dayay bata da niyan karɓa ne yasa ya matsa dabda ita ya fara bata abincin ta cokalin tanaci tana zubarwa a haka haraya gaba bata ya ajiye flet ɗin yace "barin je na dawo ko?

Da wani irin mugun sauri ta diro daga gadon ta riqe hannunsa gam tana hawaye a haka su mom da Dr. Suka shigo ɗakin. Bayansa ta koma da sauri tana ɓoyewa alamar batason mutane sosai

Murmushi mom tayi tana kallonta cikeda so sannan ta maida kallonta ga Edyan tace "Dr. Ya bada takaddan sallama se kuma drugs daya rubuta kuma suma mun siyo mata yanzu gida zamu wuce kawai. Murmushi kwai yayi yace "ok mom muje. Ya faɗa yana riƙe da hannunta

Har sunkai ƙofa ta fizege hannunta ta dawo ta ɗauki wannan jakar da Moddibo ya bata sannan ta dawo ta riƙe hannunsa suka fita.

Wajen shiga mota ba ƙaramar ɗirama akayi da ita ba ihu ta dinga zuba musu seda Edyan yay dagaske sannan ta yarda ta shiga suka tafi gida gabaɗaya, duk a tsorace take kallonsu kawai take itako zeeyadah gabaɗaya tausayin yarinyar ya gama cika mata zuciya.

India🇮🇳

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah a ɗan wannan tsukun lokacin abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa dadi, a ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi dukda irin ɓarnar da poison ɗin yayi masa a ciki, ada sam baya iya zama amma yanzu kam yana iya zama da kansa harma yayi tafiya koda bame tsaho bace. Sosai hkaan yawa Su mom da Abie daɗi har hakan ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinsu.

Bayan sati biyu da samun lfyar muzaffar Muhammad Karim Ahmad ya tura case ɗinsu zuwa Nigeria tun kafin su dawo ƙasar aka fara bincike akan case ɗin kasancewar Ummie ta amsa Laifinta na cewar ita ta bashi gubar da hannunta yasa al'amarin yazowa masu yanke hukuncin da sauƙi, wahe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria.

Sosai Ummie ta fita daga haiyacinta kamar ba ita ba, tun Doguwan rigar da aka Kamata da ita sanda abin ya faru har yanzu itace a jikinta idanunta duk sun zurma sunyi ciki tamkar bana Hajiya Aisha ba mata ƴar ƙwalisa da son kwalliya a haka aka sake jefata cikin magarƙama aka rufe.

Mom sun koma gida lfy kullum.ƙara tattalin ɗanta takeyi kasancewar Zaynab sun koma makaranta ne yasa komai yazo Musu da sauƘi, komai nasa mom ce keyi da kanta wasu lokutan abin har yana bawa Abie mamaki, Baba Hajarah ma ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba santa tayi arba da Muzaffar gabaɗaya ya rame yayi duhu kamar bashi ba, kuka ta dingayi itama daga bisani kuma ta haƙura tacigaba dayi masa addu'o'in Alkhairi da kuma na samun lfy.

Washe gari da safe mom ta kira Baba Hajara tazo ta sameta a falo tareda maryam me aikin Hajiya Aisha a zaune, da girmamawa Baba Hajara ta gaida Momy sannan ta sunkuyar da kanta

Mom ta kalleta tace "Hajara ga maryam nan zaku zauna tare kuci gaba da gudanar da hidimomin gidannan don Allah seku haÉ—e kanku kuma ku zauna da juna lfy.

Murmushi Baba Hajara tayi tace "to Hajiya insha Allahu. Mom ta kalli maryam tace "ki ɗauki kayanki ki bita zata nuna miki ma saukinki. Da to Maryma ta amsa sannan ta miƙe tabi bayan Baba Hajara suka nufi ɓangarensu.

Tunda Abie ya dawo daga india be samu ya zauna ba sabida ciku2 shariyarsu da Ummie, so yake ayi abin bisa sirri don bayaso kimarsa ta taɓu a idanun al'uma dakuma na ƴan jarida kasancewarsa babban mutum kuma wanda ƙasa kejidashi. Be wani sha wahala ba me shariya ya amince da batunsa na mayar da shari'ar tasu ta sirri because this is the only thing dayake ganin ze iyayiwa ummie a rayuwarta don bayaso ta wulaƙanta a idon duniya har yanzu yana ƙaunarta a cikin zuciyarsa ƙauna me tarin yawa bata wasa ba.

Washe gari Ya kama litinin ne kuma a ranar shariyar zata fara, Mom ce ta fito cikin shigarta na alfarmar a nitse ta gama sakkowa daga sters É—in sannan ta samu Fadilah a falo tana kallon news.

Da kulawa mom ta kalleta tace "dota idan kin tashi kije ki duba yayanki sannan kisa Hajara ta dafa masa abu meÉ—an ruwa2 wanda zeji daÉ—in ci seki kai masa kinji ko?

Fadilah tayi musmushi tace "ok mom sekin dawo Abie ya shigo tun É—azo da alama keyake jira. Shafa kanta mom tayi tareda sumbatarta sannan ta fice a hanya sukaci karo da Baba Hajara ta dawo daga rabawa masu gadi da masu yankan flowers abinci.

Cikeda girmamawa suka gaisa sannan tace "to semun dawo Hajara. Da murmushi a akan fuskar baba hajara tace "hajiya yau kece da fitar sassafe?

Tsayawa mom tayi cak sannan ta juyo da murmushi tace "wllh fitar ta dole ce kotu zamu kinsan mun shigar da ƙara akan Aisha.

Take gaban Baba Hajara ya buga da ƙarfi tanaji tana gani a haka mom tayi gaba ta barta zuciyarta na dukan tara2.

Thanks 4d love sisters naga addu'o'inku Allah yabar zumunci👏

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :27_*

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

BANYI EDITING BA🙅‍♀️

____✍️Wata irin zuface ta shiga yankowa Baba hajara tamkar an kunna fanfo da ƙyar ta iya ƙarasawa ɗakinsu tana ɗingisawa sabida ƙafar dake ɗan mata ciwo ta zauna daga gefan katifarta kasancewar ita nata katifan a ƙasa yake sabida yanayin jikinta, duk sanyin Ac n dake ɗakin nemassa tayi ta rasa sabida tsabar rashin kwanciyar hankali, maryam ce ta shigo hannunta ɗauke da faranti ta takeshi da soyayyoyar shinkafa wadda taji uban kayan lambu se baza ƙamshi takeyi, harta zauna tana kallon baba sabida yanda taganta duk ta fita haiyacinta.
Chapter 26 · 0% Book details