← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 57

Sashe 42

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ohh ai gashi nan kai naga tarbiyar a tareda kai, look I don't want to repeat my word and karka bari raina ya ɓaci maza- maza ka ɗauki yarinyar nan ta barmin gidana yanzu base anjima ba, idan yaso seka idan zaku iya kaita duk inda kukeso amma ba nan ba tunda har sabida ita Murja kike iya marin ƴata kaikuma Edriss kake jayayya dani.... "don girman Allah Dad kayi haƙuri karka yanke hukunci cikin fishi, na tabbata don baka zauna da ita bane shiyasa kake ganin kamar ita ɗin ba'abar a zauna da ita bane dad, amma wllh tafi yaya Hajar halaye masu kyau nesa ma ba kusa ba sannan kuma dad ko kaine kaga abinda yaya Hajar tayiwa baiwar Allahr nan kaida kanka zaka hukunta tat....... Haɗiye maganar Zeeyadah tayi sabida wani ɗan iskan kallo da Dad ke binta dashi

Miƙewa yayi a fusace ya kalli Edyan yace "maza ka ɗauketa ta barmin gidana yanzu base anjima ba, kuma wllh muddin bakayi abinda nace ba seƙaga fushina

Miƙewa Hajar tayi zuciyarta fessss tabi bayan dad, kokaɗanbataji komai ba akan yanayin data saka mahaifiyarta a ciki ba da ƴan uwanta.

Iya ɓacin rai ran Edyan ya gama ɓaci har wani irin ɗaci yakeji a saman maƙoshinsa, kasa cewa komai yayi yaja hannunta sukabar falon zuwa part ɗinsa suna shiga Direct bedroom Ɗinsa ya wuce still yana riƙe da hannunta, zaunar da ita yayi a bakin gadonsa se faman murza idanunta da suka koma kalar ja takeyi sabida kukan datayi, miƙewa yayi zuwa gaban drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko wannan jakar saƙin daya tsinceta da ita sannan ya dawo gabanta ya zauna akan dandiryan ƙasan carpet ɗin tareda zuba mata manyan tsimammun idanunsa Cikin harshen turanci ya farai mata magana donya fuskanci zuwa yanzu tafi ganeshi Sosai akan Hausa yce " tunda muka bugeki da mota naji a raina cewar tabbas akwai wani babban al'amari a tareda Rayuwarki, haka kuma daga yanayin ƙwayar idanunki na ƙara tabbatarwa da kaina cewar lallai a kwai ciwo a Rayuwarki wanda kike ɓoyewa har yanzu kin gaza sanar da kowa. Bazan tilasta ki cewar lallai sekin sanar dani labarin Rayuwarki ba Mulaikha kawai nidai inaso na taimakeki dukda cewar har ynzu bansan wacece ke ba, a shirye nake na fuskanci ko wani irin ƙalu bale a rayuwata muddin hakan zesa ki haɗu da iyayenki no matter what!!!! Ya faɗa tareda ɗora mata jakar Sakin akan ƙafafunta

Jikinta ne yay wani irin sanyi duk a sanadin kalamansa da yay amfani dasu na ƙarshe, lokaci guda taji wani abu ya tsirga mata a tsakiyar ƙirjinta a gameda Edyan ɗin a zahirin gaskiya ta daɗe da bashi wani mashahurin matsayi wanda ya zarta na musamman a cikin zuciyarta tunda Allah ya haɗata dashi a cikin littafin ƙaddarar ta, daƙyar ta iya tsayar da hawayen dake zubo mata bakinta na wani irin vibrateting tace " Sunana Rabi'atou Abubakar Moddibo ne, kuma ni haifaffiyar jihar tarabace, Mahaifina makiyayi ne na taso cikin maraicin Uwa sedai dukda hakan besa Mahaifina ya gaza nuna min ƙauna daga ɓangare biyu ba, ma'ana ya gama cike duk wani ɓangare a gareni dazesa na tuna cewar na rasa kulawar Mahaifiyata. Nan dai ta kwashe komai ta sanar da Edyan har zuwa ranar da ƙaddara rabuwa samu nasarar giftawa a tsakinin Mahaifinta.

Wani irin kuka ne ya kufce mata don haka ta shiga rerawa kamar bazata dena ba, koda wasa beyi yunƙurin hanata kukan ba dinya fahimci a wannan lokacin babu abinda ze sama mata nutsuwa kamar kukan, seda tayi me isarta sannan ya shig ashare mata hawayen yace " it's OK dear insha Allah I will make sure naga kin koma gaban mahaifinki lfy ba tareda wani abu ya sameki ba koda hakan yana nufin bazan dawo namu gidan da numfashi b...... Da sauri ta ɗora hannunta akan pink soft lips ɗinsa tana hawaye tace "stop saying that partner insha Allah babu abinda ze sameka sai alkhairi.

Murmushi yayi me sauti wanda ya ƙara baiyana kyawunsa sannan ya miƙe tareda janyo wata babbar trolly dake ajiye can gefe yazo gabanta ya tsaya yana kallonta ido cikin ido ba tareda ya iyafurta ko kalma ɗaya ba, itama kallonsa take a karon farko a rayuwarta dashi Wani irin abu ne ya tsirga musu a lokaci guda da sauri ta ɗauke idanunta daga kansa ƙirjinta na bugawa da ƙarfin gaske, hannunsa ta tsinkaya a daidai satin fuskarta alamar tazo su tafi ba musu ta ɗora hannunta ya Bisa tattausan hannunsa suka fara tafiya. A bakin ƙofar sukai kaciɓus da mom idanunta duk ya caɓe da hawaye da wani irin mugun sauri ta nufi Rabe ta rungumeta tana ƙara sautin kukanta.

******

NEW DELHI INDIA

Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara da kuma sa'a, sosai jikin moddibo ke ƙara samun sauƙi tamkar bashi ba har wani irin haske ya ƙara sabida yanda yake samun kulawa daga masu alhakin akan hakan, sedai har kawo yi wannan lokacin basuyi ido hudu da Muzaffar ba, a lokacin daya farka yaga fararen fata suna kai kawo a cikin Asibitin yayi zaton mafarki yakeyi kokuma ƙiyamarsa ce ta tsaya, shiru yayi yanabin ko wace kusurwa ta ɗakin da kallo har zuwa haɗaɗɗen gadon dayake kwance a kai, shigowar Dr. Rahul Gufta ne ya ƙara firgita tunaninsa musamman dayaga kyawawan mata sanye da fararen kaya a jikinsu ya ɗauka Mala'ikun da akace suna zuwa yiwa mutum tambaya ne a cikin kabarinsa yayinda aka binne shi, da sauri ya rintse idanunsa yana yana ambatona sunayen ubangiji tareda neman sauƙi wajen amsa tambaya😂

Dubashi Dr. Rahul yayi tareda duban Nurse din dake bayansa yace "ta bashi abinci sannan yasha magani. Cikeda girmamawa ta amsa da "ok sir. Juyawa yayi yabar ɗakin yana murmushin ganin tarin cigaban da suka samu a cikin tiyatar zuciyar da sukayiwa moddibon. Da ido kawai Moddibo kebin nurse ɗin a ransa yace "kodai tashi yayi a wata duniyar ta daban Batareda ya sani ba? sedai dukda irin abubuwan dayake facing besa tunaninsa yayi ƙaura daga kan tilon ƴarsa Guda ɗaya ba wato Rabe, a kullum Be taɓa gazawa dayi mata Addu'ar alkhairi ba kullum addu'arsa shine a duk inda take ubangiji ya tsare masa ita da tsarewarsa. Wasu lokutan har kuka yakeyi idan abin ya isheshi

A haka harya kwashe satin biyu cur yana jinya a cikin babban Asibitin dake cikin Birnin New delhi ɗin ƙarƙashin kulawar Dr. Rahul Guftah sannan yasan wanda ya ɗauki nauyin aikin nasa wato Muzaffar, lokacin daya sani seda ya zubar da hawaye masu yawan gaske, da ƙyar muzaffar ya rarrasheshi yayi shiru sannan suka shiga hirar yaushe gamo.

Cikeda kunya muzaffar ya É—ago manyan idanunsa yana kallon Baffa yace "Baba ya Rabi'atou take? Lokacin danaje hankalina ya tashi ban samu zarafin haÉ—uwa da ita ba. Ya faÉ—a bakinsa na rawa cikeda tsoron karaya ce masa tayi Aure.

Kafeshi d ido modɗibo yayi take wata sabuwae ƙwalla ta zubo masa cikeda karayar zuciya ya shiga sanarwa da muzaffar ɗin abinda ya faru. Wata irin zabuwa muzaffar yayi jikinsa na wani irin rawa kamar mazari , bakinsa na rawa yace " k...kkkk....kana nufin Matar tawa ce ba'asan inda take ba?

Ya faɗa yanayinsa na ƙara sauyawa kamar wani bugagge

Kallon da moddibo ke masa ne yasashi haɗiye maganar dake maƙale a maƙoshinsa.

Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad 🥰

Sushmah✍️[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :42

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*

*_Allah yayiwa Mahaifin Mamana Rasuwa a jiya 5/12/2020 ina roqonku arziqi don Allah ku sanyashi a cikin addu'oinku ubangiji yay masa Rahama tareda sauran musulmai baki ɗaya Amin😭_*

Banyi Editing ba kuyi haquri👏

____✍️ Daga irin kallon dayake binsa dashi ne yasa moddibo ya fahimci irin zallar soyayya tareda muradin dake cinsa a zuciyarsa tabbas wannan ƙaunar dake gudana a jinin muzaffar ba ƙarama bace ta zarta duk wani hasashensa, amma kuma a zahiri seya basar tamkar be fahimci komai a tareda yanayin nasa ba kokuma inda ya dosa ba, ya jima yana kallonsa daga bisani kuma ya kauda kansa gefe zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske

rintse idanunsa muzaffar yayi da ƙarfi lokaci guda kuma ƙijinsa ya shiga bigawa da wani irin ƙarfi ji yake tamkar ana janye masa jini da ruwan dake gudana a duk wata gaɓa ta jikinta, se'a yanzu yakejin cewar tabbas be kyautawa kansa ba da har ya kasa fahimtar ma'anar abinda ke gudana a cikin ransa seda lokaci ya ƙure masa, dafe kansa yayi da dika hannayensa biyu tareda zubewa akan wata lallausar kujera dake gefansa.

Wata irin zuface take keto masa dukkuwa da irin sanyin Ac ɗin dake ɗakin, kallonsa kawai moddibo keyi a ransa yana mɗe tausaya masa duk a sanadin halinda zuciyar Muzaffar ɗin ke ciki, tabbas baya buƙatar ƙarin bayani akan irin son da muzaffar ɗin keyiwa ɗiyarsa domin kuwa duk amsar dayake son tabbatarwa da kanso ƙwayar idon muzaffar ɗin ta gama nunawa.

Ajiyar zuciya kawai yake saukewa Akai-akai tamkar wanda ya gwabza tsere da ingarman doki maji ƙarfi, lokaci-lokaci yakan dunƙuƙe hannunsa ya daki ɗaya tafin hannun nasa dashi, miƙewa yayi da nufiknbarin ɗakin da sauri se kuma ya tsaya cak ba tareda ya juyo ba yace "tabbas zan sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina bawai a matsayin babban yaya kawai ba Baffa, zanyi hakanne ta wata fuskar daban a matsayin Jajirtaccen masoyi wanda zuciyarsa ke cike taf da zallar ƙauna me haɗe da sirkin muradi a cikinta, zan hakanne tareda yaƙinin sauke nauyina a matsayin mijin Aure ga Rabi'atou!!!!!

Ya faɗu hakan tareda ficewa daga ɗakin cikin wani irin saurin da tunda yake betaɓa sanin yanadashi ba a Rayuwarsa, da ido kawai Moddibo ya bishi harya ɓacewa ganinsa a ransa kuma yana jinjina irin girma da tasirin muradin dake gudana a cikin jinin muzaffar ɗin wanda abu ne mawuyaci zuciyar dake ɗauke da wannan nauyin ta samawa kanta hutu koda na sakan guda ne.

Tausayinsa ne yay masa dirar mikiya lokaci guda kuma ya sanya hannunsa ya share hawayen daya zubo masa na tausayin rayuka biyu, ta wani ɓangaren ɗiyarsa dabe san irin halinda take ciki ba, ta wani ɓangaren kuma tausayin halinda zuciyar muzaffar ke ciki.
Chapter 42 · 0% Book details