← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 59

Sashe 9

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 6 min read

da biyu take ta hayagaga so take Asabe ko Kaka wani ya kulata ta rama abinda suka yiwa ya Muhammad d azu da asuba! Ba ta san tak ameme menene ya faru d azun a tsakaninsu ba amma dai ta san a kan Asabe ne Kaka ta kira shi da kwarto. Cike da rashin kunya Dije ta ce uban nawa dai d an ki ne! Kinga kuwa idan kika zage shi kamar kanki ki ka zaga. Tabbas dama na san za ki aikata! Shegiya marar kunya fitsararriya, ai ba laifinki bane ba laifin uwarki ne da ta lalata ku yanzu gashi tun ba a je koina ba kuna shirin addabar al umma! Cewar Kaka. ewa tsaye Dije ta yi ta gyara d aurin zaninta sannan ta ce Wallahi kaff cikin mu babu wanda zai addabi al umma, kaff cikin mu babu mai sata zina ko shaye shaye kinga kuwa mu ba abun gudu bane ba ita wacce kike son kai a kanta kike goyamawa baya ita ce take da wannan tambarin ba dai mu ba dan yanzu haka akwai d an uwanta a hannun hukuma ya je ya yi shaye shaye ya yiwa al umma b arna, kinga kuwa itace mai kashi a gindi.. Mu kam in sha Allah abun alfahari zamu zama wallahi ki rubuta ki ajjiye in sha Allah sai mun yi suna wallahi sai mun baki mamaki Cikin katseta Kaka ta ce eh suna a gidan karuwai ba! Wata mahaukaciyar dariya Asabe wadda ta fito yanzun da niyyar tankawa Dije ta yi kafin ta ce ai dama baki ya san me zai fad a amma bai san me za a mayar masa ba e Baki Dije ta yi kafin ta ce ai ba gaskiya ta fad a ba! Mugun alkaba i take yiwa mutane wanda in sha Allah a kanta zai tsaya ita kad Sai kuma ta juya ga Kaka ta ce wannan rashin sanin ya kamatan naki da aiki da kike yi da k aramar kwakwalwarkin nan ne ya sanya ko kad an ba na respecting d inki wallahi! Allah na tuba in banda rashin man kai wacce kalar Kaka ce za ta yi wannan furucin ga jikarta?? Cikin fushi Kaka ta taho tana cewa Asabe rik e min Yarinyar nan yau sai na koya mata hankali wallahi, rik e min ita in daki banza, ya kamata ta san har yanzu Inada ragowar k arfi na! Shegiya kayan banza Nan kuwa Asabe ta shiga k arin rik o ta ita kuma tana zillewa tana cewa Wallahi mai dukana sai ruwan sama Dai dai sun rutsa ta a lungu Asabe ta tare hanya Kaka kuma ta taho da sassarfa har da had awa da gudu ita kuwa Dije ta yi wani tsalle ta bi ta kan kejin kajin Ya Aminu ta tsallake Asabe yayinda Kaka ta je ta gwaru da garu ji kake k ummm!!! Ta gwara hannu da Kai nan take ta zube a wajen bayan kanta ya bugu sangalalin hannunta kuma ya ce wani asss! Salati Asabe ta kurma ta fashe da kuka tana cewa shikenan za ta k arasa mana ita! Mallan! Mallan!! Mallan!!!! Ita kuwa Dije ko d arr ba ta ji dan dama ita da tsoro sun yi hannun riga, cike da gadara ta ce gobe kya sake zagin mu ai mu Allah muka ce shiyasa duk wanda ya tab o mu yake ganin ba daidai ba. Ba ta san lokacin da Ya Muhammad ya shigo tsakar gidan ba sai wuce ki tafi d in da ya ce mata ta ji. Tana waigowa ta ganshi a tsaye ransa a d an b ace abunda ba ta saba gani ba dan haka ta juya simi simi ta wuce ciki zuciyarta fess!! Har ga Allah ba ta tausayi ko jin k an Kaka saboda yadda sarai kuma k iri k iri tshohuwar take nuna musu k iyayya ko kara babu, ta tabbata in da ace babu zunubi tsaff Kaka sai ta kashesu one by one .haka nan suke rayuwarsu su da ita kamar Annabi da kafiri. A zaune ta tadda Inna tana yankan farce, sai da ta durk usa tukunna ta ce mata Inna Ina kwana, ya jikin? Dukda ta san Inna ba lalle ta yi mata magana ba tunda ba wani namijin ta kula ko ta yi dambe da shi ba amma sai da ta ji d ar-d Ilai kuwa kamar komai bai faru ba Inna ta d ago ta kalle ta ta ce Alhamdulillah. Ki je ki d aura mana ruwan d an wake Ajiyar zuciya Dije ta sauk e kafin ta ce su Ramma sun jik a duk itacen kitchen d in wasu har d igar ruwa suke yi ragowar kuma ba za su ci da wuri a yi girkin a gama da wuri ba, za su bada wahala su b ata lokaci. Ko a siyo y ar tsala kawai ko? e baki Inna ta yi ba tare da ta damu ta ji mai ya faru ita da waye ba ta ce mata ki d auki itacen namu ki kai kan simintin waje ki shanya su, daga nan sai ki biya ki siyi y ar tsalar ki tahowa Muhammadu da shayi. Ta yi maganar tana janyo purse d inta ta zaro d ari shidda ta bata. Karb a ta yi ta ce daga nan ta mik e ta d auki Hijabin ta har za ta fita sai kuma ta juyo ta ce Inna in fitar da har murhun in d aura a kan kejin Ya Aminu ko? Komai na kitchen d in ya jik Kawai Innna ta ce mata daga nan ta ci gaba da yankan farcenta. Tana fitowa ta tarar an kinkimi Kaka an wuce an fita da ita da alama asibiti za su kaita. Ai kuwa ilai tana fita ta ga anata k arin dannanta a motar Manager. Ko sake kallon inda suke bata yi ba kamar ba ita ce musabbabin komai ba haka nan ta wuce ta barsu suna ta hayya hayya. Dije bata dad e da fita ba, Umar ya fito hannunsa rik e da wani k aton salatip fari, kasancewar kusan kaff gidan aka tafi kai Kaka asibiti dan wasu ma a napep suka bisu ya sanya gidan ya zamana shiruuu, tsakar gidan shima ba kowa. Wani murmushi Umar ya yi ya k arasa inda akuyar nan take wadda ta ci kuka ta galabaitu zuwa yanzu kukan nata ma da kyar ya ke fita. Yana zuwa ya nemo kan salatip d in ya d agosa ya warwaro ya dedeta bakinta ya mannna mata, a take ta fara kiciniyar kwacewa amma ya danneta ya shiga nad a mata salatip d in nan kamar an aiko sa .Umar d in Yaro ne gashi dukda kasancewar sa Yaron still shekarunsa sun fi wayonsa yawa sosai, gashi so yake yi ya burge Dije idan ta dawo ta tarar ya toshewa Akuya Baki ta daina kuka ya san za ta ji dad i, dan haka ya had e har da hancin akuyar ya rufe koina ruff da salatip d in nan ba tare da ya lura ba. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 04. Humairah Bulama. Mikiya writers Association.
Chapter 9 · 0% Book details