← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayata suka janyota kamar wata wadda ta yi suman zaune Ramma ta mik ar da ita, wanda azabar da ta ji ta sanya ba ta san lokacin da ta rissina ta rik afarta ba. Ki yi mata a hankali fa kin san sabon jini ce, k afarki ko? Asabe ta faiyyace sannan ta tambaya. Ba su kulata ba su ka yi k arin mik ar da ita suka zo suka wuce da ita tana tafe tana d ingishi tana takawa da kyar. Zaninta ta gaba da ta baya da kuma sama-saman duk kana iya hango stain d in jini-jinin da ya zuba ta sanadiyyar tsinin wuk ar da ya chaketa a gefen mararta. Allah ya taimaka ba su tarar da kowa ba dan ba a san Ma a ya bar wajen ba! Sai da suka kusan shiga gida tukunna aka fara lellek owa wasu suka firfito da sauri aka biyo bayansu. Band aki Ramma ta shiga da ita Gwaggwo ta d auko k aton ruwan zafin da ta tara a flask tun d azu da niyyar yin wanka anjima suka yo toilet d Ganin suna shirin yi mata wanka ya sanya ta magantu da kyar ta ce musu um, um Tambayar duniya kuma sai ta gagara sake bud e bakinta ta ce wani abun dan haka Ramma ta yi mata dalla-dalla yadda za ta yi kamar wata mai wankan jego kafin suka rufa mata hijabi a k ofar suka fito suka barta. Ruwan kawai ta d aga ta shek awa jikinta gaba d aya ba tare da ta cire ko Ribbon d inta ba. Ta jima a cikin band akin kafin daga baya ta fito da jik un kayan tana d ingishi tana tafiya da kyar. Group-group ta ga an yi a tsakar gidan nasu kai kana gani ka san munafurci ake yi amma a haka an fake da jaje aka zo yi. Tana jin Kaka ta na waya da alamun da Mallan ne To dai a kan gadonsa a ka tsinto ta da kyar!! Da ma ai ita rayuwa shiyasa ake so ka zama na kirki sannan ka zauna da kowa lafiya. Matar nan kaff layin nan babu wanda ba ta yin fad a da shi ita da y arta sun addabi kowa, sannan wuyarta ta ji maganar shaye-shaye ko cikin shege a gindin wani shikenan ta tusa ka da gori kenan har sai baba ta gani, ranar nan fa cewa Asabe ta yi arta ta fi k arfin k addarar cikin shege! Sai ka ce ubanta ke raba k addarar. To dai yau ga d an daba d an shaye-shaye ya kwashe duk wata albarkar y anmatancin da ke a jikinta sai a yi jinya a had a da gwajin k anjamau! Ai shi Allah ba a yi masa gatse. Shiyasa aka ce maka ka mayar da ita makarantar addini amma ka ce kana koya mata a gida, ai ga irinta nan, bokon ma da ta ke k aryar ta yi ta iya ai ba iyaka rubutu da karatu baneba har da zamantakewa mutum yake koyo wanda ita sam bata iya ba jahilci ya yi mata k abe-k abe, kwata-kwata bata san ilimin zaman duniya ba! Yanzu ga irinta nan ai bakinta ya janyo muku. Ita dai Dije ta ji Kaka ta na magana amma wallahi sam ba ta fahimci kalmar da ta ce a cikin zantukan nata ba. Diriricewa ta yi ta rasa gane wannene d akin nasu dan haka ta tsaya tana kallon d akunan d aya bayan d aya kamar mai son k idaya su. Yanzun ma Ramma ce ta taso ta zo ta wuce da ita cikin d akin Inna dan Kaka har ta fara zaginta wai ta b ace mata daga gani warin Zina take yi, ta shige d aki kar ta sake fitowa har sai ranar da za ta bar mata gidan d a! Dan yanzu shigarta cikin al umma ma haramun ne. Ita bata tab a ganin Yarinyar da take iya kallon mutanen k urr haka a ranar da d a Namiji ya sanya a matsayin y a mace ba sai Dije! Haka nan d azuma tana a kan gadonsa d are-d are amma ta yi musu k urrr kamar sabuwar mayya A zaune suka tarar da Inna tare da Matar mai unguwa tana yi mata magana da alama nasiha ce, ita Ramma ba ta ma san sun shigo ba dan haka ta k arasa ta shimfid a mata darduma da zani dan har yanzu kayan d akin nasu yana waje an tattara a waje d aya. Zaunar da ita ta yi ta fita ta je cikin kayansu ta d auko mata kayanta ta bata ta ce ta tashi ta chanja. Zuwa yanzu yanayin Dijen ya fara tsoratata dan ko da ta tashi d in a kan kayan jikinta ta fara k arin saka waenchan d in dan haka ta yi saurin rik o hannunta ta girgiza mata kai dan ta ga kamar ta fi fahimtar wannan yaren yanzu. arin kwance mata zanin ta yi amma ta k i yarda..sun fi minti d aya suna fama a haka k arshe ta fashe mata da kuka dan haka matar mai anguwa ta ce ta barta da kayan jikinta kawai maybe fargaba ba ta gama barinta ba. Tunda Ramma ta ke a rayuwarta za ta iya cewa ba ta tab a ganin abunda ya bata tausayi bayan y anta a lokacin da Mijinta ya rasu sai Inna da Dije a halin yanzu. Ga Kaka a waje ta k i yin shiru kusan duk wanda ya shigo sai ta sanar masa da halinda ake ciki dalla-dalla Asabe ta na tayata, ka na gani ka san murna suke yi. Mallan kuwa ta kirasa ya fi sau biyar daga shigowarsu zuwa yanzu, ta na ji yana ce mata hanya babu kyau amma ta ce ya taho a haka ya tabbata ya zo Kano a yau a yi ta ta k Girgiza kai kawai Ramma ta yi ta fito jikinta a sanyaye ta bar d akin dan sosai tausayinsu zai iya sakata yin kuka a rasa mai rarrashin wani tsakanin ta da Inna. Ga Ya Muhammad a gefe a zaune shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba. Abun tausayi. Ko da Ramma ta fita ta tarar Kaka ta kira Kawu Isa tana zaiyyane masa bayani wannan karon kam har da Allah shi k ara take ta cewa dan ta kasa ci gaba da b oye farin cikinta. Ita dai Ramma ta wuce ta barta nan tana mamakinta. Kaka kuwa ji take kamar ta janyo Mallan kawai ta gansa a gabanta yanzun dan ba ta so abun ya yi sanyi ta fi so ya zo ta sake rura wutar a san na yi da Dije ta san har da Halima! Ta tafi ta bar su haka ya Isa! Dan wallahi tsintacciya ba ta Isa ta gaje mata gidan d a ba ta yi kad an!!!!. Ramma ta na shiga d akinta ta ji kanta ya sara, sai kuma tunaninta ya bata yanzu fa idan ba ta nema musu mafita ba tsaf wani azzalumin zai iya aikata irin hakan ga Rakiya ko Fiddausi kuma a gagara bi musu hakk insu, har gara ma Dije in da ace ba Ma a bane ba ta san Mallan zai tsaya mata, ita fa? Dan haka gara mata kawai ta tura su chan ta tseratar da su daga wahala da zalinci da masifar Unguwar nan, su je su dawo da k ima da kud i da mutuncin su, akan dai ta barsu a nan babu gata babu tudun dafawa. Kawar da tunanin ta yi ta nemi guri ta zauna a kusa da Rakiya wadda take zaune tana cin gari, d ago idanunta ta yi ta kalleta ta ce Allah ki tsame hannunki daga lamarin su Dije, tam! Ta yi kwafa ta ci gaba da cin kwad on garin kwakinta wanda ya ji farin mai da gishiri zallah, shima kuma a haka Kubra ce ta d iba mata komai. Ba ta kula ta ba ta yi shiruuu dai dan babu abunda ya fi shiga kanta sannan zuciyarta take azalzalarta akai a halin yanzu kamar ta ga an gama magana ta tura su Ingila ko Saudiyya. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 27. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. *************** Zuwa wannan lokacin rashin lafiyar mai martaba sarki ZainulAbiddeen ta zagaye masarautar gaba d aya har ma da wajenta da waensu garuruwan na k asar ta Khak il. Sai dai kuma Gimbiya Mariya ta fito ta k aryata hakan ta inda ta ce zamewa ya yi kawai ya fad i ya d an gurd afarsa, ba wani abu serious bane ba kuma yanzu haka ma yana a kan treatment dan haka kowa ya kwantar da hankalinsa. Alhalin a asalin gaskiya yanzu haka Sarkin abinci ma ta robar hanci ake bashi. Kwararrun Likitoci bakwai ne a kansa waenda sai ka dage ka ci sa a tukunna ake iya samun appointment da su. Malamai wajen biyar har da wani boka da d an bori, sannan Oga kwata-kwata shima yana akan nasa binciken dan halin da take ciki bai sanyaa ta mance ta saka a binciko mata su waye masu wannan d anyen aikin ba. Kowa ya zuba ido ya ga ko ya ji wani leakage a kan jikin nasa amma ta yi bakam-bakam ba ta bawa kowa dama ba sai y ar ta Zakiyya da amininta Nuraddeen ne kawai suka san komai amma hatta y anta na gidan aure ba ta gaya musu ba. Su Wambai da Galadima suma k ari take yi ta goge musu hadda, dan takanas ta kirawo su ta ce musu ranar gurd ewar da ya yi ce ta janyo suka ganshi hakan amma ba komai bane ba, yanzun jinyar k afarsa kawai yake yi kuma da zarar ya warke zai fito ras in sha Allahu. Dan haka kar ma su je suna ta yayata fake news d in da ba shi ba, kuma su sani muddin ta ji wani zance to ta san daga garesu ne dan haka su kuka da kansu. Daga haka ta fice ta barsu a wajen suna ta kallon-kallo. Su dai sun san gaskiya kuma sun fahimci me take son yi tunda ba
Chapter 52 · 0% Book details