Sashe 2
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dare mahutar bawa! In ji masu iya magana, Hausawa. A lokacin da hankali ya kan kwanta, shiru yake maye gurbin hayaniya, nutsuwa take maye gurbin karafniya sannan hutu yake maye gurbin gajiya. Ga kusan kowa hakanne dan in dai aka ce dare ya yi to ko wanne bawa ba shi da wani burin da ya wuce ya sanya hak arinsa a nutsuwa ya huta. Tsakar gida ne mai d auke da d akuna barkatai! Da alama mutanen gidan ba su kai ga yin barci ba dan ko wanne d aki kana iya hango fitila ko kendir d insa a kunne ga kuma maganganu da ake iya jiyowa suna tashi sama sama kamar dai ba dare ba. Kwance take cikin d aya daga cikin d akunan gidan ta inda ta yi kwanciyar rigingine ta na kallon fasashshen silin d in da ya yiwa saman d akin nasu k awanya, a zahirin gaskiya idan ka kalleta silin d in take kallo amma a asalin gaskiya gaba d aya hankalinta ba ya a kan silin d in dan inda ace za a tambayeta meyene shi d in to da ba lalle ta iya bada amsa tashi d aya ba. A karo na uku ta sake juyawa ta kallesu ta tabbatar da sun yi barci dan har gwartin su take ji yana tashi sama sama. A hankali jikinta a sanyaye yana wani irin karkarwa zuciyarta tana dad a yin zafi ta mik e ta zauna idanuwanta a kansu suna masu cicciko da ruwan kwalla sai dai ita kanta ta san hawayen ba iya zubowa za su yi ba. ewa ta yi tsaye har yanzun idanuwanta a kansu, ba ta da kowa sai su kuma tana matuk ar jinsu a cikin ranta..kamar yadda ba ta da kowa sai su haka nan a nasu b angaren suma ba su da kowa sai ita shiyasa ta ke da tabbacin za su yi k ewarta dukda kuwa a cikin bala in da ta zamo silar jefasu amma ta san tabbas za su sake shiga cikin mawuyacin hali idan ta barsu sai dai kuma ta san hakan da yin hakan a gareta da su gaba d aya shine dai dai..Gara ta tafi su ji zafin tafiyarta na kwanaki kad an daga nan ta san za su ci gaba da rayuwa mai dad i sab anin idan ta ci gaba da zama da su wanda ta ke da tabbacin komai sake tab are musu zai yi! Tabbas ita a karan kanta ta yarda kuma ta amince da sunan da kowa yake kiranta da shi a yanzu Annoba , ba ta jin akwai alfanun ci gaba da rayuwa a tsakiyar su kai ba ma iyaka su kad ai ba al umma kanta gaba d aya bataga amfanin zama a cikinta tana janyo musu bala i dami-dami ba! Dan haka ta juya a hankali cikin tafiyar da a yanzun ta zame mata jiki kamar ba ita ce ma abociyar kazar kazar da karafniyar nan ba ta fara tafiya kamar marar lakka a jiki yayinda jikin nata yake wani irin karkarwa . A haka ta nufi k ofar fita daga d akin zuciyarta tana mai dad a tabbatar mata Tabbas abinda kika shirya yi shine dai-dai!!! Babu kowa a tsakar gidan dan yanzun misalin k arfe sha biyu na dare ake nema amma fa baya ga mutanen da ta baro a d aki suna bacci ta sanadiyyar alluran da aka yi musu babu wanda yake da ma shirin yin barci a kaff cikin gidan wanda dalilin rashin kwanciyar tasu da wuri yana da nasaba da alhinin da suke a ciki yayinda waenda basusan Annabi ya faku ba zaman munafurci ne suka zauna yi. akunan ta bi da kallo, duk da yawansu amma ta gaza dukan k irji ta nuna guda d aya tak! Wanda za ta ce ba ta saka y an d akin a cikin alhini jafa i tare da damuwa ba. A hankali ta juya ta kalli d akinsu a karo na farko tunda satin nan ya kama ta ji hawaye ya silalo ta cikin idanuwanta dan a lokacin da masifa ta kai masifa kuka yaji ya yi mata ya k aura ya bar cikin kwayar idanuwanta. A take ta fara jin kamar ba zata iya aikata abinda ta shirya ba, gudun fasawartata da ta ji wani sashe na zuciyarta yana shirin bijiro mata da shi ne ya sanya ta wuce cikin sassarfa ta nufi tafkekiyar rijiyar da ke a chan kusurwar tsakar gidan. Ta na isa ta saka hannu ta jaa katokon da yake rufe da rijiyar a hankali ta bud eta gudun kar a jita, so take sai da safe idan sun fahimta su tsinci gawarta a ciki idan kuma ba su fahimta ba ta rub e a ciki su k araci nemanta su hak ura. Iyaka kallon rijiyar kad ai ya Isa ya sanya ka ji tsoro tsabar girmanta sai dai gareta sam ba hakan bane ba dan ko d igon tsoro ba ta ji ba saboda rayuwar da take ciki a yanzu ta fi k unci! Azabtarwa!! Kad aici.. fiye da rayuwar da ta san zata yi na wucin gadi a cikin ruwan rijiyar kafin Allah ya karb i ranta, sannan ko ba komai babu wanda za ta ji kunyar had a ido da shi a cikin rijiyar sab anin yanzu da take ji kamar ta binne kanta A hankali ta taka dakalin rijiyar ta hau ba ta bari ta tsaya b ata lokaci ba ta yi tsalle ta afka ciki tsundum!. Hayaniya mai tsananin firgitarwa ce take tashi a tsakar gidan dan harda koke koke yayinda hankulan makusantanta ya kai k ololuwa wajen tashi! Zuwa yanzu hayaniyar ta su ta fara gushe mata anin daa da take iya jiyosu .a hankali ta lumshe idanuwanta tana sake nutso a cikin ruwan rijiyar da ta yi lamooo a cikinsa dukda kuwa azabar rashin numfashi ta kai k ololuwa wajen azabtar da ita amma tabbas hakan ya fiye mata akan azaba da k uncin da zuciyarta suke ciki a doron k asa. UNGUWA UKU (Babban layi Juma atu babbar rana..Kamar ko wacce rana ta Juma ah haka itama wannan Jum ar ta kasance ranar sada zumunci da yawace yawacen gidajen k awaye ga y an Yara Yaran layin saboda yau d in babu makaranta sai hutu wasa da tsalle tsalle a garesu. Misalin k arfe biyu da mintuna arba in kenan..masu zaman majalisu na yi masu gaishe gaishe na yi masu yawo da tsalle tsalle suma suna na su. A bakin kiosk d in wani mai p.o.s kusan duk samarin layin suka taru ana hira ana raha dan basu dad e da dawowa daga masallacin na Juma a ba wanda hakan shi ya taimakawa layin wajen sake yin albarka ya cika taff tubarkallah. Da gudu wata Yarinya ta k araso wajen, tana zuwa ta sauk e idanunta a kan wani kyakkyawan saurayi dogo bak i, tana haki cikin mayar da numfashi ta ce Ya Aminu! Ya Aminu!!! Ga su Ma a chan sun tarewa Dije hanya a bakin filin kashu. iff!! Haka maganar kowa ta tsaya chak! Kamar an yi ruwa ya cinye su yayinda tsoro mai had e da firgici ya maye gurbin raha da annashuwar dake kwance a kan fuskokinsu yanzun nan. Da kyar wani daga cikin samarin ya ce Minu, kuma tunda har kun san ya takura mata ku daina aikenta inda kuka san shima yana yawan zuwa mana. Da kyar k irjin Ya Aminu ya na dukan uku uku ya iya cewa na hana, ban san me ya kaita chan ba. Sai kuma ya yi saurin yunk urawa ya ce bari in je an layin koma ace anguwar gaba d aya suna da masifar had in kai, duk abinda ya shafeka to ya shafi kowa haka nan suke rayuwarsu saidai a yanzun da kyar aka iya samun mutum biyu suka bi Minu ragowar kuma suka fake da tafiya police station dan su je su taho da y an sandan da kowa ya san basu isa su iya yiwa Ma in uwar komai ba. Duk da cewa ita d in budurwa ce mai tashe dan a k alla shekarunta sun haura sha shidda da kad an amma still yanayin k irar jikinta ta fi shekarun nata dan kallo d aya za ka yi mata ko daga kusa ko daga nesa ka fahimci ita d in tana cikin jerin matan da Allah ya wadata su da k ira mai kyau ..Daga ido idan ka kalli yanayin jikinta za ka yi mata kallon babbar budurwa duba da yadda komai na girma ya gama baiyyana da tabbata a tattare da ita, sai dai kuma yanayin d abiarta zai sanya ka fahimci har yanzun akwai ragowar k uruciya a tattare da ita. Shekarun nata sun haura sha shidda amma ba su kai sha bakwai ba wanda idan ka matso ka yi mata kallon k urilla to yanayin fuskarta ma kawai zai iya k iyasta maka adadin shekarun nata. Tsaye take ta kama k ugu tana masifa da tujara babu alamun tsoro ko sassauchi a tattare da ita, wasu zaratan samari su uku ne a tsaye a gabanta wanda ko da wasa bai kamata ace ta tsaya yi musu kallon banza ba ma ballantana masifar da take ta zazzage musu kamar ta samu y an cikinta! Ba wai iyaka shekarunsu ne ya kamata a ce ya sanya a ji tsoronsu ba! Yanayi da suffar su kad ai ta Isa ta firgita Yarinya mai shekaru irin nata, ba ma ita ba ko Babba bai isa ya ce zai kalli su Ma a ya yi musu da su ba ma ballantana fad aya bayan d aya ake watsewa a wajen, hatta masu kiosk rufewa suka fara yi masu trader suma tuni suka fara tuttura abun sana ar su suna barin wajen, dama tun tunkarowar Ma a da shi da Yaransa guda biyu wajen aka fara tarwatsewa to kuma yanzu behavior d in wannan y a marar ta ido ya sanya kowa yi ta kansa tun kafin Ma a ya yi kan mai uwa da wabi. Dai dai lokacin da su Minu suke isowa wajen suna haki dan gudu suka tsula dai dai ita kuma ta durk usa ta tittilo k asa a duka