Sashe 37
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
mu gidan gaskiya sun kashe mini jikana!! Sai kuma a fusace ta sake yin kan Dije Mallan ya yi saurin sake ruk ota amma cha take shegiya y ar iska muguwa! Saboda son ranku gashi yanzu kin mayarda Y a takwas marayu mata biyu zawarawa, wannan wacce iriyar Annoba ce Allah ya sako min ita a cikin zuriata?? Mallan ka rabani da Yarinyar nan ta b ace mini daga gani kafin zuciyata ta buga! Sosai Kaka take kuka wanda tsaff idan ka ganta dole ta baka tausayi. Shi kad ai iyayensa suka haifa amma tsabar rashin imani saboda bin son zuciyarki ke da d an iskan kwartonki d an daba kun yi musu yankan k auna A hankali Iyya ta matso ta ce ki daina aibantata sannan kar ki d aura zargi a mazaunin tabbataccen abu tunda baki da tabbas. Cikin kuka Kaka ta kalleta idanunta jazir ta ce Wallahi tallahi ba ni da tantama shi ne ya kashesa A bud e aka tarar da k ofar gidan nasa da aka shiga kowa bacci yake yi mai masifar nauyi baccin da har yanzu da muke maganar nan da ke basu farka ba! Kinga kenan abu aka shak a musu! Kuma aka tarar da shi da wuk a chake a k ahon zuciya da wata a yashe a kusa da matarsa inaga itama so ya yi ya kasheta watak il ya ji motsi shine ya gudu! Ki gaya min wannan aika-aikar kisan gillar dana wa ya yi miki kama??? Wallahi wallahi bani da tantama shine! Kuma wannan Ta yi maganar ta na mai nuna Dije kafin ta ce da saninta aka yi komai. Ai ko Sagir shima na san k are mata kallon da ya yi ne ya sanya data gaya masa aka kashe sa! In ba haka ba ai kaff samarin gidan nan duk sun fita mai yasa su bai kashesu ba sai shi? Ta yi maganar har yanzun tana kallon Dije da rinannun idanunta da suke baiyyana tsana da tsantsar tashin hankali da b acin rai. Basu ga k arasowar Mahaifiyar Sagir ba sai sauk ar ruwan dukan da ta shiga sauk ewa Dije ne ya sanya aka ganta. i take shegiya tsinanniya y ar iska wallahi yau mai raba ni da ke sai Allah sai na kasheki in sha Allahu Tashi d aya matar ta sake hargitsa tsakar gidan ta sake gigita kowa gashi sai wani irin kuka take yi kamar ranta zai fita, sauk inta d aya ma Kubra bata ji ba dan an yi mata allurar bacci mai nauyi ne. Da kyar su Gwaggo suka janyeta Iyya ta ce Ashe ba ki san k addara ba? Ita har ta Isa ta kashe ko ta saka a kashe ba tare da izinin Allah ba? Daga an fad i magana haka nan kawai tashi d aya har kin hau kin zauna kin fara aiki da ita kina hauka ne??? Cikin kuka Maman Sagir ta ce ai dan ba Kamal bane ba shiyasa kike da bakin magana! Na rok i Ubangiji da ya d aura masa Irin k addarar da kike ambatowa d Duk da Iyya ta ji zafin maganar kuma abun ya yi mata ciwo amma sai kawai ta girgiza kai bata ce mata komai ba ta juya ta wuce d aki. Abunda Kaka take yi bai gigita Dije ba kamar yadda Baba ya titsiyeta akan sai ta gaya masa gaskiyar sun yi maganar Yusufa da Ma a! Dan in ba haka ba to a Ina ya san har hanyar gidansa ba, A gaban mutane. Shiyasa ba ta san lokacin da ta durk ushe a wajen kawai ta fashe masa da kuka ba. Wani irin kuka Dije take yi kamar ranta zai fita dan har wani shishshid ewa take yi gashi ta k i jin rarrashi, wanda hakan ya sanya jikinsa ya d an yi sanyi kafin ya juya kawai ya bar wajen k irjinsa yana dukan uku-uku. A hankali Inna ta k araso ta mik ar da ita suka wuce ciki Kaka tana zaginsu ta uwa ta uba kamar ba tsohuwa ba. Ba a yi minti ashirin ba suka shirya chap suka d auki hanyar Getso har da Asabe da Zainab, ita Inna bama ta sani ba sai a bakin Minu ta ji wanda bai dad e da dawowa daga asibiti ba. Bayan tafiyarsu ta gwada kiran Mahaifiyar Yusufa a waya ta yi mata ta aziyya amma sai ta k agawa k arshema sai ta dinga rejecting dan haka ta hak ura ta bari akan washegari ta yi mata. Tunda Mallan yake bai tab a shiga tashin hankali irin wannan ba dan ya ji mutuwar nephew d in nasa gashi halin da ya ga d an uwa da Mahaifiyarsa sun shiga ya sake kid ima shi matuk Kafin dare labari ya karad e unguwa ya zama topic of the day aah ya kashe wanda Dije zata aura, ba shi kad ai ba ma hatta Sagir saboda ya ga yana sinsinar Dijen ne shiyasa ya kashesa ashe. Zuwa wannan lokacin kam kowa ya fahimci takurar Ma ah ga Dije ashe so ne, dan haka labarin sai ya yi sauk in fassaruwa aka dinga kasa shi a faranti dalla-dalla. Yayinda babban tashin hankalin Inna a yanzu ya zamto waye zai auri y arta? Dan ko ba d an unguwa bane ba tabbas ta san idan ya zo yin bincike akan Dije wannan shine abu na farko da za a fara fad a masa ..duba da yadda a yanzu aka zuzuta abun a unguwar, ake ta shigowa ana jajantawa waenda bakinsu ba ya yin shiru ne suke fitowa su gaya mata halinda ake ciki yayinda waensu gulma da son sake gigitasu ne kawai yake kawo su. Zazzab in da ya rufe Dije ya sanya dole sai da aka kirawo Sakina ta zo ta yi mata allurai itama tana yi tana tata gulmar Washegari da safe Ma ah ya nemi number Mallan ya kira shi a waya ya yi masa ta aziyyar rasuwar Yusufa! Wanda Mallan d in ya rasa ma bakin magana, daga haka ya sanar masa ya tafi Abuja ana ta shirye-shirye za su wuce England za a je a duba Mahaifiyarsa idan ya dawo zai zo ya same shi. Daga nan ya kashe wayar ya bar Mallan da waya kare a kunnensa! Tabbas idan zai mutu a yau to aurar da Dije will be the first thing to do in sha Allah a yau ba sai gobe ba. Sai dai kuma a kaff garin babu wanda ya karb i shelar tayinsa dan ko an yarda idan aka ji ba asin rasuwar Yusufa wanda nan d in ma ya karad e garin sai a ce an fasa Kwanan Mallan uku yana nemawa Dije Miji a garin Getso amma bai samo ba wanda hakan ya sake firgita shi matuk Zuwa wannan lokacin kuma ya fahimci Kaka da Mahaifin Yusufa haushinsa suke ji ata dalilin rasuwar Yusufa saboda Dije wanda tun da aka yi rasuwar dama ya ga sun sauya masa to kuma tunda suka zo suka had u da Anty d in Kaka Iyya lami da Umma(Mahaifiyar Yusufa) abun nasu sai ya k ara tsanani. Yau kam k iri k iri Kaka ta ce masa ya nemi wajen kwana d akin Baban Yusufa inda yake kwana ya cika taff da b akin kunya da suka zo gari ya gari dan haka ya nemi wani wajen ko kuma ya koma Kano kawai. Shima dama abunda yake so d in kenan dan ya lura zama a tsakiyarsu a haka ka iya janyo matsala, dan haka ya tattaro ya sake yi musu gaisuwa da sallama wanda Iyya lami da uwargidan Yusufan suka k i amsawa sai amaryar tasa ce kawai ta amsa masa itama a kumbure. Su Kaka suma da kyar suke iya mayar masa da magana, shi dai ya yi musu duk wani abunda yake ganin ya dace daga haka ya wuto Kano da k udirin aurar da Dije kafin ma ya shiga cikin Gidansa. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 18. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Yana karyo kwanar layin gidan nasa ya ci karo da Mallan Manniru. Ajiyar zuciya dattijon ya sauk e wanda yake kusan tsara d aya da Mallan d in sannan ya mik a masa hannu suka yi musabaha cikin jimami ya ce Ashe haka ce ta faru kuma? Ya hak uri? Jinjina kai Mallan ya yi tukunna ya ce uri Alhamdulillah da godiya Fuskarsa na baiyyana rashin jin dad i ya ce Allah ya ji k ansa ya gafarta masa Mallan ya ce Ameen Dan gaba d aya jikinsa a sanyaye yake ga rashin lafiyar da take cinsa ba tare da kowa ya sani ba. Sai da ya d an numfasa tukunna ya ce haka kurum ya janyowa Yarinya bak in jini! A hankali cikin sanyi Mallan ya d ago daga kallon k asan da yake yi ya kafesa da ido. Wanda hakan da ya yi ya sanya Mallan Manniru gyara tsayuwarsa ya ce Ko dai baka san abunda yake faruwa a layin ba kwana biyu? Bai jira an bashi amsa ba ya ce Ai yanzu bak in jinin Ma ah gaba d aya kan Dije ya komo, tunda suka fahimci yana k aunarta shikenan sai suka d auki karar tsana suka d aura mata kamar ma ta riga da ta zama matarsa ne. A halin yanzu fa sun koreta daga makarantar islamiyya jiya Sumayya take gaya min, wai sun ce saboda gudun kar a hukunta ta ko ta samu sab ani da wani ko wata shi kuma ya zo ya kashe kowa! To d azu ma dai har ta tafi bokon kuma sai na ga nan ma d in ta dawo lokacin Ina shago kuma kamar ma kuka take yi, ta zo ta wuce gida alamun suma d in dai korota suka yi. Wani irin yawu mai tauri da d aci Mallan ya had iye da kyar! A hankali ya sake zuba masa idanunsa waenda suka fara rinewa ya ce Mallan Manniru za ka iya auren Dije? Rasss!! Gabansa ya yanke ya fad i, sai kuma wani sanyi tare da fargaba suka rufe shi. A hankali Mallan ya ce a na kowa ne Mallan Manniru, ka rufa mini asiri ka auri Yarinyar