← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 59

Sashe 51

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

jiya da na yi wallahi! Abunda ya bani mamaki ya sanya ban shiga abunba shine da k afafuwanta na ga ta shiga wajensa sai dai shigarta ke da wuya na fara jiyo ife-ifenta to dai har yanzu da nake gaya muku tana chan a wajensa sai abunda Hali ya yi. Ku yi hak uri dan Allah ku Bai kai ga idawa ba saukar tab arya ta dira a goshinsa daga Ramma dan a zuciye ta saka hannunta mai lafiya ta d auki tab aryar dake yashe a gefenta ta maka masa duk da kuwa tana fargabar me Ma ah zai yi mata idan ya ji labari duk da ta ji Mallan Idin ya faiyyace ba sa shiri amma dai uba ai uba ne! Tayi ta samu daga Maman Kubra dan haka suka shiga jifansa suna rad a masa dukkannin abunda suka samu, duk tsare gida da masifar Baban Fati kasa hanasu ya yi, sai da Mallan Idi ya ga suna shirin yi masa illa tukunna ya tashi ya fita da gudu dan kansa. Cikin b acin rai Ramma ta ce da ka tsaya mana, shege mugu! Tun jiya ka ji Yarinya ta na ihun neman taimako amma baka zo ka fad a ko ka tattaro jama a an taimaka mata ba sai yanzu da ta kwana a hannunsa! Sai kuma ta fashe da wani Irin kuka mai d aci. Cikin b acin rai Baban Fati ya ce ai ga Irin kalar rashin hankalin naku da baya barinku ku ci riba a kasuwa, na tabbata inda ace mun lallab a mutumin da tsaff zai bayar da shaida against shi Ma in a gaban y an sanda har ma da kotu. Ko ba ke ce kika ce min y an sandan sun ce baku da shaidar ya tab a kashe kowa ba, ta waya?? Ya yi maganar yana kallon Maman Fati. Cikin takaici Ramma ta ce duk da ya kasance ubansa Wallahi ka ji dai na rantse idan ba wata kwakkwarar shaida aka samo ba to a banza! Duk fa munafuka Cikin katseta da b acin rai ya ce ai sai ku yi, ku kuka sani! Daga haka ya d aga labule ya shige d akin Maman Fati. Hmmm Kawai Maman Fati ta ce a ranta ta shiga aiyyana ka ce hakan mana tunda ai ba kai ke zaune a cikin bala in Unguwar ba, da an yi magana ka ce baka da kud in chanja gida, maza kenan Mallan Idi kuwa zuciyarsa fes! Haka ya fito daga cikin gidan dan ya san ko ba komai ya fara rama kaso d aya a cikin d ari na k untatawa da Ma a ya yi masa, tunda ya haifesa ya rasa zuciyar matarsa gaba d aya soyayyar da take yi masa da kulawa duk suka koma kan d an daga baya ma sai da suka yi baram-baram shi da ita wanda har gobe bai gama fara gane kanta ba gaba d aya ta tsaneshi ta tsani sha aninsa. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 26. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Cikin tangal-tangal Inna ta mik e tsaye jikinta yana wani irin karkarwa ta nufi k ofa sawayenta ko takalmi babu. Cike da son sake damalmala al amarin Kaka ta fashe da kuka mai mad aukakin sauti ta na cewa Ni Khadija na ga abunda ya fi k arfina! Yanzu Yarinyar nan saboda Allah a ranar da Mijin aurenta ya bar duniya a ranar ta kaiwa wani kanta?! Wacce iriyar masifa ce wannan Allah ya k addaro mini ita a cikin zuriata. Wallahi ni dama tun jiya da aka nemeta aka rasa har zan ce a tuntub esa kawai dai ban yi tunanin zata yi wannan d anyen aikin a ranar da Kamal ya bar duniya ba sam shiyasa na yi shiru. Duk tsiya dai ai da sun jira ko arba in ne an yi Dai-dai nan makwafta suka fara shishshigowa dan fitar Mallan Idi da jini a goshi yana gudu ya janyo hankalin y an layin suka yo cikin gidan. Ganin jama a sun fara taruwa ya sanya Kaka ta zage dantse ta shiga fad ar maganganun da duk wanda ya ji dole sai Dije ta fita daga ransa Wani abun mamaki a bakin k ofar gidan su Ma ah Inna ta tarar da waensu daga cikin makwabtansu waenda ba ta san ya aka yi har suka ji suka rigata zuwa ba. Sai dai kuma duk d insu sun ja sun tsaya sun gagara shiga, alamun jira suke wani ya d auki wannan alhakin saboda tsoron wanda ke a ciki tare da Dijen. Tashi d aya kuma sai Inna ta ji ba ta son shiga ..tun farko ita ba wai dan ta yarda da maganar Mallan Idi bane ya sanya ta zo ba dan in duk duniya za su taru a kanta to baza ta yarda da cewa Dije ta taka k afa ta tafi wajen Ma ah a ranar da Kamal ya bar duniya ba. Kawai dai ta na so ta tabbatarwa da kanta cewa k arya yake yi to a yanzu kuma da ta k araso haka nan sai tsoro da firgici suka rufeta wata zuciyar ta shiga aiyyana mata To kuma idan da gaske Dijen tana ciki fa? Ya zan yi? Ya zan ji? Me zai faru? Me ya faru? Me mutane za su ce? A hankali ta d ago idanuwanta ta kalli jama ar wajen waenda duk suka ziraro mata idanuwa, waensu ta basu tausayi yayinda waensu kuma suke ji kamar su zuba ruwa a k asa su sha dan murna. A hankali Ramma ta matso tana shirin ce mata su koma gida idan idon mutane ya kau sai su dawo, kawai Asabe ta taho da jagwalgwalallan hannunta (wanda da farko ya yi kamar ya gyaru ta warke jiya tsakar dare kuwa kawai sai gashi ya fara ruwa sosai) ta ingije su ta saka dukkan hannuwanta biyu ta tura k ofar da k arfi ta shiga ta na kuka. Sama-sama take jin hayaniya da koke-koke, a hankali ta d an yunk ura za ta tashi ta ji ta kasa sakamokon nauyin mutum da ta jisa gaba d aya a jikinta! Kanta ne ya yi wani Irin sarawa gashi dama ta ji ya yi mata nauyi sosai a lokacin da ta yi yunk urin duba waye a tare da ita. Motsin da ta yi ya sanya ya gyara kwanciyarsa ya sake sakin mata nauyi har da saka hannu ya sak ale ta, duk da bacci yake yi amma sam ba ya k aunar abunda zai raba shi da yanayin da yake a ciki yanzun. A hankali ta ware idanuwanta waenda suma suka yi mata nauyi sosai ta shiga kallon ceiling d in d akin wanda ya ji adon pop mai lights ga wata had iyar chandelier..k ari take yi ta tuna shin a ina take dan dai tabbas ta san nan ba gidansu bane ba kuma ba Getso bane ba!. Da wani irin masifaffan mahaukacin k arfi ta yunk ura ta tashi wanda hakan da ta yi ya farkar da shi ya tashi tare da ita sai dai har yanzun yana nan kwance a kan jikinta wanda hakan ya sanya ta kasa zama da kyau (tashin da ta yi ya zama kamar irin kishingid ar nan ta yi). Dai-dai nan Asabe da Kaka suka shigo sai kuma Inna itama ta shigo tare da Ramma. Daga nan y an layin da suke tafe tare da su aka hau lellek owa kamar an zo ganin biri a gidan zooo. Su kansu su Asabe sai da suka shiga shock d in da ya d auke maganganu da hayagagar su, saboda ba su yi tunanin za su ga komai intact ya tafi musu yadda suke so irin haka ba. Su Ramma kuwa kasa motsi suka yi yayinda k afafuwan Inna suka shiga karkarwa suka fara shirin zubar da ita a wajen. angaren Dije kuwa k amewa ta yi k am! Ta kasa motsi ta gagara cewa komai..ta san cewa a k asa ta zube ta fad i ta suma sai dai ba ta san ya aka yi ta dawo kan gadonsa haka d are-d are ba gashi kuma a jikinta a kwance wanda hakan ya sanya ita kanta ta gaza yarda da shi da ita dan in za a saka mata wuk a a wuya ba zata iya rantsewa akan cewa babu abunda ya shiga tsakaninta da shi ba, ga wani irin masifaffen ciwon k afar da tunda ta dawo cikin haiyyacinta ya yi mata sallama ga ciwon jikin da bata tab a jin kwatankwacin kamarsa ba. Kawai tsayawa ta yi ta kafe su da idanuwa yayinda shi kuma ya tsaya ya na kallon ta ba tare da ya ce komai ko ya yi komai ba. An kai kusan mintuna biyu a haka kafin ya bar jikinta dan kansa ya mik e tsaye ya tsaya ya yi mik a daga shi sai gajeran wando kamar bai san akwai mutane a cikin d akin ba bayan tun shigowarsu ya san sun shigo! Bai juyo ba amma hatta y an lek e ya san abunda suke yi. ewar da ya yi ne ya sanya aka rarragu wasu suka kwasa da gudu suka fice daga cikin gidan ma gaba d aya wanda zuwa yanzu gidan ya zama kamar ana ganin sarki a gidan ne dan k ofar gidan da soron gidan taff yake da jama a ba masaka tsinke. Cike da izza da gadara ya juyo bai ko kallesu ba ya k arasa ya d auko t shirt mai bottons ya saka ya b alle mab allan ya d auki wayarsa ya daddana tukunna ya kara a kunnensa bai jima ba aka amsa, murya a dake ya ce ka zo mu wuce. Daga haka ya nufi k Guje-guje aka fara yi kamar wani dodo ne zai fito kafin ya fito kuwa duk an watse gaba d aya gidan ya rage saura Kaka Inna Asabe da Ramma sai Maman Kubra da Gwaggo da Matar Mai unguwa wadda zuwanta kenan. Bai dad e da fita ba Tiger ya zo ya d aukesa a machine suka wuce Da kyar Ramma ta k arasa ta sa hannunta mai lafiya ta fara k arin kamo ta Maman Kubra ta
Chapter 51 · 0% Book details