← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 57

Sashe 38

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiyasa nima nai waje naja musu ƙofar falon don al'amarin dattijawan ya zarce tunanin chubaɗo balle harta iya samun zarafin rubuta muku shi🤧

*_(Jan hankali a gareku matan Aure, wllh soyayya bata taɓa tsufa so karki bari wai dan kinga kin haifi yara masu yawa kuma sun kawo ƙarfi kice bazaki nunawa mijinki tattali da ƙauna ba yayinda kuke gudanar da al'amarin sirrin kwanciyar Aure ba, my dearest sisters wllh namiji komai tsufansa yana masifarson tattali da kuma zazzafar soyayya musamman yayinda kuka keɓance dagake seshi, kada ki taɓa bari mijinki yaga gazawarki akan komai ma na zamanta kewa base lallai ta hanyar kwanciya ba, a kwai hanyoyi dadama wanda zakiyi amfani dasu ki dasawa mijinki tsantsar qaunarki ba tareda da boka ko malam ba, kunga ɗan kissing ɗinnan da kuke rainawa wllh karkiyi wasa dashi wajen yi masa su kala-kala, idan ma baki iyaba to ki koya domin wllh a kwai wani irin ni'imtaccen sirri a cikin sumbatar juna wanda Allah ne da kansa ya sanya hakan ba tareda mun sani ba ta hanyar ƙawazucin mu, yayida ma'aurata suke gudanar da kissing a tsakaninsu numfashinsu kan sarƙe dana juna tareda fitar da wani irin maganaɗisu me haifar da zazzafar soyayya gamida ƙauna me ƙarfin gaske a tsakaninsu. So pls sisters we have to be very careful akan wannan sirrin karkuyi sake akai don Allah.)_* kuma bance wata marakunyar budurwar ta gwada ba sabida sam ba ɗabi'ar arziƙi bace a gareki ki bari wani ƙato yay kissing ɗinki babu aure ba 🙅‍♀️, a kwai tarin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar kissing ɗin wani ƙaton don haka wllh ku kiyye.

Washe gari da duku-duku Muzaffar ya fito cikin shirinsa na wata shaiɗaniyar shadda gizna brown colour se faman baza yararin tsada takeyi gamida kyau anyi masa ɗinkin Muhammed, hannunsa ɗaure yake cikin rantsatsen agogonsa na rolex me launin kalar golden wanda ya ƙara haska tsintsiyar hannunsa, dukda cewar kansa a kwai hula sam be hana fitowar kwantaccen baƙin gashinsa wanda yabi harta tsintsiyar donkin wuyansa ba, ƙafarsa sanye take cikin wani haɗaɗɗen takalmi meɗan yatsa wanda aka ƙerashi daga fatar damusa me launin kalar brown da yarfen milk kaɗan a jiki, wayoyinsa ya ɗauka ya zuba a aljihunsa sannan ya ɗauki Atm card ɗinshi yasa a cikin wata cute ƙaramar wallet sannan ya fito se baza uban ƙashi yake tamkar wanda aka tsamo daga ƙoramar ruwan turare gabaɗaya.

Duk wanda ya ganshi a wannan lokacin zeyi zaton sam ba mutumin ƙasar nigeria bane sabida yafi kamada larabawan yakin ƙasar Misrah (Egypt) shugar dake jikinsa ce kawai zatasa ka fahimci shiɗin cikakken ɗan Nigeria ne.

Yana fitowa parking lot ya nufa ya faɗa cikin wata hamshaƙiyar Bugati baƙa wuluk wadda taji uban tinted kamar bala'i ya figeta @360 se babban filin jirgin dake cikin babban birnin taraiya, yana zuwa befi saura minti biyar jirgin ya tashi ba don haka a gaggauce ya perkar motar sannan ya fito ƙarfe biyar ɗin Asuba na bugawa jirginsu ya ɗaga zuba Tarabah State.

Se muce a sauka lfy Muzaffar ✊

Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :38

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba 🙅‍♀️

____✍️Cikin ikon Allah da himarsa suka iso garin Taraba lfy, sedai tunda ya shigo cikin garin taraba ƙirjinsa ke wani irin bugawa wanda shi kansa besan dalilin hakan ba, sedai yafi ta'allaƙa hakan da baƙon yanayin dayake ciki wanda Ummien sa ta fassara masa shi da suna Soyayya, ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa kwantaccen lallausan baƙin gashin dake zagaye da kyakkyawar Fuskarsa ma'abociyar haiba da kuma kwarjini

cikin gari ya shiga zuciyarsa a cike fal da tarun abubuwa wanda yasa hakan ya haifar masa da faɗuwar gaba me tsananin gaske, guri ya nema daga geban wani babban titi ya zauna tareda dafe saitin zuciyarsa idanunsa a lumshe, ya jima a hakan sannan ya miƙe ya fara tafiya cikin takunsa na isa da ƙasaita harya isa bakin wani Babban bakin wanda akayi rubutu kamar haka ZENITH BANK.

kuɗaɗemasu yawan gaske ya cira sannan ya fito ya samu shatar wata ƙaramar motar dazata kaishi Gyambu ya shiga ciki ya zauna tareda biyan Driver kuɗinsa ya kuma buƙaci da ya kaishi wani babban super makert ɗin dazeyi siyayyar kayan Abincin, ɗaga masa kai Driver ɗin yayi cikeda girmamawa sannan yaja motar don cika umarni.

A gaban wani katafaren Super maket suka tsaya ya cikin nutsuwa ya fito jikinsa duk babu wani guzari ya shiga ciki ya fara labtar kayan abinci tun daga kan buhuhuwan shinkafa har zuwa kan catons na taliya, seda ya kashe kuɗi sosai ba ɗan kaɗan ba sannan yaje ya biya kayan aka fito masa dasu zuwa mota, taf aka cika booth na motar babu masaka tsinke har seda aka zuba wasu kayan a sit ɗin bayan motar sannan suka kama hanya don gudin karsu ɓata lokaci.

Sunyi tafiya me nisa gaske damkar zasu bar gari sannan suka iso bakin hanyar dazata kaisu cikin Rugar tasu Moddibo, tsayawa da motar Driver yayi sannan ya dubi muzaffar yace "Ranka ya daÉ—e ta ina kake tsammanin zamu iya ratsawa ta cikin wannan dajin ?

"sannan kuma gurin wa zakace a cikin wannan sunkurun dajin da babu wani bil'adama dake Rayuwa a cikinsa? A haka dai kayi kamada mutum me kamala kuna wanda hankalinsa yake taredashi balle ince ko matsalar ƙwaƙwalwa gareka.

Ɗan jim muzaffar yayi kamar bazece komaiba yace "kaga malam ji nake biyanka nayi? Indai har ba kyauta ka ɗakko ni ba to kayi yadda nace ɗin idan kuma kuɗinne yayi maka kaɗan seka gayamin na ƙara maka.

Washe baki mutumin yayi sannan ga taka motar suka kutsa cikin dajin, ta tsakiyar labin fulani suka dinga raɓawa suna samawa kansu hanya har suka iso cikin tsakiyar rugar, suna faka motar Befi da mintuna kaɗan ba Mazan Garin suka zagaye motar hannunsu ɗauke da manyan makamai.

Sosai Drivern ya tsorata hakama muzaffar amma kumashi seya dake batareda ya nuna tsoron dake taredashi ba ya fito yana kallon screen ɗin wayarsa , cikin harshen fulatanci wanda yafi kamada na zallar ɗan koyo yace "ni baƙon Alkhairi ne a gareku bana sharri ba, hkaa kuma nazo ne don na gana da Malam moddibo.

Take yanayin fuskarsu ya sauya daga yanayin da suke ciki zuwa na tausayi suka dubeshi ba tareda sunce dashi ƙala ba suka buɗa masa hanya ya nufi ƙofar karan dake kewaye da gidan nasu Rabe ya kunna kai ciki, mata ya gani a zazzaune inda su kuma su malam iro suke ƙoƙarin fitowa da gawar moddibbo dake kwance samɓal cikin makara an lulluɓeshi da zani, har suka gama fito dashi daga cikin bukkarsa da aka shiryashi a ciki idanunsa na kansu ba tareda ya motsa ba sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki. Bayan sun fito dashi ne muzaffar ya samu zarafin zubewa akan ƙafafunsa dirshen a ƙasa ƙirjinsa na wani irin bugawa.

Banda rawa babu abinda bakinsa keyi so yake yayi magana amma kuma ya kasa daƙyar ya iya ɗaga hannunsa yay nuni da makarar daga inda yake zaune ya buɗe bakinsa dakyar ya haɗo kalmomin dake maƙale a ƙasan maƙoshinsa yace "why Baffah ? "why are you doing this to me? "I said why!!!? Muzaffar ya faɗa da wani irin ƙarfi lokaci guda kuma ya fashe da wani irin kuka kamar mace.

Hakanne ya janyo hankalin jama'ar dake gidan zuwa gareshi gaɓaɗayansu suka kafeshi da ido suna kallonsa.

Babu wanda yace dashi ƙala sabida sam basu shaidashi ba ciki kuwa harda Inna Laure, kallonsa kawai takeyi Idanunta na zubar da Hawaye me matiƙar zafi da ciwo tambaya ɗayace take mata yawo a rai wadda ta rasa amsarta itace shin wanene wannan Matashin ?

Yanaji yana gani su Malam iro suka Raɓa ta gefansa suka fita da gawar zuwa Waje donsuyi masa sallah, ya jima a gurin zaune yana kuka har suka kabbar Sallah still yana zaune ya kasa koda motsin kirki

Shiru yayi ya zubawa ƙofar ɗakinsa idanu nan da nan ya faɗa cikin ƙoramar tunani, da wani irin mugun sauri ya tashi ya fita da gudu zuwa inda Malam iro ke gabatar da Sallar gawar yasa hannu ya fin cike zanin da aka rufeshi dasi, cikin ƙanƙanin lokaci ya saita hannunsa a daidai saitin zuciyarsa yasa hannunsa duka biyun ya fara dannawa da ƙarfi still idanunsa na zubar da hawaye.

Sallame sallar sukayi da hanzari sukayo kansa suka janyeshi daga jikin gazawa kowa na tofa albarkacin bakinsa, masuyi masa kallon mahaukaci nayi haka kuma masu magana ma nayi.

Shidai Drivern da sukazo tare kallonsa kawai yakeyi a ransa yana me tausaya masa, igiya suka samu me kaurin gaske suka É—aure muzaffar da ita sannan aka samu akayiwa moddibo sallar

Bayan sun idar ne suka fara giji-gijin ɗaukar makarar take sukaga jikin moddibon na wani irin karkarwa, gab aɗayansu jama'ar dake gurin tserewa sukai kowannensu ya cika wandonsa da iska sabida faruwar wannan abin al'ajabi idan kuka cire Malam iro, shine kaɗai be iya barin gurin ba ya tsaya cak yanai masa addu'o'i. Shima alfarmar ilimin Addinin dayake dashi wadatacce ne ya sanyashi tsayawar batareda ya gudu ba, fuzge jikinsa muzaffar yayi da ƙarfin tsiya tareda nufo gurin da wani mugun gudu, kallon Driver ɗin da sukazo tare yayi cikin ɗaga murya yace "matso da motar mukaishi Asbiti.

Dama can drivern ya gama sauke kayan da suka lodo na abinci hakanne ya basu damar saka moddibon a ciki sannan muzaffar ya shiga baya tareda moddibo shikuma malam Iro ya zauna a mazaunin gaba shi kuma Drivern yaja motar da gudun gaske suka nufi cikin garin Gyambu don nema masa taimakon gaggawa daga likitoci.

Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad.

Sushmah 💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page : 39

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️
Chapter 38 · 0% Book details