← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 59

Sashe 46

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka tafi asibiti a rabaka da abun hannunka. Clinic d in baya inda muke zuwa nan zaka je. Tam, Oga! Scorpion ya ce da shi yana mai sara masa wata kwalla tana zubo masa dan ya san da tare za su yi masa hakan shi da Oscar, cike da alhini bak in ciki da b acin rai ya juya ya fice daga cikin d akin dai-dai Ma a ya gano abunda yake nema. Wata rikitacciyar kwayar gari ce ya d auko. Ya kunna coal a kasko ya fara k arin zubawa a ciki, da sauri Tiger ya k arasa garesa ya rik e masa hannu ya ce wai da wanne yaren kake so in yi maka bayani tukunna ka fahimce ni ne? Ka gaya mini ribar yin hakan idan ka yi, ka nutsu kar ka bari ka birkice na tabbata idan aka bincika watak ilan ma Mama tana chan England d in kamar yadda aka tsara, raina maka wayo kawai suke yi, ka tsaya ka nutsu mu san abun yi ba wai ka rikice mu rasa tudun dafawa ba. uraa masa idanuwa ya yi kafin chaan ya ce Maama ba ta chan basu kaita ba na gaya maka, Tiger treatment zamu je ba batun wasan y ar tsana ba, ka gaya min ta yadda za su iya kammala duk wasu shirye-shirye su turata a cikin y an kwanakin da suka gabata ana shirin Tabbas na tafka babban kuskure da na bar ragamar d awainiyar kula da ita a hannunsu, dana sani da nayi mata iyakar iyawata na barwa Allah komai. On top of everything kuma jiya na sake barinta na tafi wani banzan operation! Ya k arashe maganar yana mai kama kansa kamar mai shirin fasawa, wani abu mai zafi yana dakar k irjinsa, ji yake yi kamar ya kurma uban ihu! Bai ma san ta Ina ne zai fara ba gaba d aya ya rikice, ashe shi kallon biri yake yi mu su su kuma suna yi masa kallon ayaba, yana tunanin ya iya takunsa ashe suma akwai tasu manak isar a k ulle ba shi kad ai ne yake ninke su ta bai-bai ba?? Ashe suma fuska biyu suka zo masa da ita A hankali ya sake yunk urin kunna hayak in Tiger ya rik e masa hannu, cikin daka masa tsawa Ma in ya ce wai baza ka bar ni in yi yadda nake so ba ne? Ka san Allah idan baka rabu da ni na yi baccin nan kwakwalwata ta nutsu ba har kai kanka sai ka bakwanci lahira a yanzu ba sai anjima ba! Ka bar ni in yi bacci in tashi tukunna na san abun yi tun ban aikata aikin dana sani ba! Sosai tiger ya firgita ya tsorata da yanayinsa dan idanuwansa kad ai idan ka kalla dole su firgita ka! Gashi ya birkice ya fito a asalinsa dan haka ya d an jaa da baya ya sunkuyar da kansa ya ce ka yi hak uri. Bari in tafi zuwa anjima idan ka tashi sai ka nemeni. Get out!. Kawai ya ce masa har yanzu yana huci kamar wani zaki. A hankali ya juya ya fita zuciyarsa sam babu dad i, shi kansa ya ji mutuwar Oscar wanda ya mutu a yau wajen k arin ganin sun (Shi da Scorpion) bawa Ma ah d in kariya wanda ya san harda hakan ne ya sake dulmiyasa cikin kogon k unci da tashin hankali dan ko bai fad a ba ya san cewa su Scorpion suna da special place a cikin zuciyar Ma aruf d in, ga kuma Mahaifiyarsa da mutanen chan suka rik e suke k arin fara yin amfani da ita wajen ganin sun tilasta masa ya ci gaba da yi musu aiki, sannan ga Khadija wadda ya san yana matuk ar so amma k iri-k iri an k i a bashi aurenta! Tabbas dole ya shiga damuwa da k unci mai tsananin hatsarin gaske Tiger yana fita Ma a ya rufe d akin ya yi masa turnuk u ya d auki wata kwaya itama ya kora da ita dan sosai yake buk atar yin bacci mai nauyin gaske tun kafin ya yi b arna ko kuma zuciyarsa ta buga ya mutu ya bar Mama a hannun waenchan munafukan, wallahi wallahi in dai ya haifu to sai ya nuna musu kuskuren su Haka nan gaba d aya daga jiya zuwa yau ana neman a haukatashi, duk da ya shaida d ayar matsalar tasa ta kau amma har yanzu ya gagara daina ganin the worst scene da ya tab a witnessing a rayuwar sa (jiya) a idonsa, da ya rufe ido kawai su yake gani. (MEANWHILE) Sama-sama take jin hayaniya kafin ta kai ga fara jinta tarr sosai. Ji ta yi inama ace bata farka ba dan muryar Kaka ta fara ji cikin hayagaga tana cewa sai fa sun fita daga cikin gidan nan sannan daga cikin unguwar nan ma gaba d aya dan wallahi tallahi mun gama zama da annoba! Da alama a cikin d akin take, kuma ga dukkan alamu b arna take yi musu dan ta ji ana fatali da kaya sai dai ita ba wannan ce damuwarta a yanzu ba, ta yadda zata fara had a ido da mutane shine matsalarta sannan mamakinta ya fi tafiya ga Ina Innar tasu take dan bata ji motsinta kwata-kwata a cikin d akin ba illa muryoyin su Ramma ita da Gwaggo waenda suke ta faman k arin kwantarwa da Kaka hankali yayinda Maman Sagir Maman Fati da Asabe wadda bata ma san yaushe ta dawo ba suke sake zuzuta abun suna zuga Kaka. A hankali ta fara k arin bud e idanuwanta dishi-dishi ta fara gani kafin ta fara ganin su tarr sosai, ilai kuwa kamar yadda ta yi zato hatta y ar guntuwar tvn su Kaka ta fanchakalar da ita a waje hatta labulen d akin ta cisge ta jefa waje tare da duk wani kayan d akin, wanda d akin ya rage saura katifar da take ta faman kokawar ganin ta fitar da ita a yanzun ce kawai. Still har yanzu bata ga Inna ba, kuma kamar babu kowa a tare da ita. A hankali ta yunk ura zata mik e ta ji hannunta a rik e cikin na mutum gamm!. Tana d agowa ta ga Ya Aminu a zaune a saman kanta (gefe) idanunsa a kan Kaka kawai ba ya motsi amma yadda idanuwan nasa suka yi jaaa fuskarsa take karkarwa za ka san ransa ya kai k ololuwa wajen b aci!. Kallonsu kawai yake yi yana jira ya ga iyaka gudun ruwansu daga ita har Asaben. Cikin hayagaga ta ce Asabe zo ki kama mini katifar nan mana! Wallahi na gama zama gida d aya da annoba. Yana kallon Asabe ta shigo k i ta kama mata suka fitar, suka yasar a waje. Sai gata ta dawo cikin d akin ta fara k arin jaan k afar Dije fad i take yi tashi annoba, tashi mai farar k afa, tashi tsinanniya ki fice mini daga gidan d Shigowar Asabe wadda ta k araso itama tana jaan d ayar k afar Dijen ta k arfi da yaji ne ya basu damar fara janta a k asa daga nan kan sallayar da aka d aurata a kai. Har yanzu hannunsa yana a cikin nata bai cika ba dan har sun fara d an motsi da shi shima, sunayen Allah kawai yake karantowa yana k arin danne zuciyarsa amma inaa ya gagara danneta! Bai san lokacin da ya mik e ya k arasa inda suke ba yana zuwa ya d ago Asabe ya kifa mata wani gigitaccen Marin da sai da ta kifu a k asa kan simintin d akin. Duka Kaka ta rufesa da shi tana cewa shege d an iska tsinanne d an tsinanniya! Wallahi yau ka tab owa kanka tsuliyar dodo! Tunda ka tab a ta zaka sha mamaki kuma har da kai za a bar gidan nan bari na har abada! Y an iska shegu y an tsinanniya ballagaza in sha Allahu ko bayan barinku gidan nan sai dai ku wulak anta ba za ku ga dai-dai ba wallahi sai kun tagaiyy Inaaaaa! Ba zai iya ci gaba da tolerating d inta ba dan haka ya wani Irin juyowa a take ya damk i wuyanta ya tafi da ita jikin bangon d akin ya mak ure ta cikin mad aukakin b acin rai ya ce Enough! Enough!!Enough!!! Ya Isa haka, haukar ta ki ta Isa haka, k iyayya da jahilcin na ki ya yi yawa haka. Kuma bari ki ji sai dai ke ki mutu a kai ki a binneki ki bar mu a gidan ubanmu wallahi ba ki Isa ki koremu ba nan gani nan bari, kin ji ko baki ji ba!? Ya yi maganar cikin daka mata wata uwar tsawa kamar wani mahaukaci sabon kamu. Kaka ita kam zuwa yanzu bata ma san inda kanta yake ba dan har ta fara jiyo k amshin barzahu. Sosai mutane suka taru a kansa har da su Usso ana ta kiciniyar k arin ganin an kwace wuyan Kaka daga hannunsa amma sam ba ya jinsu, kunnuwansu iyaka tsinuwa da zage-zagen ta a garesu kawai suke dad a yi masa ringing a brain nasa shiyasa ya yiwa wuyan nata ruk on life support dan haka sam suka gagara kwatar Kaka daga hannunsa. Babu wanda ya lura da shigowar Mallan wanda wani makwabcinsu ya je takanas ya d aukosa daga asibiti dan hayaniyar ta cikin gidan ta fita har waje ana jiyosu tun d .ba su ga shigowar sa ba sai gigitaccen marin da ya d auke Minu da shi ne ya mayar da hankalin kowa a kansa. Still duk da hakan bai sanya Minu ya cika wuyan Kaka ba! Wata kalar tsanar matar ce take dad a tasiri a cikin zuciyarsa da ya fuskanci tabbas bata da wani burin da ya wuce ta tarwatsa kawunansu gaba d aya su d aice su wulak anta, baya jin zai tab a yiwa wani mahaluk i a fad in duniyar nan kalar tsanar da yake ji tana shigarsa a yanzu ta Kaka ba! Aminu!!!!! Mallan ya daka masa wata uwar tsawar da ta karad e ilahirin cikin gidan. A hankali jikinsa yana wani
Chapter 46 · 0% Book details