← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 57

Sashe 45

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke kan dining suna cin abinci Abie yake sanar da Ummie Batun tafiyar moddibo da safe idan Allah ya kaimu, Shiru tayi tana kallon Abie É—in ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba Lokaci guda kuma yanayinta ya sauya,

A hankali tace" daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?

Murmushi Abie yayi sannan yace "wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya qara kwana ki Kidan sabida batun lfyarsa ma.

Dik wannan hiran da suke itada Abie qarfin hali kawai take Haka kawai setaji wani iri haka a jikinta sabida mutumin yayi mata abinda bazata taɓa mantawa dashi ba a Rayuwarta.

Abie ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,
Murmushi Ummie tayi sannan tace " Abou muzaffar kenan sekace wasu yara?

Dariya yayi sannan yace " au yara ne kawai suke da hurumin yin soyayyah?

Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi Da ita,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe.
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yanayinta ya canza tunda ya ambaci Tafiyar moddibbo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa Ta canza lokaci guda haka?

A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai Koda kuwa menene shi, a daddafe ya kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din shima a zaune ya sameta da alama daga toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tana cikin damuwa, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush sannan yayi wanka yafito, beyi mamakin ganin ta ajiye masa jallabiya ba sbda hakan al'adarta ce, murmushi yayi sannan ya sanya Jallabiyar a jikin sa.

yana gama sawa Ya haye gado abinsa bece mata komaiba yaja bargon Dake gefanta da nufin ya kwanta, donya qudurtama kansa cewar baze taɓa tambayarta dalilin sauyawarta ba sabida ita kanta tasan hakan na mugun ɗaga masa hankali shiyasa ma tayi.

Da kanta ta fahimci Tayiwa megidan nata laifi dan hka ta bude baki tace "don Allah kayi haquri bani da yanda zanyi ne dolece tasa,
Sanin kanka ne kasan bazan taba mantawa da irin binda wannan baƙon mutumin yayiwa ɗana ba, sannan kuma taya kake tsammanin zan iya jure ganin halinda ɗanmu yake ciki a sanadin soyayyar yarinyar da bamuda tabbacin sanin inda take a halin yanzu?

"meyasa bazakayi amfaninda damarka ta mahaifi ka nema masa aurenta ga mahaifinta kafin ya tafi ba?

"Haba Aisha so nwa kikeso muyi maganar nan ne sabida Allah? Nayi magana da bawan Allahn nan ya cemiɓ a kwai maganar Auren wani akan yarinyar shikenan kuma sena matsa masa akai don kawai inada kuɗi kuma inason ɗana?

Kuri tayi masa da ido se kawai ta fashe Masa da kuka.
Sosai Take kukan wanda ita kanta Bazata iya cewa ga dalilin Yin kukan Nata ba. Ganin abin nata bame qarewa bane yasa me Gidan nata ya Jawota jikinsa yana me bibbiga bayanta, seda ta tsagaita da kukan sannan ya dafata ya Fara mata nasiha sosai tareda sake nuna mata mahimmancin yarda da qaddara,
Jikinta ne yayi sanyi sosai a hankali Tasa hannunta tajaa bargon dake gefanta ta kwanta Bisa jikinsa tana sauke numfashi, seda ya tabbata ta nutsu sannan ya fara tambayarta Kan cewae me take ganin zeyiwa moddibo idan ze tafi sbda nuna jin dadin abinda yayiwa dansa Wanda yasan ko duniyar nan yabashi be biyasa ba?

Murmushi Ummie tayi me sauti sannan tace "ka bari tukunna seda safen mayi maganar.
Bata qara cewa komaiba tayi addu'ointa ta tofa, ba jimawa bacci Me nauyin gaske ya dauketa.

****
Bangaren su muzaffar kuwa hira suke sosai da moddibo sekace ba dare ba, sun jima suna hiran sannan moddibo ya tashi ya wuce daki sbda bacci daya ke ji, kuma gashi fitar wuri yake so yayi,

Murmushi muzaffar yayi tareda Fadin seda safe. A hankali ya tashi ya kashe TV ÆŠin daketa faman aiki sannan ya rage Ac dake falon sannan ya rage wutar falon ya mike ya nufi bangaren sa, bisa ga mamakin sa seyaga an qara gyara masa Part É—in nasa , ko ba'a fada ba yasan Aikin zaynab ne,
Murmushi yayi sanan yace" Allah sarki my Qurrah
Wanka yayi sannan ya fito daga toilet din sanye da wata farar jallabiya, dik da cewa shirin bacci yayi amma rigar ba qara min kyau tayi masa ba, a hankali ya qraso bakin makeken gadon sa qirar Italian ya zauna yayi shiru, kallo daya zaka yimasa ka fahimci damuwa a fiskarsa,
Wani abin hannun roba dake hannunsa ya taba se kuma ya saki wani tattausan murmushi, a hankali ya firta "I miss you My darling Fulani girl, I miss everything about you. murmushi ya sake yi a karo na biyu sannan ya hau gadonsa yaja Lallausan bargon dake gefansa ya kwanta, ya jima yana nazarinta tareda Tina wasu abubuwan da suka wakana a tsakaninsa da ita gami da yawan murmushin ta sannan bacci yay a won gaba dashi.

Kiran sallar farko moddibo ya mike ya shiga toilet yayi Wanka Sabida zamansa a india yasa ya koyi amfani da banÉ—akunan zamani, alwala yayi ya kimtsa Sannan ya fita zuwa
Masallaci, yana shiga masallaci ya gabatar da raka'atanul fijir bayan ya idar ya dan jima a zaune yana addu'ah sannan aka gabatar da sallar asuba,
Bayan ya fito masallaci suka hadu da muzaffar suka wuce gda suna hirarrakin su,
Ban garan moddibo suka nufa ya tayashi ya hada kayan sa ya daure Su tsaf guri guda.

seda gari yayi haske sannan Abie ya shigo bangaren dan su gaisa da moddibo, bayan sun gaisa ne Dady yace masa yazo su gaisa da mahaifiyar muzaffar sannan yayi breakfast, se su wuce, murmushi moddibo yayi sannan ya CE to babu damuwa idan ka shiga seka sanar da iyalin Naka shigo war tawa,
Murmushi Abie yayi sannan ya kalli muzaffar yace "ka shigo dashi falon Ummien ka idan ya kammala Inyaso bayan sun gaisa da ita Ummien seka kira Saratu itama su gaisa. murmushi Muzaffar yayi ya amsa da to Abie as you wish

Abie na shiga ya sanar da Ummie cewar moddibo ze shigo yayi mata sallama, murmushi tayi sannan tace gaskia be kamata ya tafi yanzu ba dama ya qara mana kwana 2 murmushi Abie yayi Nandai sukaita hira abinsu.

Mamie tace ina zuwa naji kamar abinda na Dora yana kamawa , kichin ta nifa dan ta sauke abinda ta Dora,
Tana fita su moddibo da muzaffar suka shigo falon, guri muzaffar ya nuwa moddibo sannan ya zauna shima Daga gefansa hira suketa dan yi da Abie itama jefi-jefi, a haka Ummie ta fito ta samesu, ko kadan moddibo be kalli fiskarta ba itama haka ta qaraso falon fiskarta dauke da murmushi a nitse ta zauna a gefan Abie sannan ta fara gaida moddibo.

a nitse ya fara amsawa cike da kulawa, Lokaci guda Ummie ta ɗago fararen idanunta ta saukesu akan mamallakin muryar data doki dodon kunnenta, Wanda har duniya ta tashi bazata taɓa manta mamallakin wannan muryar ba.

Kallon moddibo take haka shima kallon Nata yake cike da tashin hankali yake nuna ta da yatsa,
Kasa cewa komai yayi dan haka kawai ya miqe da nufin yabar falon gaba daya,

Da sauri Ummie ta riqe qafafuwansa tana Wani irin kuka me tsima zuciya, cikin kukan take fadin dan Allah Baffa iya kayi haquri ka yafe min nasan nayi kuskure a rayuwa ta yanda bazan Iya gyara laifi nab!!!!

Ta qarasa maganar tana kuka sosai.

Cike da rashin fahimta Abie yake kallon su haka ma muzaffar da kansa ya gama daurewa,
Cike da damuwa Abie yake tambayar Ummie shin tasan moddibo ne Kokuma ya abin yake?

Shin meye hadinta dashi da har take fadin ya yafe mata?

Da qar ta Iya bude baki tace "dan uwa nane shine yayana moddibo da mukaje nema shekaru a shirin da biyar da suka wuce, to shine wannan ta qara fashewa da kuka,

Qarfin hali moddibo yayi ya fisge qafarsa daga hannunta ya fice daga falon da sauri yana zubar da hawaye,
Ko kayan sa be Tsaya dauka ba ya fice daga Gidan gaba daya,
Yana fita ya samu Taxi ya shiga batare da ya gaya masa inda ze kaishiba !!
Seda suka fara tafiya DaÉ—an jimawa sannan me motar yace "mlm INA zan kaika?

A taqaice Moddibo yace " masa tashar mota zaka kaini don Allah Inda zan samu motar TARABA.

Shiru mai motar yayi a tareda jefa motar kan titin daze kaisu tashar JABI

suna iya ya kwanto kuɗinsa ya miƙa masa yakoyi sa'a cikon mutum ɗaya ake Nema, Be wani bata lokaci ba ya biya kuɗin motar ya shiga ya zauna still hawaye na zuba daga cikin idanunsa sabida wani irin suya da zuciyarsa keyi masa.

*****

Tun bayan tafiyar moddibo Ummie take kuka, gaba daya hankalin Abie ya gama tashi yama rasa me zeyi guri ya samu ya zauna tare da dafe kansa daya ke masa wani irin nauyi,, falon ne yayi shiru baka jin komai se sautin kukan Ummie, muzaffar ne yayi qarfin halin cewa Abie sam wannan zaman fa ba shine mafita ba fa,
Kawai tashi zamuyi mubi bayan sa, nasan ze sauraremu inayaso se'a gyara matsalar Ina ganin hakan zefi da wannan zaman da mukeyi,

cikin kuka Ummie tace "wllh nasan halin sa muzaffar yana da matiqar haquri amma idan yayi fishi yana da wuyar sha'ani!

A hankali Abie ya sauke ajiyar zuciya sannan yace " abinda muzaffar ya fada shine daidai ki tashi kije ki wanke fuskarki ki shiya mubi bayansa hakan shine mafita.
Chapter 45 · 0% Book details