← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 59

Sashe 57

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko ta mutu sai ruhinta ya dawo d aukar fansar jinin d anta Suna fita da ita Mai Babban D aki ta saka hannu ta d auke kwallar da ta biyo ta cikin idanuwanta, zuciyarta tana wani irin tafarfasa A ko da yaushe idan ta rufe idanuwanta babu abunda take gani sai gawar Gimbiya Sakina kai a rabe da gangar jiki. Bazata gushe ba sai ta gana mata azabar da har ta mutu ba zata tab a mancewa da ita ba kuma ina sha Allahu sai ta rok eta Allah da Annabi akan ta kasheta dan sai ta zabi mutuwa sau dubu sama da rayuwar da ta shirya mata indai ta cika Mai Babban D aki! Garkuwa kuma y ar Sarki jikar Sarki matar Sarki *************** Asibitin Mallan Aminu Kano aka wuce da Mallan wanda duk kwakwar mutum baka isa ka iya ganesa ba tsabar yadda ya k one a koina ya yi bak irin yana k auri jikin yana fitar da wani irin wari. Direct I.C.U aka wuce da shi aka jojjona masa na urorin taimako Likitocin suka yi k arshen bakin k arin su suka fito suka ce musu su yi addua kawai, dan tabbas Allah ne mai yi amma Mallan kam babu alamun zai tashi, a hakan ma da yake ciki gara masa mutuwar kawai saboda azabar da yake kwasa it s unbearable. Idan ka ga Dije dole sai ka tausaya mata kamar wata zararriya gashi ta k i yin magana a kowa sam! Har gara Inna tana amsa addu a ita kam sai kuka da zaman shiru. Musamman ma da Kaka ta zo ta sake zuzuta abun ta d aura laifin komai a kanta gaba d aya sai ta amshi hakan ta aminta da hakan wani sabon feeling na masifaffen tashin hankali k unci bala i damuwa da rashin nutsuwa ya yi mata rubdugu. Ita kanta Inna kusan hakan ne a nata b angaren shiyasa duk suka taru suka fita a haiyyacinsu. A kaff fad in Unguwa Uku Sumayya ce kad ai ta zauna tare da su tana dannarsu. An d an zazzo dubiya (dukda ba samun ganinsa ake yi ba) yayinda waensu jahilan suka ce Allah shi k wai ai alhakin Mallan Manniru Ya Kamal da Yusufa ne ya hau kansa. Amma ita kam Sumayya tana nan tare da su, ta inda Allah ya taimaketa shine Kakarta ta zo Mahaifiyar Mahaifiyarta shiyasa ko da Mahaifiyar tata ta so yi mata bore Kakar ta tsawatar mata ta ce wannan rashin imani har Ina? Ta bar musu Sumayyar su d an ji sanyi, sannan idan ta sake ji ta ce Dije ce silar mutuwar Manniru wallahi sai ta had u da fushinta tunda dai ita ta ce bata san k addara ba. Kamar kuwa zata mutu da bank in ciki haka nan ta hau ta kumbura ta yi suntum!. BAYAN KWANAKI BIYU Da babu gara ba dad i, hakan za a iya cewa game da al amarin Mallan, dan zuwa yanzu kam ya ma daina responding to treatment. Hankulan kowa a tashe yake musamman Dije wadda ita ke ganin halin da yake a ciki dan itace zaune tare da shi dan haka tana samu su barta ta shiga ta lek a shi ta taga duk dare, dukda har yanzun itama bata da wani aikin sama da koke-koke amma ita ce a wajen nasa. Inna da Ya Muhammad suma kullum sai chaaan dare tukunna suke tafiya..dukda kuwa yanayin jikin na Ya Muhammad da yake nan kamar Yaro d an shekara uku hakan bai hanasu zuwa da sassafe su tafi chaan dare. Sumayya k awar arzik i dukda Dijen ba kulata take yi ba dan zuwa yanzu ta zama kamar wata kurma amma Sumayya tana tare da ita kusan ko yaushe dan wanka da zuwa makaranta ne kawai yake rabota da asibitin. Duk da halin da take a ciki sai da al amarin Kaka da Asabe ya d aure mata kai waenda ta ga kamar basu damu da halinda Mallan d in yake a ciki ba, dan ita Dije ma a tunaninta Kaka zata koreta daga jinyar ita ta karb a ko ta ce Asabe ta yi amma sai gashi da ikon Allah gaba d aya sun zame hannuwansu game da komai da ya shafi jinyar tasa da shi a karan kansa, dan tun ranar da aka kawosa tare da su da suka tafi har yau babu kyallinsu. Kawu Isa shima tunda ya kammala biyan kud in komai ya gudu yau kwana har biyu bai sake lek ensu ba, kuma babu waya. Zainab ce kawai a washegarin ranar ta zo tare da su Ramma itama tun daga nan ba ta sake zuwa ba jiya ba ta zo ba yau ma gashi har dare ya yi bata zo ba. Ita kam Dije duk kalar sanyin damunar da ake zubawa tana nan safe rana dare Hatta wanka a cikin asibiti ta ke yi, har sai da waensu a cikin Likitocin suka bata shawarar ta tafi gida kawai ta kwana dan in banda sauraye babu abunda take kwasa gashi zamani na sauro da malaria. Amma furr Yarinyar ta k i yarda ta nad e a cikin hijabinta ta sake kwana a wajen .Zama a nan d in ya fiye mata kwanciyar hankali da salama dan ko sunan unguwa uku bata son ji, besides ko bayaga hakan ma ba zata tab a iya tafiya ta bar Mahaifinta shi kad ai ba, a ko wanne yanayi da hali ta tsinceshi Mahaifinta Mahaifinta ne kuma zata so shi ta yi masa yadda ya chanchanta. Inna ma saboda yanayin jikin Ya Muhammad ne ta san take tafiya amma da tare za su na kwana Zaune Asabe take ta rafka uban tagumi hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi! Babu abunda yake sake d aga mata hankali kamar idan ta tuna yadda Inna take da zaratan maza har y a biyu yayinda ita kuma take da y a mace guda d aya tol a duniya Numfashi Kaka ta jaa ta fesar cikin mad aukakin b acin rai ta ce Asabe ai dama na dad e Ina gaya miki, yanzu ga irinta nan. A yanayin jikin Mallan ba na jin zai kai jibi kin ga kuwa Halima ita ce da gida ta gaje kowa da komai sai abinda Hali ya yi, ba abunda idan na tuna yake sake d aga mini hankali sai tsintacciya da y an tsintacciya wai sune za su gaje dukiyar d a na, dan kasonsu sai ya fi nawa, kinga kuwa ba ta ga ta tafiya ba. Sannan Halima babu Mallan a tsakanina da ita na san bazata yi mana kyau ba, k arshenta sai dai in koma rayuwa a k ashin ikon su ko kuma in hak ura in koma k auye! Kai inaaa ba zai yiu ba!!!! Ta fad i hakan tana rushewa da wani irin kuka. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 30. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Da sauri Asabe ta taso ta zo ta rufe mata baki, ta na yi tana kallon k ofa dan ta ga kamar Ramma tana yi musu lab Idan akwai halittar da Asabe ta tsana a duniyar Allahn nan to bata wuce Ramma ba, kamar k unarta ta san tunanin wa take yi a take ta hau zugi, hannun nata ta kalla ta ga yadda yake sake tab arewa dan ko wajen wanzamin da suka je last ce mata ya yi idan ba ta yi da gaske ba to abun sai ya zamo mata jeji Yanzu haka ko kwakkwaran motsi ba ta iya yi da hannun dan tana yi a take zai hau zugi, wai fa yanzun ma rik e kafad un Kaka da ta yi da hannun ta toshe mata Baki da d ayan hannun ne ya janyo zugin ya taso. Cike da tsana ta kalleta tana wucewa alamun dai lab en ta yi musu da gaske dan sai yanzu ta ga ta nufi d akinta itama da nata hannun nad e da bandeji amma wai duk da haka shanyar kayan wankin Rakiya ta fito yi da hannunta mai lafiya A ranta ta ce shegiya tsinanniya a haka za ki k are! Shi yasa ai k anin uban y an naki ya handame muku dukiya kuma in sha Allah ta tafi kenan har abad A take tunanin ta ya katse ta yi shiruuuuu kamar wata mai lissafi.. Um, umummmmumm in da Kaka take cewa tare da mutsu-mutsu d inta ne ya katse mata lissafi. Cikata ta yi da d an sauri ta d an kalla fuskarta kafin ta d an saki wani lallausan murmushi. Sakin Baki Kaka ta yi sannan ta ce eh lalle Asabe kan ki babu lafiya. Bayan kin yi yunk urin toshe min numfashi yanzu kuma a cikin wannan bala in da muke ciki har kika samu sararin farincikin yi mini murmushi??? Wani murmushin Asabe ta sake saki wanda hakan ya dad a daskarar da Kaka a wajen. Waje ta nema ta zauna a nan kan gadon gefen Kaka ta ce Kaka, bani dukkannin hankalinki ki ji abunda na tsaro mana Dai-dai Ramma ta zo shiga d akinta ta hangi Gwaggo da Mama a zaune a cikin d akin Gwaggwon ta window! Sosai ta ji gabanta ya yanke ya fad i dan wannan keb ewar tasu in ba da kyar ba Gwaggo tsara Mama take yi akan batun tafiya Ingila.. Ai kuwa ilai! Dan tana zuwa ta ji Maman tana ce mata Ai ki kwantar da hankalinki, itama Rammar zan yi mata bayani ai ko Yaran sun kai su ashirin tsaff za a sama musu waje! Yo Allah na tuba ai yin hakan a gareni nima kamar YI WA KAI ne, akwai fa wata Yarinya da na yi mata sanadi ta je chan d in wallahi in gaya miki har zobe ta siya ta aiko min na gold! Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki sannan ku rik e amana kar Yarinya ta je ta kud ance ta dawo ku ce ba ku san wata Mama ba Washe baki Gwaggo ta yi ta ce Ayya, ai ni na iya rik e alk awari da amana ba na tab a manta halaccci. Ita Ramma tana da muguwar zuciya shiyasa ma kika ga tana neman hanawa a kai
Chapter 57 · 0% Book details