← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 57

Sashe 53

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karɓa tayi itama tana dariyar tace "hmmmmm nikam ban taɓa ganin mutum me son suger kamar Abie ba ko tsoron shan zaqi bayayi. Ta faɗa tana karɓar kwanon tareda zuba masa suger ɗin ta miqa masa ya karɓa ya fice daga ɗakin, yana fita zeeyadah ma ta miqe tabi bayansa da sauri tace "ya Edyan wai ina ne ɗakin mulaikha ne ?

Murmushi ya sakin mata tareda nuna mata bukkar sannan yay gaba abinsa, da sauri Zeeyadah ta nufi É—akin cikeda zumuÉ—in ganin mulaikhanta bakinta É—auke da sallama ta shiga

A kwance ta sameta idanunta a lumshi bisa qaramar katifarta, da sauri zeeyadah ta isa gareta tareda faɗawa jikinta tana dariya, buɗe lumsassun idanunta Rabe tayi waƴanda sukai mata masifar nauyi akan zeeyada lokaci guda kuma ta miƙe zaune ta rungumeta, kukan data daɗe tana dannewa ne ya samu nasarar kufce mata don hkaa ta shiga rerawa a jikin Zeeyadan tamkar dama jira takeyi ta ganta

ÆŠan buÉ—a idanunta Zeeyadah tayi cikeda damuwa ta zarota daga jikinta tana kallon fuskarta wadda ta jiqe da hawaye tace " meyasa kike kuka irin haka Mulaikha shin bakya tsoron kanki yazo yanayi miki ciwo? Koma dai wani abin ne yake damunki ne?

Hannunta tasa ta goge fuskarta sannan ta kama hannun zeeyadah tace "ina so naga Partner yanzu pls!

Wayar hannun zeeyadah ta karɓa da sauri ta shiga kiran Edyan, bugu ɗaya ya ɗauka tareda faɗin ya akai ? Duk a zatonsa zeeyadah ce

Bakinta na Rawa tace " i wanted to see you plssssssss!

Take qirjinsa ya wani irin buga wanda sam be shiryawa hakan ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yace "ok bt where are you nw?

Zan jiraka a bayan gida wurin shanu. Rabe ta faÉ—i hakan a taqaice

Katse wayar yayi tareda zubawa qasan gurin idanu sannan ya miqe ya fita yabarsu Abie da moddibo sunata hira abinsu, jikisa a saluɓe haka ya isa gurin ya sameta a tsaye ta sarqe hannayenta duka biyun a qirjinta tana jiran isowarsa.

Ya jima a tsayen sannan ya buɗe baki yace "kinaso ki faɗamin wani abun ne? Hawayene suka zubo mata sannan tasa hannunta ta goge ba tareda ta kalleshi ba tace " inaso na gaya maka abinda ya kamata ace ka sani ne patner, dukda cewar kusancinka da muzaffar ya wuce akirashi da abota sedai a kira hakan da sunan ƴan'uwantaka, partner Muzaffar yanada wata budurwa a Rayuwarsa wadda ya jima yana ɓoye abinda ke ransa tsahon lokaci.

ÆŠago idanunsa yayi cikeda matiqar kaÉ—uwa ya dubeta yace "wannan wace irin magana ce kikeyi haka Mulaikha?

Ae haka maganar take Partner amm......." toni meyasa kike zaɓi da ki gayamin wannan wannan maganar bayan kuma shida bakinsa be taɓa gayamin ba?

Hawayen daya zubo mata ta sake gogewa tace " wasu maganganun da wanda yake qaunarka kawai zaka iyayinsu Yaya Edyan, musamman akan abinda ya shafi rayuwar ka!

Ni kawai abu ɗaya na sani shine wannan Auren daza a ɗaura min a gobe muddin na Bari akayishi shine kuskure mafi girma da zan aikata a rayuwata, wllh partner banason shi kaina gaba ɗaya ya gama kullewa banaso na aikata abinda ze taɓa kimar mahaifina!!!!!!! Ta fadi hakan tana fashewa da wani irin kuka.

Kafeta kawai da idanu Edyan yayi a ranaa kuma yana aiyana wani al'amari wanda shi kansa bazece ga matsayar daya samu a ransa ba, tabbas yasani har cikin zuciyarsa yake qaunar Rabe so me tsananin gaske, to waishin ta ina ma ya kamata ya fara ne?

A hankali yake jan qafarsa harya bar kurin ba tareda ya rarrasheta ba, guri ya samu daga can nesa da gidan ya zauna har yammacin al'muru ya fara ketowa, a hankali yaji saukar hannun mutum a saman kafaÉ—unsa don haka ya É—ago da sauri yana kallon wanda ya dafashin.

Moddibo ne tsaye bisa kansa yana murmushi yace "ai tun É—azu nake cigiyar ka shine Abou muzaffar yace min kanata nan wurin. Ya faÉ—i hakan yana zama daga gefan Edyan É—in, shiru ne ya ratsa gurin tsahon lokaci sannan moddibo ya dubeshi yace " na rigada na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna. Da sauri Edyan ya É—ago yana kallonsa zeyi magana moddibo ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Ba yanzu ba tukunna zan baka damar magana amma fa har sena gama tawa tukunna.

Wanda takeso ɗin na zauna dashi a yanzu dukda cewar shiɗin be taɓa furta abinda ke zuciyarsa akanta ga kowa ba, dukda cewar yasan hakan kurkurene me girman gaske amma kuma yake qoqarin ya aikata ɗin, nariga na gama Fahimtar komai Edriss nariga na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna har cikin Ranta,, idan harna Aurar da ita ga wanda bataso tabbas na cutar da ita mafi girman cutarwa, nasani damace ubangiji ya bani a yau wadda zan iya gyara kuskuren danake qoqarin tabkawa a baya ta hanyar turo min kai zuwa nan, koda wasa bazance Bamanga da Rabi'atou basu dace da juna ba amma to ya muka iya da zannan abinda qaddara tazo mana dashi?

Zuciyata tana gayamin cewar kaine mutumin dayafi dacewa daya mallaki Rabi'atou. Da sauri Edyan ya kama hannun moddibo lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga fuskarsa yace "aa baba sam be kamata kayi haka ba, kamata yayi ka zauna da Rabi'atou kaji ra'ayinta akan Aurensu da bamanga muddin ta nuna batason haka toseka sake bata wata damar a karo na biyu inyaso seta gaya maka waye zaɓin ranta da bakinta!!

Da hka hirar tasu ta dasa Aya.

Ɓangaren su Mom Edyan da Ummie kuwa sosai suka kacame da hidimar dafe-dafe da kuma sarrafa wasu abubuwan daza'a gabatar na al'adah, sosai mata suka cika gidan anata shewa da kuma aikace-aikace kafin kuma gari ya waye a shaida ɗaurin Aure. Bayan sallar Isha su Abie da Edyan da kuma gurds ɗinsa suka yada zango a farfajiyar qofar gidan kafin lokacin kwanciya yayi, miƙewa moddibo yayi ya nufi bukkar Rabe da sallama ɗauke a bakinsa ya ɗaga labulan dake saqale jikin bukkar, zaune suke ita da zeeyadah tanata faman bata labarin school Rabe nata murmushi a haka ya qasa shigowa ɗakin, cikeda girmamawa Zeeyadah ta gaisheshi sannan ta miqe a nitse tabar ɗakin don ko ba'a faɗa mata ba tasan magana zayi da ita wadda take buqatar sirri.

Zeeyadah na fita ya nemi guri ya zauna daga ɗan gefanta kaɗan yana kallonta kimanin wasu mintuna Sannan yay ajiyar numfashi yace" idan kinada matsala da wannan auren sam karki ɓoye min kawai ki sanar dani insha Allah zaki sameni a matsayin uba me adalci a gareki.

Matsowa tayi tareda kwantar da kanta bisa kafaÉ—unsa tace " aa baba sam banida matsala da Auren bamanga sabida ya cancanci mallakata tsahon lokaci, don haka kawai a É—aura wllh har cikin raina na amince da hakan!!!!

Ta faɗa tana kallonsa tareda qoqarin mayar da kwallar dake qoqarin zubo mata, ko kaɗan bataso ta nuna gazawarta kodan sabida ta tsirar da kimar mahaifinta a idanun jama'ar garinsu, badan haka ba tabbas bataga dalilin dazesa tabar zaɓin ranta ta ɗau wani ba.

Duk yanda moddibo yaso ya gano abinda take ɓoyewa a ranta ta hanyar kallon idanunta sam ya kasa gano komai dole ya tabbatarwa da kansa cewar lallai har cikin ranta takeson Auren Bamangan. Ƙarfe tara na dare dedai Kakar Rabe wadda ta haifi mahaifiyarta sukazo daga Yolah tareda qannen mahaifiyarta guda biyu, sosai sukai farin cikin da zuwan nasu misamman ma Rabe wadda har hakan ya gaza ɓoyuwa a tareda ita a haka dai gidan ya dinga kacamewa da abikanan Arziqi tamkar a lokaci za'a ɗaura mata Auren.

****

Washe gari tunda sanyin safiya jama'ar Rugar Arɗo suka gama hallara a bakin qofar gidan moddibo wanda aka shimfiɗa manyan tabarmin kaba fa farfajiyar, Abie ne ya fito sanye cikin wata rantsatsiyar gizna fara fat da ita wadda taji uban aiki irina manyan masu kuɗin dake matiqar jida kansu, kallo ɗaya zakayiwa Abie ka fahimci zallar kar da suke da muzaffar tamkar Abie yayi kaki, bayansa kuma moddibo ne shima sanye cikin wata hamshaqiyar gizna farar tas da ita wadda tabawa kyawunsa damar fitowa abinka da bafulatanin Asali wanda yay gadon kyau ba taka haye ba lol😂

A haka suka fito suka zazzauna bisa tabarmin inda Jama'ar ke zaune, can na hangi Oga Edyan ya É—au harami shima cikin wata shadda irinta mutanam sinigal brown wadda tayi masifar masa kyau, sedai fuskarsa sam babu yalwar murmushi kamar yanda ya saba. Nan moddibo ya shiga gaisawa da abokan arziqi har ya kammala amma shiru babu labarin Isowar iyayen Ango, tun anasa ran isowarsu har mutane suka fara cire rai da zuwan nasu nafa aka fara tsegumi qana nan maganganu suka fara tashi, can kamar daga sama aka jiyo muryar Hashimu Maroqi yana faÉ—in "Sanarwa daga bakin uban Ango Jauro ibrahimu Bawuro cewar sun janyen batun Auren ÆŠansu Bamaga da kuma Rabi'atou É—iyaga Moddibo É—an lamidon ArÉ—o bisa wani babban dalili da basu baiyana ba, fatan malam moddibo ze gafarce su.

Take gaban moddibo yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da qwallar baqin ciki, yanzu shikenan Bamanga ya gama yiwa Rayuwar ɗiyarsa illah sabida a tsarin al'adarsu muddin wata matsala ta gifta a ranar ɗaurin Aurenki har takai ga an fasa ɗaura auren tofa har Abada bazaki taɓa yin aure ba a haka zaki zauna har mutuwarki ta riskeki.

Kamar daga sama Ya tsikayi muryar Edyan a saman kunnensa yana faÉ—in , dama can Mulaikha ba sa'ar Aurensa bace don haka ka koma ka sanar da qananan mutanen da Suka turoka cewar a yau base anjima ba za'a shaida É—aurin Auren Rabi'atou da wanda ya dace da ita.

Edyan ya faɗi hakan yana me zaro bandir ɗin ƴam dubu-dubu Guda biyu daga aljihunsa ya ajiye a gaban moddibo yace "Baba ina me nemawa kaina Aurenta idan har zaka bani, lokaci guda kuma Abie ya matso dabda moddibo yace "ni nan zan zame masa wakili daze karɓa masa Aurnta, cin qanqanin lokaci moddibo ya ɗago manyan idanunsa yana kallon Abie cikin wani irin yanayi wanda yafi kamada na zallar kaɗuwa yace"................

Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :51

*_WRITING BY: CHUBAÆŠO_*
Chapter 53 · 0% Book details