← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 57

Sashe 37

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaro manyan idanunsa yayi yace "kina nufin tun tea ɗin safe ne kawai a cikinta? "sure. Fadilah ta faɗi hakan. Miƙewa yayi da sauri ya isa daining Aria ya biɗe manyan womers ɗin dake jere ya fara ƙoƙarin zuba mata abincin, white rice ce da stew wadda taji uban naman kaji a nitse ya kammala zuba mata sannan ya dawo falon ya zauna daga gefanta ya ɗebo abincin ya fara bata tana karɓa, kallon Fadilah yayi wadda keta satar kallonsa yace " bring water for me. Juyawa tayi jiki a saluɓe taje ta ɗakki masa sassanyen bottle water da cup ta kawo masa.

Tsiyaya ruwan yayiɓa cup ɗin ya miƙa mata ta karɓa tasha a haka dai har mom ta cinye abincin tass sannan ya tattara kwanukan yakai kicin. Hira suka ɗan taɓa da mom ɗin dukda taƙi yarda ta saki jikinta dashi harya miƙe yabar falon zuwa part ɗinsa.

koda ya koma part ɗin nasa ma kasa zaune yayi balle tsaye sabida yanda maganar Ummie take masa yawo a tsakiyar zuciyarsa haka kuma wanu ɓangare na zuciyarsa yake aiyana masa wani abu a gameda Moddido, miƙewa yayi da sauri ya ɗauki ɗyaa daga cikin tarin mukullan motar dake zuɓe akan table ɗin glass ɗin dake tsakiyar falon ya fice da sauri...........

Thanks 4d love sisters 🥰

Shushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :37

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

*_I dedicate this special page for all the members of HOME OF QUALITY WRITERS ASSOCIATION Especially Aglan Nissa ina taya ku murna cika shekara É—aya tak da kafuwar qungiyarku, ubangiji ya qara É—aukaka tareda basirar faÉ—akar da al'uma tareda nishaÉ—antarwa._*

Banyi Editing ba 🙅‍♀️

____✍️Yana fita mota ya ɗauka tareda ɗanna mata key yabar harabar gidan zuciyarsa na wani irin beating a hankali, wani iri yakeji a jikinsa duk a sakamakon tunanin moddibo dake bin duk wata gabar jini da curin tsokar dake gudana a cikin jikinsa, bugu da ƙari kuma wani ɓangare na zuciyar tasa a kasu mafi yawa yafi ta'allaka ne ga Rabi'atoun sa wadda a yanzu ta gama mamaye duk wata kusurwa dake cikin zuciyarsa, tabbas kam a yanzu ya gama yarda da cewar ya faɗa a cikin zazzafar soyayya wadda abu ne mawuyaci ya iya jurar wani abu me girma ta sanadin hakan.

Driving ɗinsa kawai yake very gently but sedai duk wata nutsuwansa sam baya taredashi jifa-jifa yakan maida wani kaso daga cikin nutsuwarsa a kan titi don gudun afkuwar wani abu mara daɗi, ɗan sirin tsaki yaja tareda kai hannunsa jikin redion dake manne a jikin motar ya kunna waƙa mutuniyarsa Selindion cikin waƙarta me taken I'm yours only you.

Yanayin sanyin muryar mawaƙiyar ne tareda amon dake fita a muryarta ne ya haɗe da sanyin Ac ɗin dake busa ko ina na motar hakanne yay sanadiyae saukarwa da Muzaffar wata irin kasala me cikeda tsantsar kewa gamida begen abar Ƙaunarsa, lallai soyayyar dayake mata zazzafa ce wadda Bayajin ze iya jureta koda kaɗan ne, yanayin dayake ciki a yanzu baƙone a gareshi domin shiɗin baƙone kuma sabun shiga a lamarin irin wannan wanda ya dangaci gamaiyar zuciyoyi biyu.

A haka yayta saƙa da warwara harya kai babban filin jirgi na harkar abinda ya danganci sufuri dake cikin babban birnin taraiya Abuja, be wani ɓata lokaci ba yayi booking flight from Abuja to Taraba a cikin jerin wanda ze tashi gobe da misalin ƙarfe 5:am na Asubahi sannan ya kama hanyar komawa gida, koda ya dawo gida da wani irin ciwon kai ya shigo sabida yawan tunanin daya matsawa kansa dashi duk a dalilin rashin sabo a kan baƙon al'amarin daya samu kansa a ciki wanda Ummiensa ta bashi tabbacin cewar ya faɗa a soyayyar Fulani girl ɗinne wanda shi sam beyi noticing hakan ba ko kadan, Direct part ɗinsa ya nufa yanajin wani irin abu na nuƙurƙusarsa a cikin ko wace jijiyar jinin dake maƙale a tsokar jikinsa. Zubewa yayi akan ɗaya daga cikin hamshaƙan kujerun dake falon nasa tareda lumshe manyan idanunsa da suka fara canza launi sabida ciwon kan dake addabarsa, gyara kwanciyarsa yayi batareda ya damu da ya cire murɗaɗɗen takalmin fatar dake saƙale cikin kyakkyawar ƙafarsa ma'abociyar haske gamida limsassun gashi ba, ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske tareda laso Red lips ɗinsa da suka fara ɗan bushewa kaɗan.

Dukda irin ciwon da kan nasa keyi sam hakan be hanashi sakin wani ƙayataccen Murmshi ba wanda yake ɗauke da abubuwa da dama a cikinsa, a hankali ya buɗe bakinsa cikin Husky voice ɗinsa yace "Am comming for you babe. Ya faɗa tareda datse lips ɗinsa da fararen haƙoransa

Koda yaje yin diner a babban falon ya tararda gabaɗaya Ahalin gidan suna kallon ƙofa da alama shigowarsa kawai ake jira, ɗan turo cute red lips ɗinsa yayi gaba kaɗan batareda yace da kowa ƙalaba yaja kujerar daya saba zama wadda take dab data Abie ya wani haɗe rai duk dan kar wani ya samu zarafin tambayarsa Daga inda yake yabarsu suna aikin jiransa. Murmushi kawai Abie yayi tareda girgiza kai A ransa yace "ɗan Basaja. Sannan ya fara cin abincinsa.

Ummie kuwa kasa cin abincin tayi se faman juya cokalin dake hannunta takeyi, a zahiri so take ta tambayeshi damuwarsa amma kuma tanajin Nauyin yin hakan a gaban Saratu ko babu komai ai ta bata dama akan muzaffar É—in kodan darajar rainonsa datai mata, wadda ta kafeshi da idanun tun shigowarsa kmaar daga sama ummie ta tsinkayi muryar mom tana faÉ—in "son were are you coming from?

Kamar zeyi kuka yaɗan shafi kwantaccen sajen da yaywa fuskar ado baƙi wuluk dashi se faman shining yake yace "naje hira ne mom.

Zaro ido mom tayi tareda kafeshi da idanunta tace "Hira dai kace ?

Murmushi yayi mara sauti yace "Sure mom. Idan ban fara zuwa hira yanzuba se zuwa wani lokacin zan fara ? Daƙuwa mom tayi masa tace " lokacin da ka koyi kunya don gidanku.

Dariya gabaÉ—aya falon sukayi sannan zainab ta kalleshi tace "yaya Wace me sa'arce wannan har tasa ka fara sonta ba tareda kayi shawa dani ba?

Wani shegen kallo ya watsa mata batareda yace komai ba, kallonsa Fadilah tayi tana dariya tace "nasan duk inda wannan budurwan na yaya take kyakkyawa ce sosai harnaji inaso na ganta wllh. Ta faÉ—a tana binsa da kallon tsokana

Caraf zainab tayi tace "uhmm nasan dai duk kyanta bata kaini ba don haka dole ne ma naje musaba da juna kodan nayi mata screning Sosai.

Haɗe rai yayi shi'a dole da gaske yake yace "kedawa zakije har ku saba ɗin da ita? Ba tareda ta kalleshi ba kurɓi juce ɗin dake gabanta cikin cup ɗin glass tace dakai mana, nidai pls in zakaje next time zan bika don musan juna da ita Sosai kafin ta shigo Familyn mu.

Kallon gefan ido yayi mata yace "no base kinje ba batason hayaniya ki bari ba yanzu ba, nasan idan na kaiki takura mata zakiyi da shegen surutun ki. Ya faÉ—a yana wani yatsine fuska sabida ciwon kan dake damunsa

Jifa-jifa yakan juya ya kalli Ummie wadda tunda suka fara hirarsu sedai kawai tayi murmushi batareda tasa musu baki ba, miƙewa tayi tace "to nikam zan wuce part ɗina Asuba ta gari. Ummie ta faɗi hakan batareda ta kalli inda Abie ke zaune ba, harta fara tafiye ta tsinkayi muryar mom a tsakiyar kunnenta kamar haka "pls Aisha ki tsaya ki tafi da mijinki. Miƙewa Abie yayi yana murmushi cikeda dattako ya kalli mom yace " aiko baki faɗa ba Saratu nasan alkunya kawai Aisha takeyi miki don haka barina bi matana. Dariya mom tayi tace "Abie aina fika sanin Aisha macece me alkunya shiyasa takecin ribar zamada duk wanda Allah ya haɗata dashi.

Bece mata komaiba hakama Ummie data fara tafiya ba tareda ta waigo ba harta fice daga falon Abie na biyeda ita se faman rawar kai yake mata tamkar wani sabon Ango, jikinta ya janyota suna tafiyar tare har suka isa part ɗinta suna shiya wani janyota jikinsa tareda kafeta da lumsassun idanunsa masu matiƙar narka mata zuciya yace" Aishata ina matiƙar jin kunyarki tun daga lokacin dana ƙuntatawa zuciyarki ta hanyar miƙaki ga hannun hukuma ba tareda kin aikata laifin komai ba, hasalima duk abubuwan da kika aikata kinyisu ne domin farin cikina don Allah Aisha ki yafewa mijinki ko zan samu zuciyata da nutsu daga zargin rashin kyautawar danai miki pls Aish........." taya kake tsammanin cewa Aisha zata iya ƙullatarka don kawai kayi mata laifi Abdul?

Ummie ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar ƙwayar idanun Abie ɗin wanda shima ɗin ita yake kallo, murmushi ta sakin masa sannan tacigaba da cewa " Banida wani zaɓi wanda ya wuce inyi uziri a gareka bisa laifinka tareda kuma nuna maka cewar lallai ɗan Adam ajizi ne, haka kuma a muhalin da kake kai a matsayinka na Uba koma wanene abinda kai shizeyi Abdul don haka ka kwantar da Hankalinka daga rana irinta yau karka sake kallon kanka a matsayin mai lefi a idona Abie.

Shiru Abie yayi still idanunsa na kanta ji yake komai tayi ƙara burgeshi takeyi, tunda ya Aureta yau kimanin shekaru talatin bata taɓayin jayayya dashi ba komai ya ɗorata a kai shi takeyi ba tareda ta nuna masa rashin jin daɗinta a kai ba koda kuwa abin beyi mata daɗi a ranta ba, jikinsa a mace yace "Amma Aish...... Haɗe bakinta tayi da nasa guri ɗaya cikin wani irin yanayi dake baiyana tsantsar shauƙinta a gareshi, wata irin wutar ƙaunarsa ce ke ganiyar fizgart tamkar zata zautar da ita, daga kallon farko a wannan lokacin bazaka iya tantance ma'anar irin sumbatar da sukewa junansu ba, sabida hakan tamkar wani al'amari ne dayafi faruwa a tsakanin tsofaffin masoya waƴanda sukai nutsu a Cikin ƙoramar soyayyah Mara misaltuwa.

Tsaiwar ce ta fara ƙoƙarin gagararsu ba shiri suka zube A ƙasa bisa makeken kafet ɗin da yaywa falon ƙawanya suna maida numfashi, daga kan Abie har Ummie babu wanda baiyana alfarma da shauƙin da suke ciki a gameda junansu, kunsan idan gwani ya haɗu da gwana wajen ƙwarewa a soyayya tofa sedai kawai aja musu ƙofa a barsu su kaɗai😂
Chapter 37 · 0% Book details