Sashe 43
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba tare da sun san me za su bayar ba idan sun je d in dan sun yi k aff!! Hatta Ya Muhammad ma shirye-shiryen dawo da shi gida ake yi a hakan ba tare da ya warke ba saboda basu da kud in gado bare na magani. Duk fushin da Kaka take yi da shi tana jin labari ta baro garin Getso a rikice dan Mallan daban yake a wajenta Halima ce take janyowa suke yin fad a ita da shi amma ba dan haka ba da an ga yadda ake ji da Yaro. Zuwan nata ne ya sanya suka samu d an abunda aka bayar a asibitin aka ci gaba da treatment d insa wanda daa Likitocin suke shirin ajjiyewa dan ko syringe babu a asibitin sai ka siyo tukunna za a yi maka amfani da shi su kuwa basu da ko sisi. Tijara ta so yiwa su Inna a bainar nasi dan haka Inna ta tattaro Dije suka baro wajen, tunda har an samu wanda zai d auki d awainiyar tasa to Alhamdulillah, daga haka suka fito ba su da ko kud in mota suka shiga dab awa da k afafuwansu ga dare. Kamar daga sama suna cikin tafiya ta ji an ce Khadija Tana juyawa ta ga Ya Kamal ya biyosu yana d an haki alamun da kyar ya cimmusu. A take kunya duk sai ta lullub e Inna dan tabbas ta san bai kamata Dije ta fito ba da saninshi ba. Sai da ya rissina tukunna ya gaida Inna itama ta amsa cikin jin kunyar da bata tab a kawowa zata yi ta a Kamal d in ba. Cikin rashin jin dad i ta ce ka yi hak uri ta fito ba da sanin ka ba ko? Jikin Mallan ne ya motsa shine duk muka fito imauce ni na ma matan w Da sauri ya ce haba dai Inna, ba komai wallahi Allah ya bashi lafiya, nima Iyya ce ta kira take sanar min shine na biyo sahu shigata ba wuya kuma Minu ya ce min yanzu kuka fita, shine na ce bara in duba. Bismillah mu je in k arasa da ku ga mashine d in chan. Ya yi maganar yana mai waigawa ya nuna musu inda ya yi parking. Murmushi Inna ta yi ta ce ba komai ku je zan k araso ni. Shima sai a lokacin lissafinsa ya bashi baza ta iya ta bisu a machine d in ba dan haka ya wuce ya tarar mata napep ta shiga ya biya kud in suka wuce. Dije ji tayi kamar ta bita su tafi a kan cinyarta amma Napep d in a cike take tap da mata biyu da y ansu Innar ma da kyar ta samu waje. Sai da ya ga wucewarsu tukunna ya juyo ga Dije wadda ta diririce a take ta hau kame-kame. Murmushi kawai ya yi a ransa yana mamakin yadda duk suka sauya daga ita har Innar kamar ba su ba. Ko da yake ya san in komai ya wuce za su dawo kamar yadda suke a daa in sha Allah idan komai ya yi settling hankali ya kwanta dan mai hali ba ya fasawa. A ransa ya ce zan sha daru! Fuskarsa tana baiyyana murmushin da yake nuni da nishad in da zuciyarsa take a ciki. Mu je ko? Muryarsa ta katse mata hanzari. A hankali ta sake sunkuyar da kanta k asa ta juya ta wuce inda ya nuna musu machine d in nashi. Sai da ya hau tukunna ya karkata mata itama ta hau sannan ya kunna suka wuce, yana jin yadda ta matsa sosai chan k arshe duk dan kar jikinta ya gogi nashi. Kad an ya rage bai fashe da dariya ba lokacin da akazo wajen speed bumps dan sosai ta saka hannayenta a tsakankanin k irjinta da bayansa yadda k irjinta ba zai bugi bayansa ba. Har suka k arasa gidan babu wanda ya cewa d an uwansa k ala! Yana sauk eta ta fara k arin shigewa cikin gida har ta hau kan d an dakalin k ofar gidan nasu ya yi sauri ya ce Khadija yana mai daidaita parking d in mashine d in nasa. A hankali ta ja ta tsaya kafin ta juyo, a take ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad uwa sakamokon idanu biyu da suka yi da Ma ah tsaye a bayansa. Idanuwanta ne suka wani Irin ciccikowa k irjinta ya hau dukan uku-uku jikinta ya fara karkarwa tana mai jin wata kalar tsoro da tsanarsa suna lullub eta. Ya kafeta da idanuwa sam ko kyaftawa ba yayi kuma bai yi motsi ba sannan bai ce komai ba yana nan a yadda yake wanda hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai Aljani ne dan ita a iya saninta ma Ma ah d in baya Unguwar baya ma garin. Karkarwar jikinta ne ya k aru gashi tsigar jikinta ta fara tashi a ta sakamokon kallon k urillar da yake yi mata da taimakon hasken kwan fitilar nepan da ke a k ofar gida, ga wani irin tsoro da fargaba dan haka ta yi sauri ta juyaa zata shige cikin gida ita sam ta ma manta da Ya Kamal a wajen wanda ya k araso izuwa gareta ya tsaya yana kallonta yana mamakin yadda jikinta ke karkarwa haka tashi d aya. Caraff! Ya yi ya ruk o hannunta da sauri ya juyo da ita wanda hakan ya sanya Ma ah d in ya yunk ura kamar zai yi kansu sai kuma ya d an dakata. A hankali yana kallonta ya ce mai ya faru? Ba ki da lafiya ne kema? Magana Ya Kamal yake yi mata amma kwata-kwata hankalinta baya a garesa dan haka bama ta jinsa gaba d aya idanunta da hankalinta suna a kan Ma ah wanda take hango tsantsar b acin rai da tashin hankali a cikin kwayar idanuwansa Ya Kamal yana da kirki fiye da zato ba zata ce tana son shi ba a yanzu dai kam amma ta san zata so shi a gaba a matsayin Mijin aurenta! Tabbas idan wani abu ya same shi ata sanadiyyarta to bata jin za ta iya d auka! A hankali ta ce Astaghfirullah sai kuma a take hawaye shaa suka kwace mata. Rikicewa ya yi ya shiga tambayar ta mai ya faru? wanda hakan ya sanya hawayen suka k ara dad uwa kamar an kunna famfo. Ganin yadda jikinta ke karkarwa gashi sai kuka take yi ne ya sanya kawai ya janyota ya saka ta a jikinsa yana bubbuga bayanta alamun rarrashi. Da wani Irin mugun speed Ma ah ya juya ya bar wajen kamar walk Da kyar Dije ta iya cewa Ya Kamal mai ya sa ka yarda ka aureni? Kar wani abun kaima ya sam Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da maganar saboda yadda kuka ya sake taho mata da k arfin gaske mai yawa. Bai san lokacin da murmushi ya sub uce masa ba, kenan ta damu da shi gashi har tana kuka bata so wani abun ya same shi kenan. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya ce Khadija babu abunda ya Isa ya sami bawa sai da izinin Ubangiji, Ma ah bai Isa ya yi mini komai ba sai abunda Allah ya riga ya rubuta kuma ina so ki saka a ranki ma ba shine yake kashe waenda aka yi baikon ki dasu ba, kar ki bari nauyin guilt d in kowa ya hanaki yin walwala, kin ji ko? Ya yi maganar a hankali cikin sake sakata a cikin jikinsa wanda hakan da ya yin ne ya sanya ta tuna a ina take dan haka ta yi saurin jaa daga jikinsa ta matsa gefe sosai. Murmushi ya yi ya sake kamo hannunta a karo na biyu ya ce ki kwantar da hankalinki, kin ji ko? Sannan kar ki tab a bari guilt ya yi tasiri a kanki zai tarwatsa miki rayuwa ne, ki yi min wannan alk awarin. A hankali ta jinjina kanta tana mai dudddubawa ganin bata ga Ma ah ba ya sanya ta d an nutsu bayan ta saka a ranta maybe ko kwakwalwarta ce take yi mata gizon sa. Juyawa ya yi ya kalli inda take kallo ganin bai ga kowa ba ya sanya ya kawar da tunanin ya ce gobe da sassafe zan tafi Minna, Iyya ta ce in je in nema mana inda za mu zauna sannan in sanarwa k aninta halinda ake ciki (in person) tukunna, dan daa tare zamu tafi to amma ta san za su ce suna so su zo su d aukeki hakan babbar Al ada ce a garemu dan haka baza su so ta sub uce musu ba In sha Allahu ba zan wuce 1 week ba zan dawo tare da su sai mu wuce ko? Zan had o miki har da lefen ki in taho miki da su in sha Allah. Ya k arashe maganar yana murmushi yana kallonta. A hankali ta sunkuyar da kanta k asa sosai sannan ta ce Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo. Jinjina kai ya yi ya ce za mu dinga waya ta wayar Inna. Ba zan yi miki alk awarin waya yanzu ba saboda akwai abubuwa da yawa a kanmu amma idan muka yi settling kika ci gaba da makarantar a chan zan siya miki in sha Allah. Jinjina kai ta yi ta ce na gode Har zata wuce sai kuma ta ce Allah ya tsare hanya. A hankali ya ce sai na dawo Sai kuma ya kamo hannunta ya yi kissing wanda hakan ya sanya ta d an zabura har ta so bashi dariya sannan ya zaro dubu goma dama da ya yi niyyar bata kafin ya wuce ya ce gashi ki rik e a hannunki, ko? Da kyar kuwa ta karb a tukunna ta wuce ciki jikinta sanyi k alau! Bata yi tunanin tadda kowa a tsakar gidan ba dan 12 ma ta kusa, amma tana shiga ta tarar da Rakiya da Kubra da Maman Fati suna ta k us-k us. Tana jin Rakiya tana cewa Wallahi har da kiss, hmm Yarinyar nan ai ta cucesu ko da ba a kashesa ba ya kwashi ragowa, ki ga fa yadda take nuna tana