Sashe 34
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 5 min read
yi yana mai fitar da wani huci mai zafi, sai kuma ya d ago ya kalleta yana murmushi .Ba k aramin dad i ya ji ba dan sai da ya yi hawayen farin ciki, sannan ya shiga jero mata albarka da addu i masu tarin yawa A tsari dama sai an d aura aure da sati d aya tukunna za su tare, dan yanzu haka ma ginin gidan nata inda za ta zauna flasta ake yi ba a kai ga yin ko fenti ba, shima kuma Mallan dama ya ce musu su bashi sati d aya ya yi siyayya. Ya san dan sati d aya dai Kaka zata yi hak uri ta k ara musu, za a sha daru kam amma ya san za ta k ara musu kuma ma Mahaifiyar Yusufa ta ce tun ana i saura kwana biyar d aukar amaryar za ta taho dan haka ya san ba shi da matsala tunda ba laifi suna shiri da matar idan ta ga dama. Adduarsa d aya Allah ya basu zaman lafiya Allah ya bawa Dije farin ciki ya had ata da marar adadin alkhairi. Ba laifi Inna ta d an sake dan sai da suka gama lissafin komai har aka kusa shiga sallah, suka shirya akan gobe zata je ta siyo komai na kayan d aki tukunna ya mik e ya nufi k ofa yana mai ci gaba da saka musu albarka, sosai ya ji kaso hamsin na damuwar da yake a ciki ya yaye da ya samu Inna ta kulashi kuma ta bashi goyon baya. Ta so ta yi masa maganar k in d aukar wayarta da replying message d inta da yayi kuma mai ya sa ya turo mata Asabe amma kawai sai ta basar dan kwana biyun nan komai ya sure mata a ka ga rashe-rashen da aka yi sun sake sanyayata azu da Mallan ya zo shiga d akin Inna bayan ya shiga sai ya mayar da k ofar ya rufe, wannan dalili ya sanya har ya taso ya iso bakin k ofar ya sa hannu ya bud e sam Asabe da Kaka basu san ya k araso ba. A mugun zabure suka d an matsa da suka ga an bud ofar sai kuma suka d ago a tare wanda hakan ya janyo suka k ume k ummm!!! A gigice Kaka take sosa wajen tana kallonsa yayinda Asabe ta kawar da kanta gefe ta shiga kame-kame. Yatsine fuska ya yi cike da kalar tausayi irin mai yasa kike haka d innen yana daff da yin magana cike da borin kunya ta ce dan ubanka to ba lab e muka yi ba! Ya riga ya makara sosai dan gashi ma ya ji har wani ya fara kiran sallah dan haka ya wuce da sauri yana mai cewa ni ban ce komai ba Kaka, bari in tafi masallaci na makara. Yana fita Dije ta fashe da wani irin kuka, sosai Inna take jin tausayinta kwana biyun nan dan haka ta janyota jikinta ta rungume ta shiga lallashinta..wanda sai da ta yi da gaske tukunna aka samu ta yi shiru. Wai yau ita Dije ce zata auri Yusufa mutumin da ko muryarsa ba ta son ji! Ai kuwa d an halak d in nata a take kiran wayarsa ya shigo wayar Inna dan ita bata da waya. auka Inna ta yi suka gaisa daga nan ya fara kame-kame, murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi kawai ta mik awa Dije wayar ta mik e ta fita dan ta je ta yo alwallah, ai kuwa ko gama fita ba ta yi ba Dijen ta kashe wayar kamar yadda ta yi jiya da shekaran jiya, Allah ya sota Innar ba ta ganta ba ta k arasa fita daga cikin d akin abunta. Bayan fitar Inna Yusufa ya kira ya fi sau goma amma ta k agawa kuma ta goge misscalls d in k arshema kashe wayar ta yi gaba d aya da Innar ta dawo ta ce mata chaji ne babu. Bayan ta je ta yi alwallah ta dawo, a hankali ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta a take lissafin Ma ah ya fad o mata Mugu kawai! Ta fad i hakan a ranta tana shafa hannunta dai-dai inda ya tab a rik ewa kwanaki wanda sai da wajen ya yi kwana uku ciff yana yi mata zafi-zafi!! Haka kurum na aure shi ya kakkarya ni! Mtswwww ta Yaya ma zan auri wannan tshohon, kuma d an daba Allah ya Isa ma ni da ya ce yana so na, marar kunya ko a gidan wa aka ce masa mutum yana zuwa neman aure da kansa oho masa!!!! Ta yi maganar duk ita kad ai a cikin ranta. A hankali kwakwalwarta ta shiga zoomo mata ranar nan ita da shi a asibiti! Ba zan tab a cutar da ke ba Khadijah!! Maganarsa ta dawo mata tarr kamar yanzun yake fad Da k arfi ta runtse idanunta sakamokon yadda ta ji ilahirin jikinta ya amsa. A hankali ta shiga sauk e ajiyar zuciya sai kuma ta yi tsaki ta ce cutarwa kuma ta nawa!!mugu kawai, har da had in guiwarka ne ya sanya za a yi min aure Daga haka ta runtse idanunta ta shiga neman bacci afujajan tana mai sake danna tsana da kyamar Ma ah a cikin zuciyarta. Tausayin Mama ne ya fad o mata dan ko d azu sai ta ji ana fad ar halin da take ciki, a hankali ta ce Allah ya baki lafiya, Albasa ba ta yi halin ruwa ba. Dan Mama tana da kirki kuma tana sonta, tun bata kai haka ba in dai suka had u ta gaisheta sai ta bata alawa ko kud i, tun ba ta karb a har ta zo ta fara karb a. Matar tana da kyauta ba ita kad ai ba hatta Yaran layin haka nan duk take yi musu alkhairi. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 16. Humairah Bulama. Mikiya writers Association.