← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 57

Sashe 32

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jima tana wankan sannan ta ɗauro Alwala ta fito ɗaure da wani ƙaton towel wanda ya saukar mata har idon sawun ƙafarta, gaban mudubi ta zauna tareda zubawa kanta idanu lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka har lips ɗinta na rawa sabida yanda take kukan.

Mom kuwa tunda ta shiga falon bata dire ko inada Muzaffar ba se bedroom ɗinta zaunar dshi tayi a babban dogon soofer ɗin dake ɗakin tareda zama a ƙasa tana facing ɗinsa tareda damƙe hannayensa ta fashe da wani irin kuka tace "Na shiga uku yarona wllh so suke kawai su rabani dakai don sunga banida abinda na mallaka sekai a duniya tareda sauran ƙannenka, wllh nasan ƙarya Aisha takeyi mana kawai tanaso ta ɓullo da wani abu ne wanda zesa ta ɓoye laifinta na yunƙurin kashe ka i know that tun ba yauba cewar Hajara Munafukar tsohuwace so take kawai ta kawo mana ruɗani, pls boy karka bari maganarsu ta shiga cikin kanka wllh I'm your biological mother!!!!!. Ta faɗa tana ƙara rushe masa da kuka

GabaÉ—aya jinya kawai yake inda gefe guda na zuciyarsa ke cike taf da wani irin tausayin mom É—in, jnayota yayi jikinsa ya rungumeta yanaji saukar hawayenta a gadon bayansa.

*******

Rabe ce zaune a tsakiyar makeken gadon Zeeyadah tana kuka tashi zeeyadah tayi idanunta fal da bacci tana kallonta kamar zatayi kuka don takaici tace "meye kuma? HaÉ—iye kukan Rabe tayi cikin sanyinta tace "Babana!. Daga haka bata sake cewa komai ba donharga Allah bata da isashshen hausar dazatayi mata bayanin abinda ke damun nata na mafarkin Mahaifinta datayi harya sata kuka.

dafa kafaɗunta Zeeyadah tayi tace "kiyi haƙuri kinji insha Allah komai zeyi daidai.

Kwanciya sukai har bacci ya sake ɗaukar zeeyadah still Rabe idonta biyu, jikinta a mace ta miƙe tanabin ko inada kalli musamman ma ƙwan fitilar dake ɗakin wanda kalar hasken dake jikinsa ya rikiɗe zuwa blue colour daidai na bacci, ta jima tana kallon ƙwan fitilar sannan ta buɗe ƙofar ɗakin daƙyar ta fito sabida wani irin masifan ƙishirwa datake ji, a gaban dispenser ɗin dake falon ta tsaya tareda tsugunawa ta zuba mata idanu tana kallon ruwan dake cikin dogon roban jikin dispenser ɗin, kama robar tayi da ƙarfin tsiya zata cire tasha ruwan se uban haki take amma ko gezau roban ruwan beyi ba, fashewa tayi da kuka tana dukan dispenser ɗun da hannayenta a nitse taji an buɗe ƙofar ɗakin dake bayanta

Da sauri ta juya tana kallon ƙofar da ake ƙoƙarin buɗewar, Hajar ce ta fito tana zuba uwar hamma da alama itama Ruwan ta fito sha tsayawa tayi cak yayinda idanunta suka sarƙe cikin na Rabe nan take ta ƙwalla ƙara me matiƙar firgitarwa

Rabe dake tsaye gashin kanta dukya baje a gadon batanta itama ihun ta saki kankace me tuni mutanan gidan kowa ya fito falon a tsorace jiki na Rawa.

Edyan na ƙarasowa gurin Rabe ta ɓoye a bayansa tana rarraba idanu tana kallon Hajar wadda ta ƙanƙame mom tana faɗin "waiyyo mom Aljana na gani wllh mom Aljanace. Tsaki mom ta saki tace "dilla malama ki nutsu ba wata aljana wannan ce fa uhmm. Se kuma mom tayi shiru sabida sam batasan Sunan dazata kira Raben dashi ba becouse batasan sunan ta ba har yanzu bata gaya musu ba.

zarota yay daga bayansa yace "look ba abinda zata miki kinji just feel free with her ok? Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa babu ko ƙiftawa hure mata idon yayi da iskan bakinsa dole yasa ta sunkuyar da kanta bajajjen gashinta ya rufe mata fuska kamar zatai kuka ta turo baki tace "miyara diyam.

Kafeta sukai gabaki É—ayansu da idanu suna mamakin yanda tayi magana a karon farko tun zuwanta gidan, wani irin murmushi Edyan ya saki ya kalli mom yace "what did she say ?

Ajiyar zujiya mom tayi lokaci guda kuma yanayinta ya sauya tace "she said that she want to drink water. Edyan yace "wow i like Fulani language wllh mom and then what should we call her as her name mom?

Ɗan jim kaɗan mom tayi tareda faɗin ban saniba Edyan, caraf zeeyada tace "mu dinga kiranta ihsan yaya. Taɓe baki yayi yace "no let us call her Mulaikha. Ya faɗa yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta ta cikin dogon gashinta dayayi mata rumfa yace "as from today your name is Mulaikha kinji?

turo baki tayi alamar bata ma san meyake faɗa ba dariya yayi me sauti tareda janye gashin dake saman fuskarta baƙi wuluk dashi yace "daga yau sunan ki mulaikha ne har zuwa ranar dazaki faɗa mana sunan ki na gaskiya kinji? ..... Kamar daga sama yaji tace "miyara diyam.

cup ya ɗauka ya murɗo mata ruwan a dispenser ɗin sannan ya miƙa mata ta kafa kai ta fara sha batareda ta sauke ba........

comment
Nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :32

NOT EDITED🙅‍♀️

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

___✍️ Zeeyadah ya kalla yace "go and bring Ribom for me pls wannan gashin nata yayi yawa ai duk yabi ya takurata. da sauri zeeyadah ta juya zuwa ɗakinta ta ɗakko ribom ɗin a cikin nata ta kawo masa

Dogayen hannayensa ya miƙa ya haɗe mata gashin gabaɗaya guri guda ya ɗaure mata se faman yamutsa fuska take alamar tanajin zafi, tsaki Hajar ta saki ta kalli mom tace "who is this girl please mom? Dubi fa yanda ta wani zo ta bawa mutane tsoro da wannan shegen farin fuskan nata kamar aljanah, wllh mom taci sa'a darene yanzun dasena falla mata mari. Ta faɗa tana shigewa ɗakinta tareda bunko ƙofar da wani irin ƙarfi sabida haushi

Shiru Edyan yayi yana bin ƙofar ɗakin Hajar ɗin da kallo sannan yay murmushi bece komai ba ya miƙe yabar falon kama hannunta zeeyada tayi tana kallon fuskarta wadda wani lumsashshen baƙin gashi yayiwa ado bisa goshinta tace "muje ba musu tabi bayanta tana murza idanunta da ɗaya hannunta.

Da ido mom tabisu a ranta tanajin wata irin ƙaunar yarinyar gamida tausayinta suna ratsa duk wata gaba ta jikinta, sosai takejin yarinyar a kusa da zuciyarta wata ita kanta batasan dalilin hakan ba.

Washe gari da safe Zeeyadah ta shirya cikin Uniform ɗinta milk and cofee colour ƙafarta sanye cikin wata farar socks da bakin takalmi, ƙura mata idanu Rabe tayi a ranta tana girmama irin shigar dataga Zeeyadahn tayi turo baki tayi a ranta tace "kai amma wanna bata da kunya dubeta duk jikinta a waje.

Juyowa zeeyadah tayi suka haɗa ido da sauri Rabe ta sauke kanta ƙasa tana wasa da dogayen yatsun hannunta, murmushi ta saki sannan ta tako zuwa kusa da ita tace "Mulaikha why are you looking at me like that uhm? Kina son wani abu ne? . Zeeyadah ta jera mata tambayoyin a lokaci guda

Ƙara turo mata ɗan ƙaramin bakinta tayi still her eyes on her face batareda tace komai ba, ajiyar zuciya Zeeyadah ta saki tace "ok barina tafi school sena dawo ta faɗi hakan tana hugging nata with so much love irin na fisabilillah ɗinnan.

Dagalo tayi tana kallonta harta fice daga ɗakin bata jina da fita ba mom ta shigo ɗakin da sauri ta ɗago fararen idanunta tana kallon Mom ɗin wadda itama ɗin take kallonta, sauke idanunta mom tayi da sauri a ranta tanajin cewar tabbas tasan wani me irin idanun yarinyar but she can't remember, murmushi ta ƙaƙalo ta kalleta cikin harshen Fulatanci tace mata " taso muje kici abinci ki shiya Edyan idan ya fito ze kaiki makaranta kema. Ƙurawa mon idanu tayi mamaki kwance akan fuskarta ta buɗe baki itama cikin Harshen Fulatanci tace "dama kinajin Fulatanci?

Murmushi mom kawai tayi tareda kama hannunta suka fita zuwa falo, Tea me bala'in kauri mom ta haɗa mata tareda zuba mata soyayyen dankali a gefan flet kaɗan se kuma pride egg shima a gefe. Wani flet ɗin mom ta jawo ta zuba mata pepe soup ɗin kaza a ciki wanda yaji uban kayan ƙamshi se baza ƙamshi yakeyi ta tura mata shi gabanta tace " maza ki cinye ki bani flet ɗin.

Shiru tayi tana bin abincin da kallo wanda a iya Rayuwarta sam bata taɓa cin karoda irinsa ba se a wannan rana, babban Abinda ya bata mamaki gamida ɗaure mata kai shine yanda taga kwanon abincin fari tas dashi kamar madubi"kamar zatayi kuka ta kalli mom cikin harsheta na fulatanci tace "taya mutum zeci abinci a cikin mudubi irin wannan ? Nikam gaskiya inajin tsoro kar wani abu ya faru dani yayinda nakecin abincin a cikin kwanon.

Dariya mon tayi tareda shafa tumulin gashin dake kanta tace "karki damu babu abinda zai faruda ke kedai kawai kici abincin ki. Kwanon ta ɗaga sama tana wani leƙa ƙasansa se kuma tasa ɗayan hannunta ta shafo ƙasan flet ɗin da pepe soup ɗin ke ciki ta kai bakinta a tunaninta romon ze fito ta bayan kwanon. A haka Hajar ta fito daga ɗakinta cikin wata doguwar rigar material me azabar kyau gamida bin jiki, sosai kayan suka karɓi jikinta abinka da ƴar ƙwalisa. Lol a yangance take takunta irin na mata masu jida kansu hannunta ɗaukeda wayarta ƙirar Iphone, tun daga nesa take kallon Rabe tana wani yamutsa fuska harta zo ta bayanta zata Raɓa ta wuce zuwa inda mom take, wayar hannunta ce ta fara Ringing wanda hakan yazama tamkar wani abu na daban a kunnuwan Rabe, sosai ta gigice dajin ƙarar wayar take hannunta ya fara rawa lokaci guda kuma juya bayanta tareda saki flet ɗin dake hannunta sabida yanda ta tsure take romon naman ya sheƙewa hajar a jikinta.........

Wata uwar tsawa Hajar ta daka mata wadda tasa gaba daya ta fice daga sauran nutsuwar data rage mata se kawai ta fashe da kuka, gadan-gadan Hajar ta nufeta da nufin ta watsa mata wani lafiyayyen mari Mom ta riƙeta gam lokaci guda kuma ta watsa mata wani lafiyayyen mari wanda seda taga wasu kyawawan taurari nayi mata yawo a tsakiyar kanta, cikeda ɓacin rai mom tace " Hajar meyake damunki ne ? Anya kuwa kina cikin haiyacin ki? To don uwarki da kika nufeta me kike shirin yi mata da kika nufeta gadan-gadan bayan tsorata tan da kikayi?
Chapter 32 · 0% Book details