← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 57

Sashe 40

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bubbuga bayanta ya dingayi a hankali ba tareda yayi ƙoƙarin hanata yin kukan ba, all he know is to let her cry and cry at least she will get some peace of mind akan abinda takeji dukda cewar be san meyeshi ba because har yanzu didn't tell him anything about her story shi kuma sam be tambayeta ba, abu ɗaya kawai ya sani shine a kwai ciwo a cikin Rayuwarta wanda take buƙatar koda so ɗaya ne abarta tai kuka koda kaɗan ne wata ƙila ciwon dake ranta ze rage raɗaɗi.

Seda tai me isarta sannan tayi shiru a hankali ta zare jikinta daga nasa ta kalleshi da idanunta da suka rine zuwa launin na wadda tayi kuka tace "bro Assigment pls.

Hannunta ya kama zuwa tdakiyar falon ya zaunar da ita akan lallausan kafet É—in yace "bring the book let me see. ÆŠan jim kaÉ—an tayi sabida yanda turancin nasa yaÉ—anyiwa fahimtarta nauri se kuma ta kalleshi tace "Noi?

Dariya ya sakin mata har seda kyawawan white teeth ɗinsa suka baiyana yace "nace muga littafin naki ?. Turo baki tayi a ranta tace "oh wai maganar ma baza'ayita yanda mutum ze gane cikin sauƙi ba. Hannunsa yasa yaja siririn dogon hancinta har seda ta ɗan saki ƙara sannan ya fara nuna mata yanda zatayi tayi ta fitar da answer ɗin, tunda suka fara taketa faman tura baki ita a dole wai ya takura mata. Bayan sun gama ne ta tattara book ɗin da biro ɗin ta fice daga falon babu ko thanks.

Dariya kawai yayi a ransa yana ƙarajin yarinyar a ransa sosai, haka kawai yakejin daɗin zama da ita sabida yanda wasu abubuwan nata ke yawan bashi dariya, duk daɗewarta a gidan besa ta manta wasu ɗabi'un nata dake nuna ainihin daga ina ta fito ba, a zahiri idan ka kalleta haka zakayi tsammanin itaɗin wayayyiyar mace ce Saɓanin idan tayi magana kokuma ta tafko maka wani shirmen nata me cike da zallar gidadanci, dariyace ta kufce masa daya tuna lokacin daya sameta a zaune dafi'an a saman daining tayi dare-ɗare tana shafa butter a jikinta. A hankali ya saki wani ƙaya taccen murmushi tareda Furta " Funny girl. A haka dai rayuwa ta dinga tafiya a tsakanin su cikeda zallar kulawa gamida nuna mata duk wata soyayya dazata sa ta manta abinda ke Ranta wanda kullum take aikin mafarkinsa.

Zeeyadah ce zaune a gefan gadonsu Rabe kuma tana kwance ta zubama saman ɗakin idanu tana aikin tunani, a hankali taji sallamar mom da hanzari ta miƙe tana mata murmushi alamar ta saba da ita sosai, cikin harshen fulatanci mom tace "dota bazakizo ki rungumeni ba kodai bakiyi kewata bane 2days? Tun kafin ta rufe bakinta ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana ɓoye fuskarta a jikin mom ɗin.

Edyan ne ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da wani kwali ya kalleta yace "Mulaikha come with me I want to show you something special that I Bay it for you I'm sure you will love it. Da hanzari ta saki mom tabi bayansa ba tareda ta lura da irin kallon dasu mom ɗin kebinta dashi ba, a falo sukaci karoda Hajar tana ƙoƙarin shigowa falon da sauri ta ɗaga fararen idanunta tareda washe mata baki tace "welcome beck sister. Hararanta tayi ba tareda ta kulata ba ta wuce tana jan tsaki

Shidai Edyan sam bebi takan wata Hajar ba ya buɗe kwalin ya fito da wani takalimi ƙirar toms me masifar kyau gamida tsada, ƙurawa takalmin idanu tayi kinta a buɗe tamkar taga ktafaren abin al'ajabi, ƙafarta ya jawo ya fara ƙoƙarin saka mata takalmin tayi saurin janyewa tareda fuzge takalmin daga hannusa tana dariya tace "wannan ai ba takalmi bane mudubi ne patner. Ta faɗa tana ƙalla idanunta ta cikin babban ston ɗin dake saman toms ɗin wanda keta baza uban kyalli tamkar ɗanyen daimond 💎

Baki ya saki yana kallonta kamar ya samu tv wani irin masifan burgeshi yaji tayi shiyasa ma ya shagala da kallonta, batareda ya shirya fuskanta abinda zeje yazo ba daga can ƙasan maƙoshinsa yace "I love you Mulaikha i really Love you with all my heart !!

Dakin baki tayi tareda maida kallonta gareshu ta wani irin kafeshi da wani irin mayan kallo wanda har seda yaji jikinsa yayi sanyi, ta ɓangarenta kuma haka kawai taji a ranta cewar kalmar daya faɗa ɗin tayi madifar jan hankalinta becouse ta taɓa jinta a kwanakin baya da daɗewa, seɗai dukda hakan sam bata san me kalmar take nufi ba.

Murmushi yayi tareda Sumbatar gefan kumatunta ya fice daga falon ba tareda ya waiwayo ba, yana dabda fita daga ƙofar falon ya tsinkayi muryarta tace "thank you partner. Be juyo ba ya fice gabaɗaya

Daki ta koma da kwalin takalmin a hannunta ta tarar da zeeyadah na zaine a bakin gado tana amsa waya, itadai bataji ƙarshen maganar da zeeyadah keyi ba taji tace "I love you too dear.

Kafeta tayi da idaninta sannan ta ajiye takalmin a tsakiyar É—akin ta nufi zeeyadah tareda É—ora hannunta a daman kafaÉ—unta tace "pls me wannan kalmar take nufi? Cikeda rashin fahimta tace "wani kalma kuma Mulaikha?

"i love you ? Ta faɗa with so much courage. Kallonta kawai Zeeyadah tayi da mamaki kwance a saman fuskarta tace "who told you so mulaikha? Ba tareda ta kalleta ba tace "pa....... Momce ta shigo ɗakin hakanne yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufi mom da sauri tareda ɗaukan takalmin tana dariya ta nufi mom ɗin dashi tana nuna mata.......

comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad

Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page : 40-41

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

*Duk wata Qaddarar dake ɗauke da zallar soyayya gamida muradi me ƙarfin gaske Kan zamewa zuciya Kamar gyambo me matiƙar zafi gamida Ciwo musamman Idan Zanan ƙaddarar rabuwa ya gifta atsakanin masoyan😢.*

*Banyi Editing ba kuyi haquri da typing error*

____✍️Sosai mom ta nuna mata jin daɗinta akan takalmin da Edyan ɗin ya siya mata musamman dataga yanada Mulaikhan ta nuna jin daɗinta sosai akai, kallonta mom tayi cikin ido tace " kince mishi kin gode ko Mulaikha?

Murmushi ta sakin ma mom É—in har seda beauty point É—inta both side suka lotsa at the same time, juyawa mom tayi ta kalli zeeyadah tace ki ajiye wayar nan malam kuzo khitchine zamu shirya abinci na musamman Sabida yau Dadynku xe dawo. Wani uban tsalle zeeyadah ta buga tareda wirga wayar kan gado tazo ta rungume mom tana murnar tace "are you serious mom?

ÆŠaga mata kai mom tayi tareda faÉ—in "sure darling. Sannan ta Shafi gefan fuskokinsu tace "muje ko. Tare suka fita zuwa kicin suka fara gabatar da komai cikin tsari tareda zumuÉ—in dawowar mijin nata ita kuma zeeyadah na farin cikin ganin Dawowar Daddyn nasu, a haka har suka gama girkin cikin nutsuwa da aminci bayan sun gama girkin a manyan kuloli na gani na faÉ—a mom ta kwashe abincin sannan ta kalli Rabe tace "dota kuzo kuje keda Zeeyadah part É—in Daddy ku gyara sannan ku kwashe womers É—in nan ku kai kan daining É—insa. Da to suka amsa sannan suka tafi cika umarnin mom É—in.

Kamar yanda mom ɗin ta faɗa hakan ne kuwa ya kasance, sosai suka shiga gyaran part ɗin da dukkan ƙarfinsu tun kafin aci litinin da talata a aikin zeeyadah ta xube akan kujera tace ta gaji, murmushi Rabe tayi sannan ta ci gaba da aikin ba tareda ta huta ba seda ta gama tsaf sannan suka fito zeeyada na kuranta ta da irin zafin naman da mulaikan kedashi, itadai mulaikha murmushi kawai take har suka fice daga falon sannan suka fita

Se wajen yamma sannan jirginsu Dad ya sauka a babban birnin taraiya Abuja, gabaÉ—aya Ahalin na gidan Edyan ya kwasa a mota da kansa ba tareda guards ba suka tafi except Mulaikha da aka bari a gida don gudun kar dad ya ganta.

Lokacin da sukaje ba ƙaramin farin ciki dad yayi da ganinsu ba sabida yanda yay masifar kewarsu, shigewa jikinsa Zeeyadah tayi tana dariya tace "dad i miss you wllh. Murmushinsa ya faɗaɗa sannan ya kalli mom yace "murja banga mamana ba were is she?

Ɗan jim kaɗan mom tayi don wllh koze kasheta bata san inda Hajar take ba, rabonta da ita tun safe kafin ta tafi office. Murmushi ta ƙaƙalo masa tace " she's in the office...

Taɓe baki Edyan yayi a haka har motocin jami'an tsaron suka iso sannan suka ɗaukeshi tareda yi masa rakiya zuwa gida tareda iyalansa, suna isowa gida aka wangale musu Get motocin suka dinga danno kai kamar bazasi ƙare ba, dad na fitowa daga motar idanunsa suka sauka akan Rabe data leƙo ta windon falon sama. Da sauri ta saki labulan gabanta na faɗuwa.

*NEW DELHI*

Mohad moghandi special Hospital, muzaffar ne zaune bisa wani ƙayataccen ɗaki wanda aka ƙawata da kayayyakin kula da lfy iri-iri, wani ƙasaitaccen gado na hanga daga can gefe wanda moddibo ke kai idanunsa a rufe ruf, a tsakanin bakinsa kuma masuburbuɗar oxygen ce maƙale a fusƙarsa wadda take sauwaqe masa hanyar shaƙar numfashi cikin sauƙi. Ƙura masa idanu muzaffar yayi yana kallonsa cikeda zallar tausayinsa yasa hannunsa ya shafi gefan fuskarsa sannan ya fice daga ɗakin da sauri.

Direct inda aka tanada don biyan kuɗin tiyatar ya nufa batareda ɓata lokaci ba yayi musu transfer Ɗin naira million 5 ɗin da suka buƙata sannan suka bashi racit shedar ya biya yabar gurin zuwa ɗakin da yabar modɗibon, cikin mintunan da bazasu gaza goma ba aka shiga dashi tiyata room ɗin a ƙarƙashin jagrancin Dr. Rahul Gufta da teams ɗinsa.

Semuce Allah yasa ayi a sa'a Dr. Rahul Gufta.

Ako wani lokaci abubuwa da dama kan sauya manufarsu musamman ga zuciyar dake cike da zallar muradi gamida begen akan dukkan abunda take mafarkin samu tareda mallakarsa na har abada, zuwa yanzu baze iya tabbatarwa da kansa irin halin dayake ciki ba hatta jinin dake gudana a jikin kowace gaba ta jikinsa a gauraye yake da wani nau'i na musamman tareda sirki irin na zazzafar soyayya mara misaltuwa.
Chapter 40 · 0% Book details