Sashe 36
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
in wadda ta matso kusa da su da kyar dan da kyar take iya jan numfashi ma Ta na gama gani duk wani k arinta na son ganin ta ci gaba da tsayuwa a kan kafafuwanta ta ceci y artata ya sire! A take ta tafi ta sulale a wajen jinta ganinta tare da kuzarinta duk suka d auke d iff. A hankali Wambai ya matso ya ce Tabbas maganar ki dutse! Amma duba da matsayin Gimbiya inaga wannan hukuncin ya yi mata tsauri Juyowa ta yi ta wani kallesa daga k asa ta d ebosa ta kai sama ta watsar, kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta magantu ta ce Inaga baka san matsayi da girman wanda ta yiwa laifin ba! Kuma ni a yadda na san tsarin masarautar nan in dai ba Sarki mace ta tab a aura ba to tabbas hukuncin jifa bai sauk a daga kanta ba! A hankali Waziri shima ya matso ya ce mun ji kuma mun sani amma inaga gara a sakata a kurkukun ban kwana ta mutu a chan a kan dai a jefeta! Gimbiya ce fa!! Sannan a gani na wannan hukuncin da kika yanke hukunci ne wanda ya kamata a ce an zauna an tattauna shi a Fada tukunna, tun da na san ba daga Sarki hukuncin nan ya taho kai tsaye ba! Idan kina yanke hukunci da kanki kai tsaye haka to mu meye amfanin mu? Kuma fa ki duba girman al amarin a ganina ya kamata a tsaya a tattauna Shiru ta yi kawai ta na bin motar da ta shigo d aukar Uwar Marayu, sai da aka zo aka d auketa aka sakata a ciki aka wuce da ita tukunna ta kalli Fadawanta maza ta ce su rufe mata gates d in filin kar su bar kowa ya shigo! Dan ta san yanzu za a taru! Sannan ta juyo ta kalle sa ido cikin ido ta ce Saifuddeen! Wallahi ko kaine ka aikata laifin yunk urin tab a mini Sarki to sai na kaika lahira at the very moment da na yi finding out tun kafin a shiga meeting a wanke ka ko kuma a kaika gidan Yarin da na san za a iya fito da kai daga baya. Daga haka ta d auke kai ta kalli bayin da suke wajen durk ushe cikin tsawa ta ce Ku jefe min ita na ce!! Ko sai raina ya b aci? A hankali suka mimmik e suka je suka tsaya a gaban uban tulin dutsunan suka fara d auka suna jifanta da shi Sai da kanta ya fara lilo yana shirin barin gangar jikinta tukunna suka tsayar wanda abunda ba su sani ba tun a jifan farko da wani bafade ya yi mata yanzun zuciyarta ta bugu ta mutu! Barori ne ta koina zagaye da filin ta waje a durk ushe suna kuka, hatta barorin da suka yi jifan suma akwai masu kukan a cikinsu, Barorin Gimbiya Mariya ne kawai suke farin cikin cika aikin uwargijiyar tasu da kuma wasu a cikin barori waenda Gimbiya Sakinar ta tarewa rawar gaban hantsi da kuma waenda suke jin haushinta Suna gama aikinsu suka bar wajen suka koma chan nesa suka zube a k asa. Jikin Waziri har wani irin karkarwa yake yi! Tabbas ba su da amfani a masarautar nan he really can t believe he s this powerless da har ba zai iya sakawa a yi ba ko kuma ya hana a hanu ba. Kallon Nuraddeen kawai yake yi wanda ya matsa kusa da Gimbiya Mariya suna wani k us-k us, sosai ya k ura masa ido yana mamakin sa kamar ba shine Gimbiya Mariyar ta disga a Fada satin da ya gabata ba! Kalli fa hatta Ubansa Mahaifi bai sanarwa abunda take shirin aikatawa ba bayan gashi ga dukkan alamu shine ma a gaban komai, sai kawai gani Wambai d in ya yi tare da kowa. Wanne irin kusanci ne haka a tsakaninsu sannan what are they up to? Dan tabbas Nuraddeen wanda ko a wajen Ubansa ba ya juyuwa bai kamata a ce ya tsaya suna had in kai da Mariya ba ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Tabbas akwai wata a k asa, ko kuma a tsakaninsu wani yana cin dunduniyar wani ne Ya aiyyana hakan a ransa Kai kana ganin fuskar Gimbiya Mariya ka san cewa she s relax ta sauk e wani nauyi. Ana gamawa ta gama magana da Nuraddeen d in ta wuce bayan ta tamke fuska saboda kar ma wani ya ga rangwame a tare da ita. Bayanta kawai ya bi da kallo yana wani irin murmushi Tabbas matar nan sai na yi da gaske dan ta wuce tunani na! Gimbiya Sakina yanzu haka shekarunta sun fi arba in kuma ita ce za a ce Babba-Babba a cikin y a matan masarautar dan ko Giwar Mata maza ta dinga Haifa haka itama Mai Babban D aki y a maza ta yi ta Haifa da farko-farko wannan dalili ya sanya da ta haifi Sakina sai duk ta girmewa ragowar y an matan Giwar Mata kuma bayan ita sai da ta haifi mata goma sha uku tukunna ta haifi maza biyu amma da ikon Allah yadda ya tsara mata ba ta tab a ko auren fari ba! Wanda mutanen da basu gama yarda da k addara ba suke cewa asiri ne aka yi mata. Masarautar ta KHAK IL tana da collaborations da dayawan k asashen nahiyoyin duniya wadda ita ce a sama-sama saboda girma da arzik in k asar wanda a yanzu haka power su take rawa sabida rashin capable leader! Dan kwata-kwata ko magana da iya tafiyar sarakuna Sarki ZainulAbiddeen bai gama iyawa ba ballantana azo kan mahimman aiyyuka, rannan da jirgin wasa d an k arami ya tafi fada ya manta yana mik ewa jirgin ya fad o kowa ya gani, da ikon Allah duk da girma ya riskesa amma har yanzun ya gagara ko da kamanta yi musu d aya daga cikin abubuwan da suka kamata ne, dan ko baya ga k arancin shekarunsa ma haka nan yake yin wasu abubuwan k asa da shekarunsa. Wannan ya sanya ake tunanin nad a Gimbiya Sakina a wasu fannukan kafin ya gama girma ta dinga wakiltar k asar tunda ita ta yi karatu har PhD a k asashe mabambanta kuma ta sassan mutane sannan she s very social shiyasa aka bayar da shawarar a nad a ta ko kuma su dinga wasu abubuwan tare kafin ya gama mallakar hankalin kansa, duk da kuwa ba a hakan amma a fara a kanta tunda ba su da yadda za su yi dan matan Sarkin sai da suka san yadda suka yi suka haramtawa Waziri da Wambai sarautar k asar KHAK Nuraddeen ya je mata da tayin Soyayyarsa dukda kuwa ta girme masa sai dai shi sam bai damu ba dan a yadda ya ga ana shirin yi musu raba dai-dai ita da Sarki tabbas idan ta amince masa to kamar ta yi masa rabin aikin da ya tisa a gaba ne, amma sai ta yi fatali da shi har kusan sau uku wannan dalili ya sanya ya koma b angaren Uwar Marayu wadda tunda aka fara batun ta rikice ta gigice dan ta san in dai aka fara hakan to suna iya janyowa sarautar ta bar hannun d anta dad in d awa ta fi so ta samu full control da power bata k aunar sharing ko da d igon girman kujerar ne da kowa. Wannan dalilin ya sanya ta had a mata gadar zare ita kuma ta afka ba tare da ta sani ba! Wanda daga ita sai Nuraddeen d in ne suka san kuma suka fusatata suka k ulla mata abunda ya sanya dole sai da ta kai ga yunk urin kashe k anin nata! ***************** Jiya cikin dare har su Dije sun kwanta ta ji ana tab ofar d akinsu dan Inna ta tafi d akin Mallan. Tana bud ofar ta ga Sumayya da wasu k awayenta y an islamiyyar su a bayanta. Murmushi ta yi cikin sanyin da ba d abiarta ba ta ce Ashe da gaske kike Daga haka ta bud e musu k ofar suka shigo ciki Dama Sumayya ta iya k unshi sana arta kenan, dan haka suna zama ta shiga zana mata jaa na gargajiya. Sai da ya yi ta cire ta saka mahallabiyya tukunna ta zana mata bak i shima hannu da k afa mai masifar kyau. Zuwan nasu ya taimaki Dije kam dukda babu abunda ya ragu na game da damuwar da take a ciki amma ta yi raha dan duk su ukun akwaisu da barkwanci. Ba su kwanta ba sai k arfe uku dan haka suka d an makara sallar asuba wanda kururuwa da koke-koken Kaka ne ma ya tashe su. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 17. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Cikin gigita duk suka yo waje wanda hakan ya yi dai-dai da k arasa cikar tsakar gidan. Idanun Kaka suna sauk a a kanta ta k araso gareta ta na zuwa ta sa hannu ta shak eta wanda ko yunk urin kirki idan Dijen ta yi tsaff sai ta zubar da ita a wajen sakamokon rashin k arfin jiki na tsufa da take fama da shi Shegiya marar mutunci marar Imani!!!! Dama na san wallahi ke da d an iskan kwarton kin nan ba za ku hak ura ba! Yanzu ke kin fi son d an daba akan mutum mai mutunci?? Da kika san ba zaki auresa ba ai da kin fito kin fad a an hak ura ba wai ki tura shi ya kashesa ba! Salati tsakar gidan nasu ya d auka yayinda yuuuuuu!! Wani irin jiri ya d ebi Dije ta tafi zata zube a wajen su Sumayya suka ruk o su ita da Kaka wadda ta biyo ta luu za ta fad i itama. Da sauri Mallan ya k araso wajen ya rik e Kaka idanunsa jazir alamun ya ci kuka. A karo na ba adadi daga fitowar Kaka zuwa yanzu Asabe ta sake cewa Kaka mai ya faru? Ya rasu fa kika ce, Yusufan ne ya rasu. Cikin kuka mai cin rai Kaka ta ce Wallahi Yusufa ya rasu Asabe ya riga