← Book details Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 57

Sashe 1

Bafulatana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[3/3, 5:21 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*_BAFULATANA_*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*Page - 1*

*WRITING BY :ZM CHUBAƊO*✍️

*WARNING! WARNING!! WARNING!!!*

*_THE BOOK BAFULATANA IS NOT FOR SALE, DUK WANDA YA SIYAR MIKI DASHI TO ƊAM DAMFARA NE WLLH, HKAA KUMA DUK WANDA YA SIYARMIN DASHI KO YA JUYA MIN SHI TA WATA FUSKAR BATAREDA SANINA BA ALLAH YA ISA🙅‍♀️_*

*_Da sunan Allah me Rahama me jinqai salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabin mu Muhammad (S.A.W). Ya ubangiji kayi min katangar qarfe da duk wanda ke shirin ɗaga min hankali a yanar gizo Ko waneneshi Mace ko Namiji🤲 sannan kayi riqo da hannuna wajen Rubuta dukkan abinda ze amfani al'umar musulmi gabaɗaya._*

*_wannan littafi ba Sabo bane tsoho ne zan sake faÉ—aÉ—a muku shi ta yanda waÆ´anda basu karanta ba A baya zasu samu damar karantashi , amma sedai salon zesha banban dana farko kamar yanda sunan littafin ya canza Salo daga BAFULATANA zuwa BAFULATANA RETURN. Fatan Ubangiji yasa mu Amfana da darusan dake ciki_*

***

*_GYAMBU ((TARABA STATE))_*

______Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne, cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata cikeda damuwa tace "wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.
Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace "to Rabe Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to "Baba.

Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta, tana Gama cirewa ta Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.

A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske, can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi, a hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma launin baki aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar, nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda tace musu, suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana lol

Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne yasa Duk yayu jajir Sabida jar Ƙasar dake hanya, haka tai ta shiga cikin ruwan dake kwance bisa hanyar tana bin shanun Suka kama hanyar gida, basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta Ƙarasa inda bukkokin su suke, da gudun ta ta Ƙarasa bakin Ƙofar da zata sada ta da Bukkar matar babanta da sallama ta shiga Ɗakin cikin harshen Fulatanci tace " inna na dawo.

cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa tace " Uwar me zan miki da kike gayamin kin dawo shegiya me mugun hali, Zaki fita ko sena fito naci ubanki shegiyar yarinya me baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa sabida baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare Tinda kikayo gadon tsiya. Inna ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya

Tunda ta fara maganar Rabe Ke kallonta cike da rashin fahimta dan harga Allah bata fahimci abinda Innah Lauren take nufi ba Sam, kullum tana gaya mata haka amma Sam abin Be taɓa damunta Kamar yau ba, tambaya ɗayace ke mata yawo a cikin zuciyarta a gameda maganganun inna laure shin meyasa kullum take Maimaita mata magana ɗaya babu canji? Shin meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan kawanakin nan?

Tana cikin duniyar tunanin datakeyi ne taji Saukar murfin kwano a daman goshinta!

Inna Laure ce ta buga mata tana huci lokaci guda kuma ta suri kwanon dake gabanta ta
Cike da Mugunta ta jefi Rabe dashi Daidai saitin hancinta aiko nan da nan Jini ya fara fita a goshin ta Da hancinta, gigicewa ta juya tana nemam hanyar fita daga bukkar Tana Neman agaji sabida Jinin data gani yana Zuba daga hancinta da goshinta, sosai ta gigice sabida a Rayuwarta batason ganin jini komai ƙanƙantarsa tsoronsa take ji. Da gudu ta nufi hanyar garken shanunsu Tana kuka sabida batado Babanta ya dawo ya gani tabbas bazata taɓa jin daɗin haƙan ba.

Karo taji tayi da mutum cikeda tsoro taja da baya zata fati taji an riƙeta gam, mahaifinta ne malam moddibo,
Cike da tashin hankali yake firta "innanillahi'wainnah'ilaihirraji'un

Cike da tashin hankali ya Jawota jikinsa tare da kama goshin Yana dubawa da sauri, hannunta Ya kama suka nufi ÆŠakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali take sauke numfashi sabida zafin da gurin ke mata cikin sanyi murya baban ya fara magana Kamar haka
"Rabi'atu kiyi haƙuri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce masa sbda bata da burin daya wuce ta illatamin ke, sanin kanki ne bani da kowa Daya rage mini a yanzu seke, tunda na rasa mahaifiyarki nakejin a raina cewar na rasa wani Ɓangare na rayuwata, shikuma dan Uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a bakin hanya, A kwai cuwuka sosai a cikin Rayuwata wanda banaso ma na dinga tunasu sabida yanda zuciyata ke zafi a sanadinsu. A sanadin mutuwar ɗan Uwama muka dena bin titi da dabbobin mu Har zuwa lokacin da mahaifiyarki ta haifeki, tunda na rasa iyaye na ban Ƙara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga baya Allah ya karbe Rayuwarya ta rasu ta barmin ke, tun kina shan nono a haka kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na Ƙara aure Kodan sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace " Banƙi shawararka ba Iro sedai inajin tsoron wace mace zan Aura wadda zata iya riƙemin Rabe bisa gaskiya da Amana?
Har ga Allah bana so Rabe ta rayu da ciwon maraicin Uwa A Rayuwarta Ko kaÉ—an. da kulawa malm Iro ke kallon Aminin nasa
Yayi murmushi yace "indai wannan ne ba wata matsa bace Moddibo zan baka Ƙanwata Laure ka aura nasan zata riƙeta da Dukkan gaskiyarta fatana kawai ka Amince da wannan batun Kuma ka kwantar da hankalin ka.

badan zuciyata taso ba na Amince Da maganar Auren laure, koda
malam Iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake murmushi a karo na biyu yace "indai Har ka amince ka aureta nikuma nayi maka alƙawarin zan zama me koyar da Ƴarka Rabe karatun addini Tayanda zata zama daban a cikin sauran yaran dake maƙotaka da Rugar mu. Ya ƙare maganar cikeda murmushi

Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikin Ƴata ba Auro. Moddibbo ya Ƙare maganar Yana Kuka

A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share mai hawayen dake Sauka a saman kumatunsa da tafin hanunta, seda moddibo Yayi kuka me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa Ya shafi gefan fuskarta yace "kinci abinci Kuwa? Da sauri ta ÆŠaga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata ci ba, Ta amsa masa da Ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta

Moddibo yay murmushi yace "to maza tashi ki tafi daukar karatun don kar lokaci ya ƙure miki banda tsayawa wasa kinji Allah, ya albarkaci rayuwar ki Rabe na.
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar Allon malm iro inda take daukar karatu,

Dik da cewar su fulanin daji ne amma Sam hakan Be zama illa garesu ba Kuma be hanasu karatun addini Ba, duk cikin sa' oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita da Ƙawarta Ruƙatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi auren ba,
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo Ɗaya zakai mata ka fahimci hakn, tana da manyan idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta sannan yana da dan fadi kadan, labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan tanada yalwataccen gashin kai ma'ana yana da tsayi sosai Irin na Fulanin Asali kuma ƴan gado, Rabe doguwa ce Sosai tayanda tsayinta yafi ƙarfin shekarunta, kallo daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin Usuli, Rabe miskilace ta ajin Ƙarshe magana ma ba damunta tayi ba Se idan ta zama dole, sedai Sam hakan baya hanata Gaida mutane
Chapter 1 · 0% Book details