Sashe 29
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
irji sai sun jaaa sun kai ta har k asan tumbinsu kayan ciki sun fito tukunna suke jefar da su! Hakan da aka gani ya sanya aka ci gaba da guduwa. Grenade ne ya yi kan Minu ya sare shi da wuk a a hannu Allah ya so ba sosai ba dan ya goce kuma ya kare sarar ne dan Kansa Grenade d in ya kaiwa hari Allah ya tak aita, garin guje-guje (wani ya taho da gudu) ya bige sa aikuwa a take ya zube a wajen, dan haka Grenade d in ya sake d aga wuk ar yana shirin sauk e masa ita a kai kenan Allah ya kawo Ma a wanda ya hangosa tunda ya nufesa ya hankad e sa ya tada Minu mistakenly ya tura Grenade d in kan su Scorpion ai kuwa suka zube rikicaa makamansu suka fad i a k wasu a cikin samarin layin kuwa waenda basu kai ga guduwa ba suka yi kukan kura cikin zafin nama suka yi kansu wani a cikinsu ya d auke zabgegiyar wuk ar scorpion bai yi wata-wata ba ya sauk eta a kan Grenade dama shi kad ai ne Allah bai bawa ikon tashi da wuri ba sakamokon k unar da take a jikinsa ya sanya dama dauriya ce kawai yake yi. arasowar Ma in shi ya taimaki su Scorpion amma da tuni suma an kasheshu, da kyar ya kwacesu ta hanyar kaiwa wajen mutun biyar sara a lokaci gudu, suma kuma mutanen dama tunda suka ga ya shiga fad an aka fara guduwa. Suna tashi suka yi kan Minu wanda jiri ya hanasa tashi a wajen nan ma Ma a ya sake taresu ya ingiza su cikin gida, ai kuwa suna gama shigewa aka samu wani mai k arfin Hali ya biyosu ya datse k ofar. Yayinda su kuma suna shiga cikin gidan kawai suka ga wuta tana ci kamar hauka sun cinna musu wuta ta baya ashe, ga Maama a yashe a tsakar gidan wadda tun fitarsa ta farko da ta yanke jiki ta fad i bata sake shurawa ba. Da gudu suka nefeta duk su ukun dan shima sai yanzu ya ganta d azu da ya shigo kunna ruwa sam bai ganta ba. Yana zuwa ya d ago fuskarta, da mugun sauri ya runtse idanuwansa sakamokon yadda ya ga gaba d aya halittun fuskartata sun zaizaye sun koma gefe guda inda ta kwanta a kai Wani irin wutar bala i ce take taso masa yana k arin dannewa dan ya san idan ya fita a haka tabbas sai ya kashe duk wani rai da yake a wajen nan Cikin tsananin fushi Scorpion ya ce Shi fa Yaron da kake ta karewa a yanzu inda ace zai samu dama wallahi da sai ya kasheka!!! Bai ma fa san kana yi ba, ga gawar Grenade chan yashe a waje inaga hakan ya isa ya sanya ka fahimci idan baka daina katsemu ba to muma duk sai an kashe mu! Sannan ka gaya min ta yadda zaka fita da Mama a cikin gidan nan idan ba a yi clearing wajen nan ba??? Yana gama fad in hakan ya d auki waya ya kira Yaronsa yana d auka ya ce wai dan durun uwarka kuna Ina? A buge Saurayin ya ce go slow ne ya tsare mu a kan gada, ka san tal udun da ka ce mu zo dole sai an bi ta cikin gadar ruwa Tsaki ya yi ya jefar da wayar da wani irin mugun k arfi ta tarwatse bai samu ya ji na gefen saurayin wanda ya ke ce masa mun kusa fa Oga ka d aga masa k afa a china yake shi yanzu haka ba. Tabbas ya san in dai ba Ma ah ne ya shiga fad an nan ba to sai an kashe su su duka hud un a yau! Dan tun d azu ya fahimci ba iyaka samarin layin bane kusan kaff y an Unguwar ne suka yi musu taron dangi, yanzu haka kuma hayaniyar da yake ji a waje ya san sun ninka na farko! Ko da ace kanshi ba ya ja ya san cewa Sarkin yawa ya fi sarkin k arfi Ammafa dukda haka ba zai zuba ido a gaban idanunsa Ma a da Mahaifiyarsa su mutu a cikin wutar nan ba ba tare da ya tab uka uwar komai ba dan haka kawai sai ya juya ya nufi d akin Ma ah d in wanda yake a soro ya bud e ya shiga! Sun bar wuk ensu a waje dan haka yana shiga wajen da ya san zai ga wuk e da adduna ya nufa. Wata zabgegiyar Adda ya d auka ya d auki wata wuk a mai mugun kaifi ya sak ale a k ugunsa ya fito. A bakin k ofar d akin ya ga Ma a a tsaye rik e da Maama a hannunsa zai yi magana ya ga kawai ya wucesa ya ajjiye ta a d akin nasa dan nan ne kawai hayak i bai bule ba a cikin gidan yana ajjiyeta ya d auki wuk e ya fito ransa a mugun b ace! Ihu suka saka suna yi masa kirari yayinda shi kuma ya k arasa bakin k ofar gidan ya saka dukkan k arfin da Allah ya bashi ya dake ta da k sau uku ya kai mata duka ta b alle ta fad i a k asa, y an wajen kuwa kamar jira suke suka hau yi musu ruwa fetur basu kai ga fara cilla musu itace masu ci da wuta ba suka yi kansu Sun fi su d ari wanda kaso goma ne kawai za a ce suka d auko makamai! Zuciya mai cike da Imani da rashin iya aikata kisan kai ya sanya suka rikice gashi wani irin chachchaka Ma a yake yi musu da hannu bibbiyu! Tsoro da kuma ganin ana ta kashe wasu ana jiwa wasu rauni ya sanya wasu kaso hamsin a cikin waenda suka yi saura sake guduwa dan haka suka sake samun galaba a kansu! Ammafa suma an sassaresu, dauriya ce kawai suke yi da kuma sabo shiyasa basu galabaita k arfinsu ya gushe ba. Gudu sosai ake yi zuwa yanzu dan tiyagas Ma a ya koma cikin d akinsa ya d auko ya zo ya sakar musu dan haka baka iya ganin komai sai dai kawai ka ji sauk ar wuk a a ruwan cikinka, su kuwa su duka ukun akwai glases d in da suka saka mai tare hayak Sai da ya yi clearing wajen ya tabbata it s safe tukunna ya koma cikin gidan da mugun gudu ya kinkimo Maama ya d auki wani briefcase dan sosai gidan yake ci da wuta! Ya fito da ita, suna fitowa gas ya yi bindiga wutar ta fi ta farko. Da gudu ya saka Mama a mota ya bawa Oscar key ya shiga ya zauna tare da ita yana kallon fuskarta yana jin wani kalar wutar bala i da k unci suna taso masa .Yana shiga mota Yaran Scorpion suna k arasowa wajen! Har an tayar da motar Ma a ya yi kiransa.. kamar zai hanasa sai kuma abunda ya faru d azu da rijiyar da ya tsallake da baya duk a yau suka dawo masa tarr cikin kwanyarsa dan haka kawai ya ce masa duk rintsi kar ku tab a gidansu Khadijah! Da y an gidan. Jinjina kai Scorpion d in ya yi ya sara masa tare da addu ar Allah ya bawa Mama lafiya tukunna ya juya ya koma kan tawagar Yaransa waenda zuwa yanzu har sun cinnawa gida uku wuta. Suna wucewa .a hankali yake bin gidansu da kallo yana ganin yadda yake ci da wuta kamar ba gobe! Ya san ko tsinke ba za a iya fitarwa ba dan da kyar shima yanzun ya iya shiga ya d auko Mama tare da takardun credentials d insa dukda kuwa bayajin akwai wani amfani da za su yi masa. Sai a lokacin tukunna ya tuna yau fa tun d azu bai ga Mallan idi ba! Tsaki ya yi ya kawar da kansa a ransa ya shiga addu Allah ya sa ya na ciki ya bugu yana ta uban bacci, bai ji komai ba har wutar ta cinye sa A chan gidan su Dije kuwa Mallan yana gama fahimtar komai ya juya zai fita shi da kawu Isa a gigice, Kaka ta fito ta ce Duk ku biyun idan kuka fita sai na tsine muku Wallahi, ba zai yiu in rasa y ana har biyu akan wani Minu wanda ba a da tabbacin ma d anka ne ba. Ta k arfi Inna ta runtse idanuwanta tana gani n wani irin dishi-dishi, a hankali ta juya ta koma d aki ta d auko mayafinta ta zo ta nufi k ofar fita. Mallan bai motsa ba kuma bai ce mata komai ba sai da ta k araso daff da shi tukunna ya ce mata ki koma ki zauna Allah yana tare da su Rikitattun idanuwanta da suka rine da kuka da tashin hankali ta d ago ta watsa masa sannan ta ce bani hanya in wuce! Idan kai zata iya tsine maka ai ni ba zata iya ba! Eh ai dama a tsinen kike!! Shegiya gantalalliya! Ina amfanin tsinewa tsinanniya!? Cewar kaka Da sauri kawu Isa ya ce Kaka ki yi hak uri ba za mu fita ba ki koma ciki kin ji!!! Cikin b acin rai ta ce ai Isa yau kuma a yanzu za mu yita ta k are!! Idan ka ga na koma ciki to Mallan ya zab a ko ni ko Dije da uwarta!! Dan wallahi na gama zama da su k ashin inuwa d aya!!! A hankali Mallan ya runtse idanuwansa sannan ya bud e ya ce Kaka dan girman Allah ki yi hak uri ki tsaya tukunna a gama wannan tashin hankalin da yake wakana a waje!!! Cikin halin ko in kula ta ce yo ni Ina ruwana da wani tashin hankali?? Ai bai shafe ni ba tunda babu d aya daga cikinku a wajen! Abunda nake so yanzu shi za a yi idan kuma su zaka zab a to fad a min tun wuri in fitar maka daga gida in shiga gari!! irjinsa ne ya ji ya