← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 59

Sashe 24

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

sam ya gagara b oye zalamarsa a kanta yau d in dan kwana biyun nan dama kamar wani wanda aka yiwa xdubu na k aunarta haka yake ji, komai da yake ji a kanta ya nunku bilaadadin. Tunda ya kinkimeta su Scorpion d in suka sunkuyar da kai, Sai da ya dakawa Oscar tsawa tukunna ya zo ya kunna motar suka ja suka bar wajen su duka hud Kwata-kwata tunanin Ma a bai bashi ya je ya kaita gidansu ko ya kira wani nata ba dan a nashi ganin hakan ka iya janyo tangard a da delay a had uwarta da Likita.. Suna wucewa aka fara firfitowa ana dudduba mutanen da suke zuzzube a wajen cikin jini, mutane wajen ashirin ne suka ji rauni yayinda ake da tabbacin mutuwar d aya dan a mak ogwaro Oscar ya chaka masa wuk a gashi idanunsa sun k afe suna kallon sama, wannan saurayin shima suna tunanin ya rasu dan ko shurawa bai yi ba. Akwai cases da yawa irin haka har da wanda ya kai shekara biyar a hannu ana kan yi dan duk yadda aka kai ga jin tsoron su indai suka kashe rai ana iyaka bakin k ari wajen tsayawa a kan abun sai dai matsalar da ake samu itace idan anje sai a dinga danganta abun da Oscar yayinda shi kuma Oscarn yana da file ma a Dawanau! To da haka ake fakewa kuma har gobe an gagara kullesa a gidan mahaukatan where he truly belongs. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 10. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Da mugun gudu Usama ya shiga cikin gidan nasu yana haki hannunsa yana d igar jini. A hargitse waenda suke tsakar gidan suka taso aka yo kansa da tambayar mai ya faru? Yayinda na cikin d aki suka fara firfitowa Cikin haki ya ce Su Ma a ne suka kawo hari amma ni basu tab ani ba garin gudu ne na fad a a kan langa-langar da aka jide a k ofar shagon Aliyu shine na ji ciwo. Cikin fad a Iyya ta ce Amma sai da aka ce kowa ya killace nasa ko? Garin yaya ya fita? Cikin rashin fahimta Inna ta ce mai ya faru? Fad a ake yi? Juyawa Iyya ta yi ta kalli Zainab ta ce ke baki je aiken da na yi miki d azu wajenta ba? Turo Baki Yarinyar ta yi ta na guna guni. Cikin taraddad i Iyya ta rafka salati ta ce yanzu a batun rai da mutuwar ne kika sako kishi da b akin hali dan buhun ubanki? Ta yi maganar tana mai kai mata duka. Cikin b acin rai Ramma ma ta rankwashi kan Yarinyar ta ce shegiya mai irin halin uwarta Dai-dai nan kuwa Uwartata ta shigo .kamar yadda takeso ta dawo a gajiye hakan kuwa ta dawo dan Ya Muhammad bai dad e da komawa barci ba da kyar da taimakon allurai, tun d azu ya tashi Mallan kuma ya aiki Minu ya ce sai ta tayashi rik esa, har gula sai da ta sha a ciki garin rik esa. Gashi basu ci abinci ba wai duk su biyun azumi suke yi tun jiya suka cewa Inna kar ta kawo abinci shi kuma Ya Muhammad an hana sa cin abinci wai za a yi masa wani gwaji ba zai ci abinci ba for 24 hours. Wani irin takaici ne ya tasowa Inna na ganinta amma sai ta d auke kai kawai. Tana shirin yin magana Asaben ta ce Ramma mai ya faru kike dungure mini kan y Sai kuma ta yi tsaki kamar an tambayeta ta ce ko da yake ba ta ke nake ba, duk a gajiye nake, Mallan da iyawa wai ai kwanana ne dan haka in je in tayashi jinya. Shiruuu, kowa ya yi yayinda wasu suka fara tunanin anya kuwa kan Asabe babu motsi?. Tsaki ta sake yi ta kalli Zainab ta ce zee d aura mini ruwan wanka, in samu in yi wanka na yi sallah in huta Iyya ba ta san lokacin da ta ce ikon Allah ba. Shiruu tsakar gidan ya kasance har ta zo ta wuce su tana tafe a gajiye, sai kuma ta juyo ta kalli Inna wadda ta bita da kallo kawai, ta ce Yauwa, shima Mallan d in Ina ga gajiya ce ta tarar masa yanzu haka ma drip aka d aura masa ya ce in sanar da ke Duk yadda Inna ta so sai da ta ji wani irin zazzafan kishi ya taso mata, wato bashi da lafiya ba zai iya gaya mata ba sai k anwar bayanta ce zai aiko ita zata gaya mata kuma daga ji ma rashin lafiyar tasa ba wata serious bace ba tunda gashi har y ar tayin kwana yake nema amma ita ya gagara d aukar wayarta Da sauri ta kawar da tunanin ta ce kawai daga nan ta juya kan Usama ta ce ka ga Dije? A take hankalin kowa ya koma kan Yaron. Jinjina mata kai ya yi ya ce eh, na ganta ana ta gudu ita kuma tana tsaye tana kallo Dai-dai nan wata mak ociyarsu mai suna Ladidi ta shigo tana rafka salati Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yanzunnan labari ya iske ni Halimatu Ma a ya yi garkuwa da Dije. Salati tsakar gidan ya d auka ana tafe hannuwa yayinda Inna ta tafi ta zube ta zauna dab ass! A dede k ofar d akinta inda suke dama ga damuwa ga bak in ciki yanzu kuma ga mad aukakin tashin hankali duk sun had e mata waje guda. ************ Idan ana maganar Fada (palace) to tabbas wannan ta cika ta kai Fada har ta wuce hakan ma Girmanta ya kusan kai girman wani tafkeken filin ball d in, yayinda adon ta ya bambanta da sauran Fada dan ita nata ado da tsarin na musamman ne! Kamar yadda bangon ko wanne d aki da parlour na duk wani mai fad a a ji a cikin masarautar ya kasance an yi masa ado da asalin gold, haka itama wannan Fada ta ke, sam! Girma da fad inta bai hana an yi mata wannan ado na gold a bangonta gabas da yamma kudu da arewa ba. Bayan ka shigo cikin asalin ginin na Fadar wanda Dogarai da sojojin masarautar suke tsaronta kamar rayukansu, sai ka bi ta k ofofi uku tafka tafka waenda suma ake bawa tsaro ba na wasa ba tukunna za ka Isa Babbar tangamemiyar k ofar da zata sadaka da main hall na Fadar! Ana bud ofar bayi ne (masu lamba d aya) sanye da jajayen kaya da bak in d ankwali mazan kuma da bak ar hula a zaune sun d an rissinar da kawunansu hannayensu hard e a kan ruwan cikinsu waennan bayi sun kai su d ari biyu a zazzaune tun daga farko har zuwa kusan tsak iyar Fadar a kan layi..layi wajen ashirin, layi goma a waje guda(b angaren dama) layi goma a waje guda(b angaren hagu) sai hanyar wucewa wadda ta kasance a saitin k ofar shigowa a tsakiyarsu, haka nan suke zaune cikin tsananin tsari opposite kujerar Sarki wadda take a saman wasu kujeru guda biyu ta su Wambai da Waziri kujerun da sai ka bi ta wani stairs mai wajen taku kusan goma waenda aka k awata da lights da gold tukunna za ka k arasa kujerun Wambai da Wazirin yayinda ta Sarkin take a saman tasu dan a k alla itama sai ka bi ta stairs d in da ke a tsakaninsu kusan guda goma tukunna za ka risketa a tsakiyarsu (chan sama) kuma ta fi ko wacce kujera girma a wajen dan ta ninka ta su sau biyar a tsayi da fad i adonta kuwa tsayawa fad a ma b ata Baki ne Ta b angaren dama chan k asa gefe guda kafin ka fara taka stairs d in da zai sada ka da kujerun Wambai da Waziri har a kai ga ta Sarki wata tattausar shimfid a ce ta alfarma tafkekiya wadda a k alla za ta ci zaman mutane saba in, a kan shimfid ar a kwai wasu manya-manyan pillows na sarauta na zama masu taushi sai k anana guda-goma a zagaye da ko wanne d .waenda a k alla sun kai guda tara a kan dardumar. Opposite wannan shimfid a gefen hagu nan ma wata shimfid ar ce irinta sak a tsari da fasali. Baya ga waennan Bayi wajen su d ari biyu da suke zazzaune irin zama na k anci, da waensu Sojojin masarautar guda biyu a tsaye suna kallon kujerar Sarki sun saka k ofar shigowa cikin Fadar a tsakiya babu kowa a cikin Fadar kuma baka jin k arar komai sai na standing Ac wajen guda ashirin da suka yiwa fadar k awanya. Tafkeken Agogon fadar ne ya buga k arfe tara dai-dai sai kuma ya hau k irge daga d aya zuwa tara dai-dai yana gama k irgawa Sarkin k ofar Fada (wanda yake tsaye a bakin k ofar shigowa ta waje) ya ware murya ya ce Gyyyaaraa kintsi!!! Gimbiya Zakiyya y ar sarki jikar sarki yayar sarki, an gaisheki sarauniya. A take waennan bayi da suke cikin fadar suka sake shan jinin jikinsu suka sake k amewa k am! Dai-dai Sojoji guda biyun nan da suke tsaye k yam suma a bakin k ofar ta ciki suka kama hannun k ofar ko wanne ya rik e handle d aya a tare suka bud ata suka wangale mata k ofar sannan suka saki kafin su durk usa alamun girmamawa a gareta. Ta tsakiyar bayin nan da suka hau kan layi ta zo ta wuce alkyabbarta na jan k asa bayi mata (masu lamba d aya) guda goma a bayanta suna binta sai Hadimai maza guda biyu. Bata ko kalli kowa ba ta je ta nemi guri ta zauna a kan dardumar dake a hannun dama, kan pillow d aya babba ta yi zama irin na sarauta, yayinda bayinta suka nemi waje suka zauna a k asa bakin k ofa suma suka jona layin waennan bayi suka yi irin zaman su. Ta na wucewa sojojin nan suka mik e suka mayar da k ofar suka rufe ko gama rufewa ba su yi ba Sarkin k ofa ya sanar da
Chapter 24 · 0% Book details