← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 57

Sashe 18

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___✍️murmushi yayi sannan yace "ngde Ummie kusan a tare suka shiga cikin gidan wanda aka ƙawata da kayan ƙwa na zamani kuma masu matiƙar tsada, miƙewa yayi Direct zuwa inda ya saba sauka idan yazo ƙasar harya kai bakin ƙofar part ɗin Ze murɗa handile ɗin ƙofar Ummie tace " idan kayi wanka ka huta sekazo daining kaci Abinci.

Da to ya Amsa mata yana me ƙara faɗaɗa murmushin dake kan Fuskarsa sannan ya kunna kai zuwa cikin haɗaɗɗen falon, bedroom ya shige tareda rage kayan dake jikinsa zuwa singlet with boxer wanda hakan ya baiyana santala-santalan legs ɗinsa, a hankali yake takawa harya isa cikin ƙayataccen toilet ɗin wanda aka wadashi abubuwan ƙyale-ƙyale iri-iri, tsayawa yayi cak yana kallon kowace kusurwa dake toilet ɗin bisa ga mamakinsa komai an sauya masashi daga waƴanda ya sani a baya zusa Sababbi, a nitse yake takawa cikin takunsa harya isa gaban wani baban Abu wanda yafi kamada bahon wanka na zamani, ruwa ya tara a cikin ƙaton bahon me ɗan zafi tareda zuba shower gel ɗin daya saba amfani dashi mallakin Companyn Olay me bala'in ƙamshi take kumfa ta cika bahon ,

Murmushi yayi me kyau tareda shiga cikin Ruwan ya zauna tareda lumshe manyan idanunsa zafin ruwan na ratsa duk wata gaba ta jikinsa, sosai yakejin daÉ—in yanda zafin ruwan ke Ratsashi ya jima a ciki daga baya ya buÉ—e ruwan ya wuce sannan ya tare wani yayi wankan ya fito. Bayan ya fito daga wankan be wani tsaya shafe-shafe kamar yanda ya sababa ya shirya cikin kayan sport marasa nauyi tareda kabbara sallar dake kansa, ya jima yana sallar sannan ya idar taredayin Azkar É—insa kamar yanda ya saba a kowace Rana.

Yana miƙewa kiran Abie ya shigo wayanshi daga yanayin ringing ɗin ya Fahimci cewar Abie ne, zama yayi daga bakin gadon dake ɗakin tareda kara wayar a kunnensa da sallama yace "Abie ya gida? Ɓangaren Abie yayi murmushi yace "lfy lau Son ya gajiyan Hanya? Ɗan shagwaɓe fuska yayi sannan yace "uhm wllh Abie a kwaita kagafa se yanzu na yi wanka tun shigowana ƙasar. Dariya Abie yayi me Sauti sannan yace "ka kula da kanka sosai I'm sure of you will do your job with full success. Muzaffar yayi murmushi yace " sure Abie insha Allah.

Mom dake zaune gefan Abie haka kawai seta samu kanta da rashin samun kwanciyar Hankali tunda muzaffar yayi tafiya, haka nan seta samu kanta da rashin Amintuwa da tafiya jiki babu ƙwari ta karɓi wayar daga hannun Abie cikin tattausan lafazi tace "Boy ya dai ina fatan kana lfy? Ɗan shafa gefan fuskarsa yayi kana yace "I'm fine mom and why your voice was so cool? "I don't know why darling I'm just feel like something is definitely going to happen to me. Pls take good care of yourself kaji yaron kirki? Sannan ka kula da makircin Hajiya Aisha ok.

Shiru yayi bece komai ba a haka suka katse wayar Abie na binta da kallon mamaki yace "why are you behave like that Hajiya Saratu? Meyasa ke bakya ƙaunar kiga an zauna lfy ne?

Yau kimanin shekaru nawa ana wannan abin ai yaci ace yanzu kun haƙura kuma kun zubar da komai kodan kwanciyar Hankalina. Cikeda karyewar zuciya mom tace "Abie bazaka gane komai ba shiyasa kake faɗar hakan, taya matar dta nunawa ɗana tsana tun yama ɗan ƙarami kayi tsammanin cewar yanzu bazata iya cutarmin dashi ba?

Nifa uwa ce Abie taya bazanyi yaƙi da duk wani me neman cutar min da rayuwar ƴaƴana ba? Kada ka manta da wacece matarka Aisha kasancewar bata taɓa haihuwaba tunda ta hafi ɗanta bezo da raiba take ƙoƙarin ganin bayan nawa ɗan har zuwa lokacin daka ɗauketa tabar ƙasar nan. Wllh nasan she can do anything don ganin ta lalata min rayuwar Ahalina amma nasan onday one time you will understand what I mean insha Allah.

Shidai Abie girgiza kai kawai yayi tareda miƙewa ya faɗa toilet tana binsa da kallo,

*******
Ɓangaren Muzaffar kuwa Ajiye wayar yayi ya fita sabida wani irin juyawa da cikinsa keyi sabida yunwa yana fita a falo ya samu Ummie tareda wata ƴar aikinta Maryam kallo ɗaya zakayi mata kasan ƴar Nigeria ce, a ƙalla shekarun Maryam zasu kai 40 tun lokacin da Ummie tabar nigeria Suka taho tare.

da fara'a Ummie ta tarbeshi suka nufi daining ita kuma Maryam ta durƙusa tana gaisheshi with so much respect, murmushi kawai ya sakin mata sannan ya wuceta ba tareda ya amsa ba Hajiya Aisha da kanta tayi sarving nashi Abincin wanda keta zuba uban ƙamshi sannan ta miƙa masa itama ta xauna ta fara zuba nata Abincin wanda keda banbanci danasa kasancewar tanada ciwon suger

Kusan a tare suka fara cin Abincin har wani lumshe ido Muzaffar keyi sabida DaÉ—in Abincin hakan ne yasa yaci sosai har ummie tayi mamakin hakan, dabida a iya sanin datayi masa bayacin abinci sosai.

bayan sun gama cin Abincin ne Maryam ta miƙe ta kwashe kayan Abincin takaisu kicin tareda gyara gurin, zama sukai a falon suna ɗan taɓa hira duk akan abinda ya kawoshi Indian wani tayi murmushi wani kuma ta kalleshi, wayarta ce tayi ƙara hakan yasa ta maida hankalinta ga wayar tareda karawa a kunnenta Tace "bayi zamuyi magana yau insha Allah komai ze kammala ba tareda anci lokaci sosai ba. Ta faɗi hakan tana satar kallon muzaffar wanda ya maida duk hankalinsa akan System ɗinta dake gabansa,

a nitse yake gabatar da komai cikin nutsu ba zato ba tsammani yaji cikinsa yay wani irin juyawa tareda muɗa masa, dafe cikin yayi da duka hannayensa tareda zube gwiwowinsa a ƙasa ya saki wata irin ƙara wadda ta firgita Hajiya Aisha da me aikinta Maryam dake kicin tana wanke kwanikan da akaci abinci dasu, Sakin wayar Hajiya Aisha tayi tareda nufo kansa gadan-gadan tana raba idanu hanyar kicin ta kalla ganin babu wanda ya taho yasa ta ɗagoshi tana kallon fuskarsa kimanin 5second jin tafiyar Mutum daga hanyar kicin ɗin yasa itama ta saki ihun neman taimako. A gigice maryam ta ƙaraso gurin idanunta duk a waje sabida tashin hankalin tareda kallon Ummie lokaci guda kuma ta sake maida kallonta ga muzaffar wanda ke fitarda wata irin farar kumfa daga bakinsa hakanne ya bata tabbacin cewar Guba yaci.

cikeda tashin Hankali maryam ta dora hannu akanta tana faÉ—in "innanillahiw'inna'ilaihirraji'un!!!!!!

a gigice maryam ta nufi wayar telho ɗin dake ajiye bisa wani ƙaramin table ta shiga wayar Babban Asibitin kuɗin dake kusa dasu ko'a samu a ceto Rayuwarsa cikin Sauƙi.

Ummie kuwa ta kasa motsin kirki balle har ta tsinana wanu abin arziƙin a gareshi, take wani irin gumi ya fara keto mata tareda nadama mara misaltuwa babban abinda ke ɗaga mata hankali a wannan lokacin shine da wani ido zata kali Abie bisa wannan abinda data kasance itace silar Faruwarsa?

tabbas duk irin sonda yake mata a wannan lokacin ta tabbata bazata tsira ba daga hannunsa shida matarsa Saratu ba tunda har tayi poisoning É—in dansu namiji tilo........

*GYMBU TARABA STATE*

Da ƙyar Inna Laure kejan numfashi sabida tsabar azabar datakeji ko hannunta ta kasa ɗagawa balle tasan ran cewar zata iya miƙewa, seda suka gama zuba Rashin imaninsu sannan suka tattara komai suka tafi dashi tareda ketawa Yara ƙanana haddinsu, a wannan rana rayuka dayawa sun sosu da baƙin ciki mara misaltuwa haka kuma zuciyoyi sun baƙanta, a wannan tsukun ne Mahaifin Ruƙatu Babbar Aminiya ga Rabe ya rasa Rayuwarsa al'amarin daya ƙara ɗaga mata hankali kenan.

sosai malam iro ya zubar da jini sosai har hakan yasa suka fitar da rai da cewar ze tashi, moddibo kuwa gabaɗaya ya kasa cewa komai duk a sanadin bala'in daya sameshi, baya iya furta komai se ido kawai dayakebin kowa dashi, miƙewa yayi ya shiga ɗakinsa da sauri ya kauda kansa sabida ganin irin Rashin imanin da suka aikatawa Laure komai bushewar zuciyarka dolene ka tausaya mata muddin kanada imani, da sauri ya isa gareta sabida ganin yanda jini ke zuba daga ƙasanta duk yamda yaso ya taimaka mata kasawa yayi dole ya zube a gurin ya saki kuka me sauti da ban tausayi, itama kanta Lauren kuka takeyi tareda tausayawa kanta a irin Rayuwar dazata fuskanta nan gaba

seda yayi me isarsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin ya haɗo ƙirare ya kunna wuta tareda ɗora ƙatuwar tukunya akai, cikin mintunan da bazasu gaza 20 ba ruwan ya tafasa wata babbar fanteka ya ɗakki ya zuba ruwan a ciki kimanin rabin fantekar sannan ya ɗauka ya shiga da ita ɗakin ya zuba wani garin magani a ciki take kallar ruwan ta sauya zuwa launin kore, seda yaɗan sha iska sannan ya kinkimeta ya zaunar da ita cikin ruwan, wata uwar ƙara ta saki har seda ta bashi tausayi

cikin ikon Allah jinin ya tsaya har taji ɗan dama-dama a jikinta, seda ya gana bata duk wani taimaki dayake ganin ze iya bata sannan ya fita zuwa waje ya fara duba sauran jama'a ba tareda ya damu da jinin dake zuba a kansa ba. *_(Allah sarki modibo haqiqa kyakkyawar zuciyar halitta ce ba kowani mutum ne ke tuna al'uma ba a lokacin da musiba ta sameshi ba, kowa kansa yake fara ginawa sannan daga baya ya tuna da al'uma amma shi kuma moddibo yace "al'uma itace farko kafin kansa. Ya Allah ka cire mana son kai da ƙyashi daga zukatan mu🤲)_*

A hakan seda ya tallafawa kowa sannan ya agazawa kansa daga baya. Baze iya furta komai ba a irin wannan halin baƙin cikin dayake ciki ba, amma yana roƙon Allah ya saka musu bisa zalincin da aka aikata musu

******

The fulani girl Tafiya take tana kallon titin kmaar wata me koyan tafiya ba zato ba tsammani wasu farar mota sol ƙirar formatic C350 Da suka taho cikin jerin gwanonsu kimanin guda 6 ta gaban tai sama da Ita, take ta zube a saman kwantar jini na ɓulɓula ta hancinta da kunnuwanta!!!!

A gigice Drivern dake motar ya fito take motocin dake binsa a baya suka tsaya sabida ganin tsayawarsa, kwance yake cikin motar dake tsakiya yana latsar waya yaji motocin sun tsaya, dago madaidaitan idanunsa yayi yana kallon drivern dake jan motar dayake cikin yace "what's wrong?
Chapter 18 · 0% Book details