Sashe 11
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
lungun malan mai kanti, sai da na kusan kaiwa k arshen lungun tukunna na lura da su a zaune Yaransa suna ta shaye shaye. Wari gaba d aya lungun shine na toshe hanci wallahi ko kallonsu ban yi ba ya taso ya zo da kanshi ya saka igiya ya d aure mini hannu da sauri ta baya sannan ya saka d ankwalin Oscar ya d aure min k afafuwana wai dole in tsaya in shak i warin da nake toshe hanci shine garin guduwa na fad i na kasa tafiya wai in yi irin ta cartapillar kawai in k arasa gida a haka. suka dinga yi min dariya, na dad e ina ta k arin tafiya na kasa har rana ta zo kaina shi yana tsaye a kaina su kuma suna gefe suna ta hira, shine yana gani na fara kuka kuma sai ya yi saurin kunce ni ya ce in tafi, wai ashe ni marar kunyar k arya ce. Ajiyar zuciya Inna ta sauk e kafin ta ce kin tabbata shikenan? Daga haka shikenan? Zuwa yanzu Dije ta gane me innar ta ke nufi dan haka ta ce ko da ya zo d aurenima ni ban ji ya tab a ni ba. Sosai Inna ta sake sauk e ajiyar zuciya sai kuma ta koma ta zauna a kan gadonta ta dafe kai. Matsakaicin gida ne (a layin su Dije) mai d auke da d akuna uku da babban band aki da kitchen sai d aki mai bayi a soro shima Babba. an hargitse ya shigo cikin gidan yana rarraba ido, idanunsa suna sauk a a kanta ya k arasa ya zare silifas d insa ya zauna a kan tabarmar nan kusa da ita inda take zaune tana tankad Murmushi ya yi kafin ya ce uwargida kuma amarya sarautar mata, barka da gida Murmushin itama ta mayar masa kafin ta yi masa barka da shigowa sannan ta fara k arin mik ewa tana cewa bari in kawo maka abinci Da sauri ya rik o hannun nata ya ce a ba abinci ba tukunna zauna mu yi wata y ar magana .a cikin ajiyar da aka baki jiya nake so ki d an bani rance A take annurin fuskarta ya d auke, ba ta zauna d in ba ta ce dan Allah ka rufawa kanka asiri, ni da ace ina da nawa wallahi da na baka ka sani. Kud in nan da ka gani ya bani jiya yau fa yace min zai karb Cikin katseta ya daka mata wata uwar tsawa yana cewa ke dalla malama rufewa mutane Baki! Ba wani dogon zance na nemi ji a wajenki ba kud i kawai za ki ranta min. Kin san ni yau nawa na kashewa b arnar da ya yi d azu da asubah a masallaci? Ki d auko mutane zan biya bashi na gaya miki zan mayar kafin ya karb Ya yi maganar yana mai matse tafin hannunta wanda yake a cikin nasa.. Azaba sosai take karb a dan kamar zai karya mata hannun haka yake yi mata cike da mugunta, cikin dauriya ta ce Allah wannan karon idan ya zo kai tsaye zan ce masa kai ne ka karb a ba zan sake rufa maka asiri ba.. Cikin tsananin b acin rai ya fincikota kuma ba kansa ba gefen taburmar ya zubar da ita sannan ya ce idan kin fasa!! Ki tashi ki d auko min kud i na ce Ji ta yi kamar mutum a kansu dan haka ta d ago ta kalli direction d in aikuwa a take idanunta suka sark e a cikin nasa, da mugun k arfi gabanta ya yanke ya fad i karkarwar da jikinta ke yi ya k aru gashi babu damar wayancewa dan da gani ya dad e tsaye a wajen Tana shirin yiwa Mallan Idi magana ko ta yi masa inkiya ta ji an fincikesa kamar wanda aka jaaa da mashin hakanan kafin k iftawar ido ta hangesu ya buga shi da bangon gabas ya shak esa yana huci!!! Cikin mad aukakin tashin hankali ta k arasa garesu da gudu ta fara k arin b are hannunsa daga wuyansa amma ko gezau, tsabar bala i jikinsa har wani karkarwa yake yi yana huci gashi ya kafesa da idanunsa waenda suka rine da b acin rai. Zuwa yanzu idanuwan mallan idi har sun fara k afewa!! So yake yi ya basa hak uri amma ya k i ma ya bashi damar yin hakan, ganin yana shirin aika sa lahira a take ya sanya ta daga hannuwanta duk biyu kawai ta rufesa da duka sai kuma ta fashe da kuka ganin ba ma dukan yake ji ba ta durk ushe a wajen tana cewa ka rufawa kanka asiri so kake tsinuwar Allah ta tabbata a kanka ne??? Sautin kukan ta ne ya d an fara dawo da shi cikin haiyyacinsa, a hankali ya juya ya kalli yadda ta durkush e a wajen tana kuka, cikin wani irin rauni ya ce ki daina kuka! Ganin ta yi nasarar karkarto da hankalinsa ne ya sanya kawai ta mik e ta shige d aki still tana kukan, ba ta da tantama yanzu zai biyo ta Ko gama zama ba ta yi ba ya d aga labulen d akin ya shigo fuskarsa a hargitse, cikin rashin jin dad i ya k arasa inda take ya zauna ya kamo hannunta. Fisgewa ta yi cikin kuka ta ce tashi ka fita Cikin rauni dan sam ba ya k aunar kukan nata ya ce Mamaa A fusace ta juyo tana kallonsa ta ce me za ka ce min? Ma aruf ubanka ne fa shi!! Idan ba ka tsoron mutane zuciyarka ta k ashe ai ya kamata a ce kana jin tsoron mahallicin ka! Ka san me ake nufi da iyaye kuwa? So kake yi Allah ya yi fushi da kai ka sake tab arewa??? Kalli rayuwarka Ma aruf ko kishin kanka ba ka yi? Ba aiki ba sana a ba aure ba girma? Ko wannan fadanci da ake yi maka ganinsa ka ke yi a mazaunin girma? Ka yi karatunka ka je ka nemi aiki ko ka ci gaba da karatun ko ka kama sana a wannan rayuwar da ka zab awa kanka ba fa mai b illewa bace ba, mai ya sa su y an siyasar ba sa saka y ansu yin ta addancin sai kai? Yadda ya runtse ido ya fara haki ne ya sanya ta fahimci ransa ya kai k ololuwar b aci, dan haka kawai sai ta kawar da kai ta k i ci gaba da cewa komai A hankali ya zame hannunsa da ke a cikin nata ya ce dan Allah ki daina kuka Daga haka ya mik e ya juya ya fice fuuu kamar zai tashi sama. Inda ya bi ya fita ta juya ta bi da kallo zuciyarta sak e sak e kala kala ba ta san wasu ba amma ita dai tunda ta ke ba ta tab a ganin mutum mai saurin fushi rik o da taurin zuciya da masifar taurin kai had e da zafin kai kamar d anta Ma aruf ba! A lokacin da ta haifesa bayan ta farfad o daga suman wucin gadin da ta yi ungozoma hud u ta tarar a kansa suna ta duba shi dan ya k i yin kuka sam! Ga dai idanunsa a bud e yana kallon jama a amma bai ce uffan ba, k arshe sai hak ura suka yi suka ce ta kaisa ya ga Likita Sai da ya kai shekaru uku tukunna ta fahimci halayensa tsaff waenda suke matuk ar d aure mata kai wasu lokutan.. Tun haihuwarsa Mahaifinsa Mallan idi ya ke jinyar karaya, dan haka ita take fita ta je ta yi aikatau ta nemo musu abinci, barinsa da Ma a da take yi ne ya bashi damar cin zalin Yaron kamar ba shi ya haifesa ba dan har da molestation yake had awa wanda sai da Ma in ya kai shekaru goma sha biyu tukunna ya gane cutarwa ne ake yi masa kuma abun bai dace ba..shi d in ya kasance Yaro mai tsananin so da yiwa Mahaifiyarsa biyayya to a duk lokacin da ta dawo gida ya tambayeta me ye hukuncin wanda ba ya yiwa iyayensa biyayya sai ta ce masa an wuta ne to top it all ya ga ita kanta da ya ke matuk ar so da girmamawa tana jin tsoron uban, ga uwar wahalar da yake gana masa idan ba ta nan waennan su suka taimaka wajen sake saka tsoronsa a cikin zuciyarsa. Tsoro azabtarwa da wahalhalun da Mallan idi yake basa ne suka bada gudummawa wajen jefasa a hali na damuwa sannan zuciyarsa ta tab in Hali da miskilancinsa da ba sa barinsa ma ya shiga cikin Yara ya sanya bai fahimci komai ba sai da Mahaifiyar sa ta harhad a kud i da kyar ta saka shi a makaranta lokacin shekarunsa goma sha biyu Musu suke yi shi da wani Yaro Antynsu ta ji shi Ma a ya ce ko menene idan iyaye suka ce a yi dole a yi shi kuma Yaron ya ce masa ban da sab on Allah. Dan haka ta kirasu ta faiyyace masa komai ta yi masa bayani dalla dalla. Ko da ya je islamiyya nan ma same thing Malamin su ya gaya masa dan haka kawai ya samu Mama da maganar kai tsaye. Da farko ba ta yarda ba sai da ta d ana tarko ta kama Mallan Idi da kanta tukunna. Ita sam maganar wanki da ragowar wahalhalun ba su dame ta ba kamar molestation Yanke jiki ta yi ta fad i sai a asibiti ta tsinci kanta. Ko da ta farfad o a take ta ce ba aure! Shi kuma ya ce bata isa ba Ganin y an unguwa suna shirin maida su su zauna ne ya sanya ta tatttara kayanta suka gudu ita da Ma Sai bayan shekaru goma sha d aya tukunna da kyar aka gano inda suke, ya tattaro mutane har da k aryar ciwo ya na kuka aka lallab a ta koma ba dan ranta yana so ba sai dan ba yadda ta iya dan har zuwa wannan lokacin ya ce shi fa bai saketa ba. Ko da suka dawo ita kanta