Sashe 5
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
itama zata gurza musu tunda ba su san mutunci ba. Umar da Usama ne kawai suka rage a tsakar gidan dan kowacce ta shige cikin d aki, masu fita yawon Juma a kuma sun fice amma har zuwa wannan lokacin Inna tana nan zaune a tsakar gidan tana bala i da masifa dan tana gama waya da Minu da ta ji jikinsa da sauk i Alhamdulillah nan ta fito ta ja kujera ta dasa a inuwa ta shiga k arewa Asabe d iban albarka, gori kuwa kala kala kamar ita ta yankewa k asar garinsu cibiya .Kasancewar wata k anwar Asabe ta tab a yin cikin shege, a cikin yayunta maza kuma akwai mai shaye shaye wanda kowa in dai a Unguwar kake to ka san Yaron da shaye shaye da sace sace!Hakan ya sanya Inna ta samu abun yi dama ta saba goronta mata akan hakan amma na yau ya fi na kullum ga kuma wasu sabbin surrakan gidansu waenda ita kanta Asaben ba ta san ta ya aka yi Innar ta ji ba, haka nan dai ta yi mata tatass! Ta tsigale ta ta yi mata tumb ir dan har sai da ta saka Asabe kuka ita kad ai a d aki. Tukunna da kyar Ya Muhammad wanda ya dawo daga wajen Minu, yau d aya ya ci nasarar mayar da ita d aki lokacin har sallar la asar an yi an idar. Wunin ranar Asabe a d aki ta yi shi gashi babu wanda ya lek ota dan Inna tana gamawa da ta mik e ta shige d aki sai ragowar matan gidan da basu fita ba suka taru a d akin Ramma aka dasa faifan munafurcin gidan su Asaben! Dama yanzu haka ma akwai wata k anwar ta bazawara da ta fito daga gidan miji kuma matar tana da d an tara zawarawa ga shegen yawo, to ga kuma sabbin abubuwan da suka ji daga bakin Inna yanzun, dan haka topic d insu na ranar sai ya kasance a kanta. Jikin Minu da sauk i, an yi masa dressing na ciwonsa inda ya yanke a ta sanadiyyar dutsen da Yaron Ma a ya cillashi a kai, yanzu haka ma ruwa ake k ara masa zuwa bayan sallar la asar zai dawo tare da samarin layin da suka yi cincirundon kaisa kuma har yanzu suke a tare da shi, kud in asibitin ma sune suka yi karo karo suka biya Suna shiga d akin Ya Muhammad ya kalleta ya ce Inna ko kin san cewa daga makwabta aka kirani aka ce min har yanzu ba ki yi shiru ba in zo in raba fad an, haka nan na baro marar lafiya na dawo. Cikin fad a fad a Inna ta ce Gidan su Suwaiba ko? Shegu munafukai, bar ni da su! Da suka kira ka ka dawo to duka na za ka yi??? Dafe Kai Ya Muhammad ya yi saboda sam shi sentence mai tsaho ma juya masa kai yake yi ballanta doguwar muhawara, cikin rashin jin dad i ya ce haba mana Inna, ya kike so in yi ne? Da wannen zan ji? Dan Allah ki daina Cikin katse shi ta ce na ji! Zai yi magana ta sake cewa na ji na ce a d an hassale dan haka ya ja bakinsa ya yi shiruu. So yake ya fad a mata sak on Mallan da ya ce Ita da Dije su bada kud i a kai Zainab chemist amma yana jin tsoro dan ya san ba zata bayar ba kuma bala i ne zai kunno kai, dan haka kawai sai ya yanke shawarar kai Zainab d in da aljihunsa in ya so ya ce mata Inna ce ta bayar da kud in dan ya san dole Mallan zai nemi ji daga wajensu, Allah dai ya sa Yarinyar ta yarda dan a yadda aka gama kashe boss da uwarta da Innar ya san tana da wayon da ya ci ta fahimci kud in kaita chemist ba zai tab a fitowa daga aljihun Innaa a yau ba. Haka nan ya k arasa ya yi sallama a k ofar d akin nasu ya ce Zainab ta zo zai kaita chemist a duba mata hancinta in da ya fashe. Sosai Asabe ta so ta hana ganin sai yanzu ma aka kula su amma kuma kawai sai ta barta ta bishi a ranta ta ce raba Arne da makami ibada ne. Bayan Ya Muhammad ya fita, sallah Inna ta fara yi daga nan ta zari mayafinta sai gidansu Suwaiba makwabtansu. Sai da ta yi musu tatass!! Tukunna ta ji zuciyarta ta d an yi sanyi ba laifi dukda kuwa rashin tanka mata d in da suka yi ya b ata mata rai amma dai ta rage takaicinta. Haka nan ta k are musu d iban albarka tare da kwakkwaran kashedin su daina yi mata shishshigi da munafurci daga nan ta juya ta fita ta koma gida.. Sai gab da sallar isha tukunna aka dawo da Minu. D akin mazan gidan shine na farko a jerin d akuna hud u da suke a hannun hagu, dan haka suka nufi nan da shi, amma sai Mallan ya ce su dawo da shi d akinsa mai k ofa ta soro Hakan kuwa aka yi suka kai shi daga nan suka yi masa sallama suka wuce bayan wasu a cikinsu sun shiga sun lek a sun gaida Inna tare da yi mata jaje da fatan Allah ya kare gaba. Wannan Abu da aka yi ba k aramin sake tunzura Asabe ya yi ba, dan ta gama tsarawa idan ta je turaka ne zata warware masa abunda ya ke cikinta amma gashi ya ce a kai Minu bayan yau d in ba kwanan uwarsa bane ba kwanan ta ne. Har wajajen k arfe goma na dare bata ji kuma ba ta ga an fito da Minu ba dan haka hankalinta ya sake tashi ranta ya sake b aci!! Ta yaya ma za a d auki k asurgumin gardi a d aura a kan katifar sunnah fisabilillahi Ta aiyyana hakan a cikin ranta. Ta dad e a tsaye tana ta faman lek en d akin, da yake akwai wata k ofar shiga d akin ta inda suke shiga ita da Inna da window ya sanya ta hango yadda aka rage fitilar alamun ana shirin yin barci kenan Ko mayafi bata tsaya d auka ba daga ita sai y ar hula da sleeping dress d in da matar manager ta bata a kayan kunce dan Asabe ba dai son gayu ba, haka nan ta fito rai a b ace ta Isa bakin k ofar ta saka hannu ta tura amma sai ta jita a rufe. acin ranta ne ya sake hauhawa dan haka ta zagaya ta Isa bakin k ofar d akin dake a soro ta fara bubbugawa Ba ta wani jima ba ya zo ya bud e mata, har yanzun rawani ne da babbar riga a jikinsa alamun bai yi shirin kwanciya ba. Kallonta ya yi kafin ya yi gyaran murya ya ce yi hak uri ban nemeki da wuri ba, yanzu nake shirin zuwa in nemi yardarki akan Minu ya kwana a wajena, Ina ga ba sai kin zo ba ko? Akwai tofin da nake son in kwana yi masa saboda kin san al amari idan ya shafi kai dole a bashi muhimmanci. Ba tare da ta kalle sa ba ta ce ban amince ba Yadda ya yi da fuskarsa zai sanya ka fahimci maganar ta dake sa matuk a amma sai ya kawar yana shirin yin magana ta katseshi ta hanyar sake cewa Ban fa amince ba kuma ban lamunta ba! Ai kai Malami ne mai tsoron Allah dan haka na san ka san yin hakan haramun ne. Dai dai nan Kaka wadda tun d azu ta ga fitowarta ta k araso wajen cikin takunta na tsoffi rai a d an b ace ta ce yanzu ja inja za ku tsaya yi ku tarawa kanku jama a ko yaya? Dai dai nan Minu wanda tunda ta fara maganar ya farka ya tashi daga kan kafet d in inda ya yi shimfida shima ya k araso wajen Da kyar kunya ta barshi ya iya cewa Mallan bara in je da safe sai ka k arasa min. Cikin d an b acin rai Mallan d in ya ce wa ya sako da kai? Yana shirin yin magana Kaka ta ce Aminu wuce ka tafi d akinku A hankali Mallan ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai. Simi simi Minu ya zo ya wuce bayan ya yi musu sai da safe gaba d aya jikinsa babu kwari. Cikin d an fad a fad a a hankali saboda kar a ji Kaka ta ce ka san Allah idan ba ka daina gwada wannan son kan da nuna banbancin ba to ka tabbata za mu samu matsala da kai! Wanne irin sakarci ne haka za ka d auko k ato ka saka a d aki ranar kwananta?? Kuma idan ta yi magana sai a ce ba ta da gaskiya ba ta kara bayan kune da laifi! Ina ce rigimar y ar uwarsa ce ta jefa shi a matsalar dan haka Ina ruwanka?? Ai dama abunda ake fad a ake guje muku kenan amma sam ba kwa ji yanzu ga irinta nan! Ayi mutum kamar mai karin kumallo da wuta amma sam baka son laifinta ita da uwarta ai kuwa ka gamu da aiki babba wallahi.. Sannan Ina so ka jaa wa Halima kunne duk da na san ba jinka zata yi ba dan ta raina kowa amma dai ka fad a mata kuma ka yi mata kashedi mai zafi!!! D azu bayan ka fita haka nan ta wuni a gidan nan tana rashin albarka dukda kuwa kashedin da na yi mata amma bata ji ba saboda ta raina ni, ban kula ta ba a lokacin amma wallahi ka ce mata na ce idan ta k ara to ni da ita ne a cikin gidan nan, da ni za ta yi! Ai ta sanni ta san abunda zan iya aikatawa dan haka mu zuba ni da ita a cikin gidan nan tunda ita dai ta ce bata san mutunci ba. Tana gama fad in haka ta juya ta bar